NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 26 of 97

kansu, idan na ce zan fanɗare ba su isa ma su min kallon banza ba, to bana son tashin hankalin iyayena da damuwarsu, sannan kuma ina tsoron abin da zai jawa igiyar aurena samun matsala. duk matsaltsalun da ke ta faruwa da sanin surukata, tun ina zuba ido in ga ta tsawatar akan abubuwan da ƴaƴanta su ke min naji shiru, ga mamakina ma sai na ga tana goyon bayansu, itama ta hau kan layinsu, ƴaƴanta su min, ɗanta yay min, itama tayi min. gaba ɗaya na rasa ta ina ƙiyayyar ta samo asali, na rasa laifina. idan na bada haƙuri sai ya ƙara zama wani babban laifin, abin da na lura da shi ma ba akan rashin haihuwa kaɗai yasa su ka tsane ni su ke tsangwamata ba, akwai wani dalili na su a gefe wanda su ka barwa kansu sani. tabbas babu babban tashin hankali a gidan aure irin ace uwar miji ta sanyo ka gaba, ni a baya ban san wani matsalar uwar miji ba, idan naji ƙawayena suna ƙorafi akan uwar miji sai in ce ku ne dai baku iya zama da ita ba, ku sota tamkar mahaifiyarku sannan ku mata biyayya kamar taku mahaifiyar, to duk sanda na faɗi haka Hassana Tijjani ta kanyi murmushi kawai ta ce Sa'ida ba za ki gane ba, in uwar miji na sonki tana sonki kawai, in kuwa bata sonki to wallahi duk son da ɗanta ke miki zaman auren ba zai taɓa yi miki daɗi ba, in kuwa tana sonki to ko ɗanta bai sonki kya sami ƴar salama, ita uwar miji idan ta sako ki gaba duk wani kalar biyayya da za kiyi mata a banza ne, ashe hakan da su ke faɗa gaskiya ne domin kuwa ga shi ina ga ni, kallon banzanta gareni ya fi tsorata ni fiye da na ɗanta. duk wannan tashin hankalin da na ke ciki iyayena da ƴan uwana babu wanda ya sani, ban taɓa faɗa ba kuma ban taɓa nunawa ba, sai dai kawai fa duk wanda yay min farin sani yana ganina zai ce ina cin matsala, hankalina ba'a kwance yake ba. domin kuwa lokaci guda na fita a hayyacina na ƙara yin wata muguwar rama, nayi duhu duk na sakwarkwace, na zama kamar mara lafiya ƙwaƙwalwa saboda kullum a firgice na ke, haka na ke jin duk rayuwar ta fita a raina, har so na ke dare yayi ɓarawon bacci ya ɗauke ni in sami ƴar salama, don bani da babban tashin hankali sama da wayewar gari, da zarar gari ya waye na shiga fargaba da taraddadi kenan. uhmm so kenan, wallahi duk wannan tsananin da na ke ciki na gidan aurena har yanzu banji soyayyar mijina ta taɓu a raina ba, ban ji ina nadamar aurensa ba, ban taɓa jin ina ma ya sawwaƙe min in huta ba, sonsa na ke da dukkan raina, sam bana fushi da duk abin da yake min, uzuri na ke masa da kuma adu'a, tun bayan aurena da shi ban canja akalar adu'ata ba, kafin na yiwa kaina shi na ke yiwa, ni har na fi so ya zo yana min bambami akan ya shareni kwata kwata babu magana, kuma kullu yaumin bana fasa zuwa neman yafiyarsa da basa haƙuri a kowanne daren rana kafin kwanciyata, zan ta haƙuri ba zan karaya ba, Allah na zan ta faɗawa ya daidaita tsakaninmu, ya kuma bani ikon cinye jarabawar. yau na tashi da matsanancin ciwon kai, hakan yasa na kasa fitowa gaba ɗaya, tun da nayi sallar asuba na durƙufa kan sallaya, bacci ma na ke so na koma amma na kasa saboda gabana da ke ta faɗuwa, ga shi ina so na tashi in je in tada yara su yi shirin makaranta sai dai in na tashi jiri sai ya mayar da ni. da ƙyar dai na lallaɓa na tashi a daddafe na fita, ɗakinsu na shiga, na shiga banɗaki na tara musu ruwan wanka, sannan na fito na tashe su kan suyi wanka. su ka tashi da ƙyar kowacce na faman ɓata rai, zama nayi ina lallashinsu da ba su haƙuri akan cewa watarana sai labari, yanzu ne su ke da dama da lokaci na yin karatu, idan basu yi ba nan gaba za su ciji yatsa. na lallama su da ƙyar su ka sauko su ka wuce banɗakin, na jaddada musu da su yi sallah in sun shirya. ɗaki na koma saboda sanyin zazzaɓi da ya rufe ni, ina shiga na ƙudundune cikin bargo ina ta karkarwa, kaina jinsa na ke kamar zai faɗo, haka cikina ma wani bala'in ciwo ya ke min. ban ankara ba kawai naji amai, duk ƙoƙarina na kar in yi akan gadon hakan sai da ya faskara, amai nayi sosai mai wahalarwar gaske. gaba ɗaya jikina sai ya saki, da ƙyar na kimtsa wajen a wahalce na dawo na kwanta, hawaye kawai na ke zubarwa saboda ni ɗaya na san irin azabar ciwon da na ke ji a jikina. ina cikin wannan halin aka turo ƙofar ɗakin, Rumana naji tana cewa,"Anty mun gama shiryawa". fito da fuskata nayi ta cikin bargon kaɗan, bana iya ko ganinsu da kyau, murya a wahalce na ce da su. "wayata na kan mudubi ƙarfe nawa?". Atika ta duba tana cewa,"seven twenty". idona na rufe, har ga Allah ban da wani ƙarfi da ƙwarin da zan tashi in dafa musu abinci. a hankali na ce da su,"Rumana ban da lafiya, ku yi haƙuri kuje kitchen akwai sauran abincin dare a flask ɗin Abbanku ku ci kun ji, na san bai huce ba. abincin makaranta kuma zan bayar a kawo muku". su ka yi shiru ba su ce da ni komai ba duk su ka yi cirko cirko. tsoron abin da zai biyo baya yasa na miƙe za
🏠