NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 97

kaɗai har yanzu cikin gidan nan shi ne kike son zuba iskancin da kike so. To ta ƙare wallahi, daga yau komai yazo ƙarshe, za ki gane kin hora ƴaƴanmu da yunwa, za ki tabbatar da bani da mutunci bani da kirki ko kaɗan. Kuma na rantse da Allah in kika sake wata cutar ta sami Atika sai na saka an ɓalla miki ƙafa dan ba zan kai ki police ba, sakawa zanyi kema a kashe ki dan uwarki da ubanki, azzaluma wacce bata san ciwon ƴaƴa ba". Yaya ke wannan furucin da suke daidai da watsa ruwan zafi a jikina, kallo take min mai cike da tsana, yayin da ni kuma ke mata kallon da na kasa fassara shi. idona ya koma kan Anty Aisha da ke cewa,"saboda ba ki san darajar haihuwa ba, ba ki san zafin ɗaukar ciki ba, ba ki san wahalar laulayi ba dole ki bar mana yara babu abinci tun da abincin ubanki ne ya kawo. Mahaukaciya! jahila! juya! wacce da ita da namiji basu da banbanci, har gwara ma namiji zai yi ciki a ɗauka ke kuwa fa?, shekara takwas ba ɓatan wata balle ɓari" Yaya ta kalleta da ce mata,"Aisha ƙyaleta mu wuce asibitin nan, hankalina na kan sanin halin da yaran nan ke ciki". sai kuma ta kalle ni ta ƙara cewa,"dangin matsiyata gayyar tsiya, masu baƙin baya". ta faɗa tana tana kama hannun Aunty Aisha su yi gaba, suka bar ni kwance ina kuka ina sauke numfashi a hankali cikin tsananin jin zafin ciwukan jikina. da ƙyar na samu naja jikina har zuwa bakin ƙofa na ɗauki ledar abincin da na zuba, cikin sauri na fita ina kwaɗa kiran Yaya! Yaya! su na gab da fita a gate su ka dakata, na ja ƙafa na ƙarasa gabansu ina miƙa musu da cewa,"na san nayi laifi, na kuma aikata babban kuskure, ban san me yake faruwa ba, kamar yanda ban san a halin da ƴaƴana su ke ciki ba, amma furucinku ya tabbatar min da su na cikin yanayi mara daɗi, ko kusa wallahi summa tallahi bada gangan na bar su suka fita basu ci komai ba, kuyi haƙuri don zatin Allah, tun da ku ka bamu yaran nan na ɗauke musu matsayin ni nayi naƙudarsu. duk wani dogon bayani da zan yi daga baya ne na sani, amma Yaya a gafarce ni don girman Allah, wannan abincinsu ne na break a tafi musu da shi kafin na zo asibitin". ba wacce ta katse ni daga maganar da na ke, kamar yanda babu idon wacca ya fasa jifina da kallon banza, Anty Aisha ta warci ledar ta ciro flask ɗin, tana buɗewa ta watso min abincin a jikina Allah ya tsare bai zuba a fuskata ba, haka kuma bai zuba da yawa a jikina ba saboda saurin ja da baya da nayi. "munafuka, kin dafa za ki kai gida ki bawa tsaffi su ci shi ne za ki fake da abincin yara, idan na su ne me ya hana ki basu su ci kafin tafiya, makira kawai". cewar Anty Aisha, daga hakan kuma su ka buɗe ƙofar gate su ka fice. nayi tsaye ina ina kallon jikina da abincin da ke zube a ƙasa me uban yawa, wani ƙunci na daban ya daki zuciyata. maganar me gadi ta fargar da ni da yazo gabana yana cewa,"kiyi haƙuri ƴata, ga ruwa ki ɗauraye jikinki kar zafin tururin yaywa fatarki illa". ina share hawaye na ce,"na gode Baba". ya ƙara cewa da ni,"a ci gaba da haƙuri watarana sai labari". juyawa nayi na koma ciki da gudu gudu. a falon na zube ban iya hawa sama ba. _"Gayyar tsiya, dangin matsiyata, masu baƙin baya."_ kalaman Yaya na ƙarshe ya haska a kaina, nayi murmushin takaici ina hawaye, wai yau ni ake cewa dangin matsiyata, ba zan fasa faɗa ina nanatawa ba, tabbas ciki mai manta kyautar jiya!.  Jingina nayi da kujera ina juya kaina da ke bala'in sarawa, ga cikina na min ciwo sosai wanda na san bayan zafin duka har da na yunwa ma. idanu na lumshe saboda ciwon da na ke ciki na kasa motsin kirki, jikina duk yay tsami, ban san adadin lokacin da na ɗauka ina kuka a wajan ba sai kiran sallar azahar naji. Ganin lokacin sallah yana sake tafiya sai naja jiki da ƙyar na shiga banɗakin falo, nayi alwala na fito nayi sallah a zaune kamar zan kifa haka na ke jina. A kan sallayar na kwanta ina son yin bacci, ba don komai ba sai don in mance da abin da ya faru da kuma samun sauƙin ciwon jikina. ina riƙe da cikina ji nake kamar zan mutu saboda ciwon da yake min, ganin zan kashe kaina ya saka na tashi na lallaɓa na hau bene da ƙyar, shima da dafa bango har naje ɗaki. magani na ɗauka da niyar sha sai kuma na tuna babu abin da na ci, ko da na sha maganin ba wani aiki da zai min. horn ɗin mota na jiyo hakan yasa na ƙarasa ina dubawa, Hubbi na gani ya faka mota ya fito ya nufo cikin gidan, gabana yay mugun faɗuwar da ban taɓa ji yayi ba, na saki labulen na fita a ɗakin da sauri, jin takun hawowarsa benen yasa na tsaya har ya ƙaraso. Kamar bai ga mutum ba ya wuce ya shiga ɗakinsa, nabi bayansa na same shi a tsaye a jikin durowa yana lalube da alama akwai abin da yake nema, jiki a sanyaye na ƙarasa ciki, har lokacin ciwon bakina bai daina jini ba. murya a hankali cikin tsoro da shakkar abin da zai biyo baya na ce,"Hubbi." Banza yayi min kamar ba halitta mai motsi ke magana ba
🏠