NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 3 of 97

“anin yanzu da ko'ina a jikina ƙashi da jijiyoyi ne suke magana, ido kuwa ramar da ta fito da shi waje yanda kasan na mujiya, gefen kumatuna duk ya zurma ciki, shi kansa uban hasken da nayi ba na komai ba ne sai na shegiyar ramar da nayi, albarkatun ƙirjina kuwa duk sun kwanta shalaf kamar wacce ta shayar da Æ´aÆ´a ɗari, duk na zama wata babu kyan gani kai baka ce me tashen ƙuruciya ba shekaru ashirin da huɗu a duniya. Lokaci guda idona ya cika da tarin ruwan hawaye, sai dai basu sami nasarar zubowa ba, cikin yanayi na bala'in tausayin kaina na sunkuyar da kaina ƙasa ina jin wani dunƙulallan abu na tsaya min a maƙogoro yaƙi wucewa, hakan sai ya zama famin ciwo a gare ni, wanda da zan samu in korashi da yawun bakina ko kuma ya wuce da kansa wataƙila da na sami sassauci. Cikin ƙarfin halin da na saba na ɗago kaina ina mayar da tarin ƙwallar da ta cika min ido, ɗakin kawai nake bi da kallo, ko a iyaka shi aka bar bawa rayuwa ya ishe shi jin daɗi da more rayuwa, damuwarsa ta gushe, ballantana kuma ace rayuwa kake yi a cikin tamfatsesen gidan nan da yake sai kace a ƙasashen turawa, lumtsum nake a cikin daula, duk wanda yazo gidana ba ya son tafiya, iya dukiya dai an narkata wajen ginin gidan, zaka rantse da Allah ba duniyar da talakawa ke rayuwa ba ne, idan ba Allah ya soka da rahma ba sheɗan sai ya shagaltar da kai da yin ibada. Sau tari ƙawayena da Æ´an uwana kan ce min ke kam Sa'ida kin more, ba ki da saurin baƙin ciki da takaicin duniya domin Allah ya kashe ya ba ki, arziƙi ta ko'ina, kalli gidan da kike ciki kamar ba za'a mutu ba, irin motocin da ake fita da ke a cikinsu zamansu kaɗai yasa kiyi ƙiba ki fresh, abinci kullum da nama, ke kam ba ki da sauran damuwa, ba su san da cewa ba anan take ba wai abin da yawa mutuwa taje kasuwa, sai da kwanciyar hankali ake jin daɗin. Madubin da ke gabana na kalla da kyau, na sauke babbar ajiyar zuciya tare da yin murmushi mai ciwo, ina mamakin masu faɗa min irin wannan zantukan, ban sani ba ko iyaka daular da Allah ya ajiye ni a ciki kawai suke kallo shiyasa ba su taɓa lura da cewar akwai ƙalubale mai wahala a gefe, bana jin daɗin gidan, bana farin ciki sam, su ka kasa ganin irin lalacewar da nai, su ka kasa fahimtar gwara ma rayuwata ta baya akan ta yanzu, su ka kasa fahimtar ina da buƙatar taimakonsu. Su na ganin cewa zan iya yi musu komai tun da su na kiran wannan ƙaton gidan da gidan Sa'ida, ba su san cewar babu abin da zan iya, domin ba ni da komai, tun da komai ɗin da su ke kallo ba mallakina ba ne ba taƙamata ba ne. Ƙwarai kuɗi da rai da lafiya rahma ne, kuɗi komai ne bayan lafiya, babu abin da yafi ace yau kafi ƙarfin komai, ace yau kai ne kake ɗauka ka bayar ba wai a ɗauka a baka ba, kaci mai kyau kasha mai kyau ka kwanta a mai kyau kasa sutturu masu kyau da tsada, ka hau jirgi ka keta hazo zuwa in da kake so, ka ɗiba ka kashe babu mai ƙayyade maka, kayi mu'amala da mutanen da su ka fika. To amma me?, duk da irin tarin dukiyar da kake da ita, da irin daular da kake rayuwa a ciki, muddin babu kwanciyar hankali to babu farin ciki da jin daɗi. Ni a wurina gwara in rayu cikin talauci akan ace ga tarin dukiyar amma babu zaman lafiya babu kwanciyar hankali balle na sami natsuwar zuciya. Na sake sauke ajiyar zuciya mai nauyi a karo na uku, murmushin da yafi kuka ciwo nayi ina girgiza kaina wanda ni ɗaya na san ma'anar hakan. Abu ɗaya na barwa kaina sani shi ne kowanne matakin nasara ba'a hawansa sai da ƙalubale, kuma komai na duniya fararre ne ƙararre, kuma dogaro ga Allah jari, babu kuma mai yi sai Allah, muddin akwai yau, gobe da jibi to komai zai shuɗe ya zama tarihi. Na gyara ɗaurin ɗankwalin da ke kaina, turare na ɗauka oil na shafa, sannan cikin sanyin jiki da mutuwarsa na fita a ɗakin ina jin ƙafafuna tamkar a ƙanƙara. cikin sauri da rashin jin daɗi a raina da ban ankarewa tafiyar lokaci ba na fita, na san duk inda Hubbi yake yanzu yana kan hanyar dawowarsa gida, wataƙila ma ya dawo ban sa ni ba, tun da Æ´an kwanakin nan bana sanin dawowarsa in ba zaman parlo nayi ba, kamar yanda ba zan san fitarsa ba, ga shi ko abinci ban ɗora ba sakacin da ban taɓa yi ba, abincin da idan nayi ma ba'a masa cin kirki ko kuma a barni da kayana, amma duk hakan ba zai sa in daina ba, zan ta ƙoƙarin sauke hakkin da ke kaina na dafawa tun da an siyo an a jiye. Ina fitowa daga bedroom ko ƙasa ban sauka ba don gani nake zan ƙara ɓata lokaci ne. kitchen ɗin sama na wuce kai tsaye, babu ɓata lokaci na buɗe fridge na ɗauko gwangwanin bama da nake zuba dafaffen kayan miya a ciki, ni kam ba ruwana da wahalar jajjage ko markaɗe kullum, da ya jido uban kayan miya na ke markaɗe su in dafa in juye a kwalabe. Ina aiki ina ta muraja'a, A ƙanƙanin lokaci na kammala dafa taliya jallof sai tashin ƙamshin busassan kifi take yi da ƙamshin kayan lambu, na juyeta
🏠