, ya Éauke kansa gefe ya cigaba da abin da yake yi.
"Hubbi".
na sake maimaitawa ina kallonsa, nan ma shiru.
gaban Æafafunsa na duÆa ina riÆe Æafarsa alamu na neman yafiya.
"Hubbi magana na ke maka fa, na san nayi maka laifi amma kayi haÆuri ka yafe min, kafi kowa sanin halina ba zan hana su Atika abinci haka kawai ba. Meye ribata in na hana su abinci?, wallahi ko wasu Æ´aÆ´an ba zan hana abinci ba balle kuma su da su ke Æ´aÆ´ana".
magana ya fara, sai dai maganar ya ke yi tamkar ba da ni ba, ni kuma nayi cak saboda kiÉima ina kallon bakinsa da ke motsawa.
"shugabar makarantarsu ce ta kira, ta shaida min an kai Éaya daga cikin yarana asibiti har an kwantar da ita, in yi gaggawar zuwa domin akwai ÉuÆatuwar kashe kuÉaÉe. ina zuwa likitan ta shaida min ciwon ciki ne amma sun Éauki hoto anyi gwaje gwaje, tun bayan awa biyu yanzu Atika na cikin matsanancin hali na rayuwa, bata farka ba, har yanzu bata motsa ba Sa'ida! bata samun isassan abinci a cikinta haka likitan ya faÉa".
yay shiru da maganarsa, naga ya Éauko Æaramar takarda alamun daman ita yake nema tun Éazu, ya tura durowar ya kulle sannan ya gifta ni zai wuce na riÆe hannunsa na ce,"Dan Allah Hubbi kayi haÆuri, wallahi ban san bata da lafiya ba, ban kula ba kuma bata faÉa min ba".
Zafin hannunta shi ya ratsa shi sosai hakan ya tabbatar masa da zazzaÉi ne a jikinta bana wasa ba, ya kalli fuskarta yaga duk ta canja ga gefen bakinta a fashe, zai so yay tambaya akan silar ciwon, sai dai ba ya son jin wani ba'asi, hasalima fuskarta haushi take bashi.
ganin irin kallona da yake min sai na Éauka ko ya fara sauka ne, sai na sake marairaicewa ko Allah zai sa ya fahimce ni, kumburarrun idanuna na hawaye na ce,"don girman Allah ka bawa zuciyarka salama ka tsaya ka fahimce ni. Hubbi kana yawan min nasiha akan fushi da haÆuri. Hubbi ka tuna wata rana da nayi fushi da kai tunasarwar da kayi min?...ka faÉa min fushi tamkar taÉin hankali ne Æarshensa Nadama ne...ka tunasar da ni cewa fushi shi ne tarkon abin da shaiÉan yafi amfani da shi wajen halaka Éan adam. haka ka Æara tunasar da ni da faÉin manzan Allah(SAW) akan maganin fushi; yace idan kai fushi idan kana tsaye ne ka zauna, idan kana zaune ne ka kwanta ko kuma kabar wurin da aka saka kai fushin...Hubbi ka tuna...".
bige ni yay yana Æwace hannunsa, ya nuna ni da yatsa yana cewa,"ba ki kai nayi fushi da ke ba...na sani kina so na sakko ne saboda na buÉe miki kitchen, to kinyi a banza wallahi don ba zan buÉe ba sai dai kema a kai ki asibitin, ai yanda kika hana yarana abinci kema haka za ki kwana babu abinci a cikinki, in yaso ki ÉanÉana abin da suka ÉanÉana. Useless woman".
ya faÉa yana hararata ya shige ya fita ya bar min Éakin. nayi murmushi mai ciwo kan abin da ya faÉa, ban da abinsa ta ya zan nemi wani abinci a wannan halin bala'in da na ke ciki?, ta ina abinci zai samu gurbi a cikina?, ai hakan ba abu bane mai yuwa a wajana.
ina jin tashin motarsa alamun ya Æara fita, na jawo Æafata na fito daga Éakinsa na koma nawa, na kwanta a kan gado nayi lamo jikina duk ciwo yake min, ina ta karkarwar sanyi. Haka na yini a kwance cikin matsananciya damuwa, Éangare Éaya cike da fargabar dawowar su Yaya haka kuma cike da tsananin tsoron hukuncin da Hubbi zai yanke.
tashi kawai na ke in shan ruwa in koma in kwanta har magariba babu abin da ya shiga cikina sai ruwa, na galabaita sosai ga ciwo ga yunwa ga aman ruwa, kwata kwata na rasa me ya ke min daÉin a duniyata, ban isa na tuhumi ubangijina kan jarabawa da Æaddarar da su ke ta Æwallo da ni ba tun aure, sai dai zan roÆe shi da ya bani ikon cinyewa zuwa matakin nasara.
bayan nayi sallar magriba ina zaune jugum, lokacin na kira wayar Hubbi yafi sau goma bai Éaga ba duk saboda naji ya jikin Atika, hatta ita Yaya da Iyam sai da na kira su amma babu wanda ya Éaga wayata, ban san wanne asibiti ba ne balle na bi bayansu, sai Lubabatu na kira tace min duk suna asibiti itama an barta ne da yara a gida, amma sun yi waya ance jikin da sauÆi. ajiyar zuciya na sauke don sai a sannn na sami relief, na kwantar da kaina gefen gado ina jan carbi, cikin tunanin da na ke zuciyata ke faÉa min ya kamata in kira mahaifina mu gaisa don mun kwana biyu bamu yi waya ba.
duk da ina fargabar in kira shi saboda yacca zai saurin gano damuwar da ke kan muryata, haka na daure na danna kiran saboda ko ba komai waya da shi Éin zai yaye min damuwar da na ke ciki.
nemo lambarsa nayi, nafi Æarfin minti uku ina saÆa da warwara akan in kira ko in fasa, can kawai na danna kiran ya tafi, kamar yanda ya saba duk lokacin da na kira shi yauma hakan ce ta kasance, ya katse kiran nawa sannan ya biyo baya.
da adu'a na samu raunina ya Éoye da na Éaga wayar nayi sallama.
"Salamu alaikum Abbaa".
"Wa'alaiki salam da ma'aikaciyar lafiya, Ƴar albarka ya aka yi saÆon zuciyata ya iso gareki da wuri hak