in abin da kika aikata a yau, wawiya mara aiki da iliminta".
fita yay daga Éakin yana ta surfa masifa, na daskare wuri Éaya ina bin bayansa da ido, Æirjina naji ya matuÆar yin nauyi, me na yiwa Hubbi a wannan rayuwar ne?, wanne kuskure na aikata masa da ban cancanci yafiyarsa ba?, mijina me kyan hali da nagarta ne, ta ko'ina amfani da yake da tarin ilimin addininsa, amma me ya sauya shi?.
ban san lokacin da na zamo daga gefen gadon ba gwiwoyina su ka dire a Æasa, na fashe da matsanancin kuka. me yasa aurena zai tashi daga rayuwar farinciki ya juye zuwa rayuwar baÆin ciki?, mun auri juna ne don muna son juna, mun fuskanci Æalubale da yawa tun daga haÉuwarmu har aurenmu, duk tarin Æalubalen da muka fuskanta bamu taÉa ji a ranmu cewa zamu haÆura da juna ba haka har muka yi nasara, amma me ya kawo canjin a lokaci farat Éaya haka?, lokacin da ya kamata ace munji daÉin rayuwarmu, mun dulmiya cikin kwanciyar hankali da natsuwa.
Haihuwa!, kalmar ta motsa da zuciyata, kenan yau da zan haihu shikenan komai zai sauya?, kowa zai koma sona tamkar a baya?, za'a daina tsangwamata da tashin hankali?, idan kuma ban haihu ba shikenan haka za'a ci gaba da tafiya?. zuciyata ce ta fara jujjuya tunanika, wa ya kamata in kira in shaida masa halin da na ke ciki?, wa zan sanarwa da cewa rayuwar aurena ta juya cikin tsananin baÆin ciki da Æuncin da ban taÉa tsammani ba, wa zan kira ya lallashe ni ya bani haÆuri da shawara?.
mahaifiyata ce ta zo cikin kaina, sai dai ba zan taÉa iya kiranta in sanar mata da matsalar nan ba, ba zan iya faÉa mata matsalar gidan aurena ba, na Æwammaci in zauna a hakan ko zan mutu in mutu, har kullum farin cikin iyayena da kwanciyar hankalinsu na ke so, saboda haka ba zan taÉa bari su san halin da na ke ciki ba.
kai na kifa a gefen gadon, idona a rumtse yake kalaman cin mutuncin Hubbi nata yawo cikin kaina, lokaci guda kuma wani lokaci ya haska a cikin idanuna, yayin da wasu kalamai na lokacin su ka haska tarr a cikin kaina, jinsu na ke suna amsawa a ÆoÆon kaina tamkar yanzu yake faÉar su.
_"na yi miki alÆawarin zan tsaya a tare da ke a kowanne irin yanayi, nayi miki alÆawari cewa duk wata matsala ta hanyarki ni zata fara fuskanta, na yi miki alÆawari zan ba ki kariya ta kowanne gefe, na yi miki alÆawari ba zan taÉa bari idanunki su yi hawaye ba, na yi miki alÆawari a kowacce rana zan yi ÆoÆarin dacewa da ke, ba zan juya miki baya ba, ba zan taÉa canja miki ba, nayi miki alÆawarin cire ki daga duk wani baÆin ciki, nayi miki alÆawari Sa'ida! daga yau da kika zamto matata, dukkan soyayyata, amanata da rayuwata naki ne ke Éaya, ina sonki Sa'ida, alÆawarin dawwamammen farin ciki Habibty"._
waÉannan sune kalaman da yay min a ranar Éaurin aurenmu, bayan Éaurin aure san da suka zo gidanmu gaisuwar surukai, na same shi a Éakin Yashaik kafin a gama kimtsa cikin gidan su shiga. lokacin da na shiga na tsaya na kasa zama wurin da yake min nuni saboda kunya, wanda hakan yasa shi tasowa ya tsaya gabana tare da kamo hannayena duka biyun ya saka cikin nasa ya haÉe, kaina na Æasa a wannan lokacin amma haka ya Éago fuskata da dogon hancinsa, ya tilasta min saka Æwayar idona a tasa kafin ya shiga karanta min waÉancan kalaman fuskarsa na me washewa da dukkan murmushin farin ciki da jin daÉi gami da alfahari.
sabbin hawaye ne masu zafi suka shiga zubo min, a raina ina tambayar duk ina wannan tarin alÆawarin da yay min?, shin mantawa yay ko kuma fatali yay da su?. doguwar ajiyar zuciya na sauke tunawa da farkon rayuwar aurenmu, sai kawai na saki murmushi me ciwo, ko ba komai ai nayi farin ciki tare da shi ko ya ya ne, ina alfahari da iyaka wannan ma.
tsaida kukana na yi na miÆe na shiga banÉaki na wanko fuskata, na gyara jikina sannan na fita jiki a saÉule, tunanina me zan dafawa yaran cikin ÆanÆanen lokaci, amma me daÉi wanda zai gusar da rashin jin daÉinsu, abincin da su ke matuÆar so na tuna, wanda hakan yasa na sauka daga benen cikin karsashi, sai dai da zuwana Æofar kitchen na murÉa handle naji ta a rufe, na zaga ta Éaga Æofar itama a rufe.
doguwar ajiyar zuciya na sauke, kenan da gaske ya ke akan furucinsa na zai hukunta ni akan barin Æ´aÆ´ansa da nayi da yunwa. yanda ban ba su sun ci na safe ba haka kenan nima yau zan wuni babu ci?, dama ana horo da yunwa?.
kan kujera na koma na zauna na rafka tagumi, jefi jefi sai na sa hannu in goge hawayen da ke sakko min, tunani na ke yi daban daban, sai dai akan kowanne na rasa irin warwarar da zan masa. na kalli agogo naga Æarfe goma da minti sha biyar, kuma kaÉawar lokacin ya haÉe da Æugin da cikina yay saboda tsabagen yunwa, dama banci na daren jiya ba, lokaci guda dukkan tunanina ya tsaya cak, take kuma nauyin kaina ya dawo naji yay bala'in sara min, nayi saurin dafewa ina mai rumtse ido tare da jinginar da kaina jikin kujera, wucewar daÆiÆu uku na m