NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 27 of 97

une cikin tsananin azaba, cikin dauriyata na yunƙura zan sauko Rumana ta ce. "Anty ki koma ki kwanta, a bamu kuɗin makaranta idan mu ka je sai mu siya snacks kafin a shiga class, ba zamu iya cin sauran abincin jiya ba". na san yanzu Hubbi bai tashi ba, don haka nace da ita,"duba ƙasan littafin can akwai ɗari biyar ku ɗauka". ɗari biyar ɗin kenan na ke ta ririta ko da wata buƙata ta ujila zata taso min. ta ɗauko tana faɗin babu canji, na ce suje da ita tun da ba su yi breakfast ba, magani nasa ta miƙo min ta fita ta ɗauko ruwa ta kawo min. nayi musu adu'a tare da a dawo lafiya su ka fita, Rumana ɗin ce dama me sauƙi sauƙin kai, don ko yanzu ita ce tayi min sannu tana Allah ya bani lafiya, amma Atika har su ka tafi fuska a murtuke tana ta ƙunƙuni. ni dai zan iya cewa cikin awa guda na kusa shanye sacet ɗin paracetamol, amma duk da haka babu wani sauƙi da na ke ji a tare da ni, ciwon ma tamkar ƙara shi ake yi, hawaye masu zafi ne kawai ke sauka kan kuncina, idan nayi haka zan ɗau waya in kira shi sai in tuna kashedin da yay min, ba kuma na so in kira gidanmu nan ma ya zama fitina, haka dole na haƙura. adua na ke tayi, da kaɗan kaɗan kuma naji ciwon na ɗan raguwa tun da har ina iya buɗe idona, cikin baccin da ke son kwashe ni naji muryar Hubbi daga can nesa na kiran sunana da amon sautin da ya gigita ni ya firgita ni, zan iya cewa ban taɓa jin tsoro da firgici irin na kiran da yay min a yanzu ba, take kuwa na ambaci ƙalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un domin na san kiran bana lafiya ba ne, kafin na kai ga buɗe idanuwana ya banko ƙofar ɗakin, kana jin yanda ƙofar ta bada garam ka san a hasale ya ke. "Sa'idaaa". ya ƙara kiran sunan a tsawa ce wanda hakan ya daɗa gigita ni musamman da na ke jiyo hucinsa kamar mayunwacin zaki. ta cikin bargon da nake ƙudundune na amsa, sai dai bai ma jini ba, ya ƙaraso ciki ya yaye bargon yana sa hannu yay min wata muguwar fincikar da sai ganina nayi tsaye akan ƙafafuna, da sauri na runtse ido tare da dafe bango jin ina neman faɗuwa. na buɗe ido da ƙyar a ɗan runtse na dube shi na ce,"lafiya?, bana jin...". ban ƙarasa furucina ba ya wanka min zazzafan marin da yasa ni zama daɓas babu shiri, a ruɗe na shiga girgiza kai ina kiran sunan Allah, tun da na ke da shi, tun da muke rayuwa gefen rigarsa bai taɓa sawa ya duke ni da ita ba, amma yau mari, marin ma a mawuyacin halin da na ke ciki, ban wartsake daga jin zafin ba ya shiga cewa. "Wacce irin muguwa ce ke mara imani da tausayi, wannan ai tsagoron zalunci ne, banda rashin hankali da tunani irin naki ki bar yara su fita da sanyin safiya ba tare da kin basu abinci sun ci ba, haka babu abincin makaranta, Sa'ida haka aka yi miki da kina yarinya shi ne kike neman hucewa akan yarana?, wato saboda ba ƴaƴanki ba ne, ba ke kika haifa ba shi ne za ki azabtar da su da yunwa, wai me yaran nan su ka miki kika ɗora musu karan tsana?, kawai don ba ke kika haife su ba?, yunwa Sa'ida, kisa fa take yi, ko ke aka bari da yunwa ai an zalunce ki balle ƙananan yara, ba kya tunanin hakkinsu ya biki ya hanaki sukunin rayuwa, yaran nan fa yanzu ni ne mahaifinsu, ko darajata ai sa ci ki sassauta musu, amma saboda dai zuciyarki a mace take, tayi maƙil da baƙin ciki da zalunci shi ne za ki huce haushinki akan su, to Allah ya isansu, kuma ni bazan yafe miki ba...". tun marin da yay min na nemi ciwon jikina na rasa, kallonsa na ke da mamaki ƙarara, idona tamkar an buɗe famfo haka hawaye ya ke sunturi saman fuskata, jujjuya kaina kawai na ke na rasa bakin magana. cikin kyarmar jiki na kamo hannunsa, na san zafin jikina da ya ratsa shi ne yasa shi ware ido akaina, ina kuka sosai na shiga ce masa. "don Allah kayi haƙuri, wallahi ko kaɗan ba da gayya ko mugunta na bari su ka fita ba abinci ba, Hubbi ba ni da lafiya, ba ni da ƙarfin da zan iya tashi, ka tambayesu har kwatanta hakan na yi naji ba zan iya ba, kai kanka ka san in ba lalura ba babu abin da zai kwantar da ni a ɗaki har wa yanzu duk kuwa halin da muke ciki, amma na rantse da Allah ban bari sun fita ba su ci komai ba saboda mugunta ko rashin so ba, Hubbi ban tsani yaranka ba, ban taɓa jin ina ƙin su ba balle har in ƙuduri cutar da su, Allah shahidi shi ne shaidata yanda zan so ɗan cikina haka na ke sonsu, Hubbi ƴaƴan ƴan'uwanka ne fa, kai kuma ɗin nan ina sonka, mijina ne kai, Hubbi don me zan ƙi abin da aka baka?, don Allah ka sassauta fushinki ka ke daina faɗin duk abin da ya zo bakinka...". buge hannuna yay daga jikinsa yana ƙara faɗin,"shashasha kawai, bagidajiya wadda bata san hakkin yaro ba. sai ki laifi da an miki faɗa ki fashe da kuka, a hakan kike sona?, idan kina sona ai ba za ki wulaƙanta ƴan uwana ba, ba zaki ƙi yarana ba. kuma ki sani wallahi tallahi yanda kika azabtar da su da yunwa haka kema zan hukuntaki, Sa'ida sai kin yi matuƙar danasan
🏠