iÆe jiki babu Æwari ina matuÆar jin jiri, a daddafe da bango na fita daga falon zuwa farfajiyar gidan.
can ta bayan gidan na nufa wajen da shuke shuken fulawoyi su ke, na nemi manyan duwatsu da busassun itatuwan fulawa da aka ciccire na haÉa murhu, na gangaro durum na kawo shi bakin tagar kicin. takawa nayi na zura hannu ciki, da dabara na samu na buÉe murfin durowar sama da Æyar tukunna na lalubo ashana, dama tagar da Éan faÉinta da haka nayi nasarar ciro Æaramar tukunya.
zuwa nayi na iza wuta na Éora tukunyar, sannan na dawo na gangara durom Éin zuwa tagar suto, shi dama ana iya shiga ta tagar don haka na shiga ta ciki na Éebo macaronie da kayan sarrafata wajen girkawa, cikin sauri sauri na ke komai gudun kar mai gidan ya dawo.
a wurin me gadi na aro wuÆa da ce masa na nemi tawa na rasa, don haka yankan kayan miyan nayi tun da babu abin jajjage. nan da nan na tashi jalof Éin macaronie, adu'a na ke tayi ta dahu da wuri har in samu na zuba akaiwa Æ´an makaranta abinci tun da break biyu su ke fitowa dama, babu Æaramin cooler da zan zuba musu abincin don haka Éakina na koma dole na lalubo wani Æaton flask me guda Éaya, ashe da ranarsa da har ina cewa Kakarmu da ta bani bana so, a cikinsa na juye musu abincin na rage kaÉan wanda zan ci.
bayan na kammala haÉa musu komai ina sauri in fito in kaiwa Me gadi ya taimaka ya kai musu, isata bakin kofa in Éaga labule na jiyo kamar tashin hayaniya daga compound, sai dai kafin nayi wani tunani akai aka cakumar min wuya.
tsoro yasa na ambaci sunan ilahu da Æarfi, sai dai idona na sauka kan wacce ke damÆe da wuyana abin ya bani girgiza ni. Anty Aysha ce sai huci take tana hararata, gaban rigata na Æara kallo in da ta cukume da kyau, kafin nayi magana Anty Aysha ta riga ni da cewa, "don bura'ubanki wacece ke?, wanne kalar jahilci ne cikin kanki?, uban me kike gadara da shi a cikin gidan nan da kike ganin kin isa ki yi kowanne kalar iskanci ki zauna lafiya?, to koma me kike ji da shi yau zan banbance miki tsakanin aya da tsakuwa, zan sauke miki kowanne kalar buyagi Sa'ida, tabbas yau za ki ciji yatsa kina me nadamar abin da kika aikata don kutumar ubanki".
baki sake na ke kallonta da maÉaukakin mamaki, ba kalaman ba ne su ka shige ni, zagin shi ya girgiza ni. ko ban kasance matar Æaninta ba ina ganin ai babu dacewa ta danÆara min zagi na rashin Éa'a irin haka. sai dai kafin na kai ga wani motsi Yaya da ta iso ta Éauke ni da gigitaccen marin da ya kai ni kifewa Æasa, sai dai nayi jarumtar riÆe kaina a tsaye.
kuma kafin zafin marin ya sakeni ta Æara min wani ta Éaya Éarin, wanda a ruÉe na Éago ina ÆoÆarin Æwace riÆon da Anty Aysha tayi min inyi ta kaina.
ganin hakan Yaya tace,"Au ÆoÆarin Æwacewa ma kike?, guduwa za ki?, To bara nayi miki dukan tsiya sai naga da wanne Æarfin za ki Æwace ki gudu, Sa'ida ai yanda kika kwantar min da Yarinya a asibiti kema sai na illataki wallahi".
tana faÉin hakan ta fara dukana, duk inda hannunta ya kai a jikina nan take duka kamar wacce ta samu ganga, ni kuma duk wannan bala'in da na ke ciki tunanina ba ya ga in Æwaci kaina ko in Éau matakin cin zarafin, a'a hankalina da tunanina na kan furucinta na cewa na kwantar mata da Æ´a a asibiti, wacce Æ´ar?, mene dalilin kwanciyar?, kar dai sharri yaran su ka haÉa min?, waÉannan su ne tarin tambayoyin da ke cikin kaina kuma amsarsu kawai na ke da buÆata.
sai da na farga daga hallakanin da suke shirin yi tukunna na fara kiciniyar Æwatar kaina, amma ina sun riÆe ni gam sai dukana su ke babu ta yanda za'ai na iya Æwacewa kun san ance sarkin yawa yafi sarkin Æarfi.
"Yaya ki daki cikin shegiya tunda babu uwar komai a ciki sai kashi".
Anty Aysha ta faÉa tana kallon Yaya. Ai kuwa kamar Yaya na jiran tuni akan hakan ta dunÆule hannu ta daki cikina da Æarfi. "Wayyo Allah!". na faÉa da Æarfi jin azaba wacce ban taÉa jin irinta ba a cikina.
cikani Anty Aysha tayi ta duÆa ta Éaga Æafata nayi baya na kifa Æasa, ta saka Æafa ta dakar min kwankwaso, a wahalace na runtse ido ina kuka amma hakan baisa sun daina dukana ba. da dukkan iyawata na tattaro Éan Æarfina na ture su daga jikina, naja baya da sauri ina Éoye kaina.
idonuna masu zubar da zazzafan hawaye ya tsaya cak akan Yaya wacce ke numfashin wahala tana girgiza, yanda take abin ba zaka taÉa sanyata cikin sahun manya mutane ba, ba Æaramar mace ba ce, sai ÆwaÆwalwarta kawai da ke aiki da Æarancin shekaru, zancen da na ke muku tana kan shekaru arba'in da Æ´an kai ne.
"bagidajiya Æ´ar gidan Æananun mutane, shashasha wacce bata ajiye komai ba. ke har kina da ikon hana Æ´armu abinci a cikin gidan Æaninmu?, wawiya kawai, ba ki san da cewa ta fiki dajara da Æima a idanun mai gidan ba?, ko mancewa ki kai da ana rabuwa da uwa a zauna da ƳaÆ´a?...ko kuma ganin an zuba miki ido kina zaune ke