NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 25 of 97

a da yunwar watanni da yawa da ya ɗiba. Cikin wucewar wasu kwanaki lamari ya ƙara taɓarɓarewa tsakanina da mijina, abun ya koma tamkar sa hannu, bai barni da yunwa ba zan ci in sha, amma babu zaman lafiya sam, na rasa kwanciyar hankali da jin daɗi daga gare shi, komai nayi ba daidai ba ne, abinci idan na yi ba ko da yaushe zai ci ba, magana idan nayi sai yaga dama zai amsa min, makarantar tahfeez ɗin da na ke zuwa ya soketa ya ce in har da aurensa akaina na gama zuwa makaranta. idan na zo masa da buƙatar wani abu ranar sai yayi tamkar ya tashi gidan da wuta, ya dinƙa masifa ban da aiki sai shegen tambayar a bani a bani kamar don ni kaɗai ya ke neman kuɗinsa, kullum a nurƙufanci ya ke fuska ba wata walwala, ya dinƙa ƙunci da ɗacin rai, ba zan san fitarsa ba haka ba zan dawowarsa ba. zaman haka na ga ba zai kai min ba na tambaye shi jari, dalilin haka har kuka nayi saboda cewa yay na sakawa dukiyarsa ido, ban da godiyar Allah sam, menene ba ya yi min da har sai na zubar masa da ƙimarsa, salon a ce ya gaza wurin kula da iyalinsa, cuta in zan mutu sannu ba zai ce min ba, haka zan ƙara ci ciwona in warke babu ganin likita balle magani, sai ranar ma da ya ɗan ji tausayina ina matsanancin ciwon kai ya siyo paracetamol kwali guda ya bani wai in aje kar in sake ciwo ya kama ni in zo masa da zancen magani ko asibiti, wannan ya ishe ni ko da ciwon ajali na ke. ya daina tambayata ko shawarar duk abin da ya kamata ya aje a gidansa, sai dai ya kira Yaya, abin da ta ce shi zai yi, to yanzu ma ta ce da shi duk su nama da kayan marmari da ya ke ajiyewa ya daina domin ta lura ina masa almubazzaranci da kayan abinci, kuma ɗiba na ke ina bayarwa ba tare da saninsa ba. abubuwan baƙin ciki su ka taru su ka min yawa, shi na rasa laifin me na masa da duk ya ke ƙuntata min. ya hana ni fita kwata kwata, rasuwar da aka yi ta wata kakarmu ya barni da ƙyar ita ma sai da na sha kuka wajen magiya da roƙo, ita ma ɗin kafin ya bar ni sai da ya gama ci min mutunci da cewa ai idan na fita gulma da munafurci ke kai ni, da koyo fitsarar wulaƙanta aure da dangin miji, tun daga wannan furucin na sa kuwa na cirewa raina son fita ko da gidanmu ne. A ɓangaren Rumana da Atika kuwa, zuwansu gidan ban da matsala da nesanta tsakanina da mijina ba abin da ya haifar, yara su ka zamar min annoba, don zan iya cewa ta silar su ne hargitsi ya girmama a cikin gidan aurena, har akansu ina neman na kamu da ciwon zuciya. ya nesanta tsakanina da shi ya kusanta tsakaninsa da yaran fiye da tunani, da su ya ke shawarar duk abin da zai yi a gidan, ko magana zai min wacca ta kama dole sai dai ya faɗawa ɗaya daga cikinsu ta faɗa min, ga yaran sun raina ni, ba wacce na isa na mata magana sai ta min rashin kunya da fitsara, har kallon idona su ke su faɗa min ai Abbansu ba ya sona su ma don haka basa sona, ko abinci na ba su sai su ce ban iya girki ba ba zasu ci ba, idan ya dawo kuma su gilla masa ƙaryar ban ba su abinci ba, ba zan taɓa baƙi ba ƴaƴan nan su ga baƙona da ƙima su gaishe shi. ranar da na tsawatar musu akan ba su gaida Ya Imam ba, Hubbi na dawowa su ka ce ai na zazzagesu na ce zan koresu a gidan, alhalin kuma sun gaida Yayan nawa amsawa ne bai yi ba. ranar na yi kuka na gode Allah, don zagi na cin mutunci da ƙare dangi yay min a gaban yaran. wannan dalilin na cin zarafina da ya ke a gaban yaran sai ya ƙara ba su lasisin yi min duk abin da suka ga dama, ji na ke har gwara kishiya da su, don su idan su ka kunna wata wutar bala'in ba zaka taɓa cewa yara ba ne kuma ba zaka iya kasheta ba. ga sun iya kirsa abin kamar koya musu ake, a gabansa ladabin da su ke yi min kamar uwarsu, amma da zarar an ce bai gidan duk wacca ta ganni ma sai dai tayi min tsaki, ban isa ko ɗaga murya in yi musu ba nayi hakan na shiga uku ranar, idan suka ɓata wuri nasa su gyara sai yaci zarafina. na yi musu faɗa akan ƙin makarantar da su ke hakan sai ya zama tashin hankali har yana faɗin saboda ba ƴaƴana ba ne ba kuma ƴaƴan ƴan uwana ba ne, ina baƙin ciki yayyuna sun kasa sadaukar min da ɗansu ko guda, shi ne shi saboda an ba shi zan takurawa yaransa, to in cire idona daga sha'aninsu tun da ba ni ke ɗaukar nauyinsu ba. ɓangaren ƴan uwansa kuwa sun taso ni gaba da gorin haihuwa, ba su tsaya iyaka nan ba har faɗi su ke wai me ake da auren ƴan talakawa, sam ba su ga abin da aurena ya tsinanawa ɗan uwansu ba, ban da ma tawaya da yaja masa, da sun san haka aurena zai zamarwa ahalinsu masifa da ba su bari ya aure ni ba. idan na shiga cikinsu tamkar mushe haka suke ja baya da ni suna habaici, a ke min gorin wai ai ko da aka auroni haka na zo babu kayan gara. ƙalilan cikinsu ne ma su tausaya min, sauran duk daga kyara sai hantara da nuna ƙyama, shi yasa na kama kaina na ja gefe domin wulaƙancin na su ya fara min yawa, har bana so abun zuwa cikinsu ya ta so, mugun haƙurina kawai ke sawa na sharesu bana bi ta
🏠