cikina ina rufe idanuwana tare da roÆon Allah ya azurtamu da haihuwa kafin mutuwa.
farin cikinsa ya kasa Éoyuwa, abin da ya siyo musu ya basu suma sai murna su ke yi, wayarsa ya Éauko ya kira Yaya yana Æara yi mata godiya da alkhairinta gare shi, Anty Aisha ma ya kirata daga baya. ya tambayi yaren sun ci abinci suka ce masa ehh, yace to su taso suje Éakinsa, a tare muka fita gaba Éaya muka bi shi, haka naci albarkacin yaran walwalarsa gareni ta dawo, mu ka ta hira kamar ba shi ba da ya canja Æ´an kwanaki, bini bini ya tambayeni me ya kamata a siyawa yaran, ni dai abin da na fara cewa shi ne akai su makaranta da wuri gudun kar ayi musu nisa a karatunsu.
bayan Æ´an kwanaki da safe na fito a wanka, turus nayi ganin Hubbi ya shigo Éakin wanda rabonsa da Éakina har na manta. kallonsa na tsaya yi wanda shima ya ke bina da kallo, to da yake dai tun zuwan su Atika ya Éan sakko tsoronsa ya ragu a raina, muryata a hankali na ce,"ina kwana".
ciki ya Æaraso yana zama bakin gado. "kin tashi lafiya".
"lafiya lau, mun je Éakin ai na tarar baka tashi ba. na Éauki Éari biyu a wallet na bawa su Rumana kuÉin makaranta".
na Æarasa gaban madubi na Éauko takarda Æarama na miÆa masa ina daÉa cewa,"jiya aka basu a makaranta wai sun manta ba su baka ba".
ya kalli takarda yana cewa,"ta mece?".
"ban duba ba".
karÉa yay ya duba ya ajiyeta. sai kuma ya kishingiÉa da gadon yana danna wayarsa. ni dai tun fitowata daga wankan na ke jin tasirin kallonsa na shiga jikina. tun da aka bamu yaran nan naga ya dawo hayyacinsa, kuma alamunsa sun nuna ya gaji da Æauracewa junanmu, so ya ke ya kasance da ni sai dai ni Éin kuma na Æi basa dama da fuska, don ko jiya da naga take takensa na agwiwa ya ke Éaki na gudo.
yi nayi tamkar na mance da shi a Éakin, na buÉe wadrobe na Éebo kayan da zan saka, sannan na Æarasa na zauna kan kujerar madubi, ta cikin madubi na hasko shi idanuwansa sun kafe a kaina. cikin natsuwa na yin komai nawa a hankali na Éauko man shafawa ina shafawa, tun da na shafa humra na hasko ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. na Æarasa kimtsa jikina da turaruka cikin salo na jan hankali, ina gamawa na wuce zan saka kayana sai naji muryarsa a kasalance yana cewa.
"zo".
Éago ido nayi na kallesa naga yanayinsa duk ya sauya. rigar nayi ÆoÆarin sakawa ya sake dakatar da ni da cewa,"ki zo na ce fa".
ina Éata fuska na ce,"Hubbi bari na Æarasa saka rigar...".
sai da na saka sannan na je wurin nasa, ya Éago fuskata yana kallona ya ce,"Habibty fushi kike da ni?".
kai tsaye na Éaga masa kai, sai kuma hawaye ya sakko min. kwanto kaina yay saman kafaÉarsa da cewa,"ba kya kewata?".
cikin muryar kuka na ce,"idan ma nayi kewar taka ya zanyi Hubbi, ka mayarshe ni tamkar ba matarka ta so ba, ka Æi faÉa min dalilinka na Æaurace min, duk na baka haÆuri ka Æi haÆura, ban san laifin da nayi ba ka daina sona".
ya zago da hannayensa ta Æuguna ya ce,"to kiyi haÆuri na san na miki ba daidai ba, afuwan kin ji". yay maganar Æasa Æasa da muryar lallashi.
na Æara cewa,"to me yasa hakan Hubbi?".
numfashi ya sauke ya ce,"saboda ina so inga na sami Éa sai dai ke kuma shiru, naga kamar rashin haihuwar bai damunki, shiyasa na ke ganin mu'amalar tamu ma bata da wani amfani. amma yanzu da na sami yarancan sai na ji kaso saba'in ya yaye na damuwar rashin haihuwar da bamu yi ba. amma kin sani ina sonki, matsayinki bai taÉa canjawa ba daga gare ni, don haka kar ki Æara cewa na daina sonki kinji ko, ni na ki ne na har abada, ke Éaya jallin jal Sa'idan Nazifi".
murmushi nayi ina kallonsa, jin maganganun nasa nayi kamar daÉin baki, sai dai kuma ba hakan ba ne, tabbas shi Éin mai tsananin sona ne duniya kanta zata shaida hakan. sabuwar soyayyarsa naji ta kamani, sai dai na kasa amayar da duk wata magana da ke narke a cikina. duk tarin baÆin cikin da ya Æunsa min naji ya gushe, tabbas ina son Hubbi, ina Æaunarsa, kuma sonsa da Æaunarsa ne yasa zan ci gaba da haÆurin rayuwa tare da shi Éin, domin a Æ´an kwanakin nan kaÉai na lura soyayya da komai nasa da ya tattare ya Éora akan yaran can zai iya haifar min da babban Æalubale.
"ya kamata mu sha soyayyar da zata mantar da mu komai da ya faru, komai Éin ya zama tarihi".
ya katse tunanina da faÉin hakan. kuma lokaci Éaya naji yana tattare rigata zai cire. lokaci guda ya fara aika salonsa ga jikina, tuni kuma na biye masa muka faÉa cikin duniyar jin daÉin ma'aurata, mun daÉe kafin mu sami natsuwar da muka rasa na tsawon watanni. da mamakina muna gamawa ya tashi ya fita a Éakin ko wanka bai tsaya yayi ba, saÉanin da anan yake wankansa, wataran ma tare mu ke yi, mamakin hakan ya tsaya min a rai.
na miÆe cikin gajiyar jiki na shiga wanka, ko bayan fitowata kasa komai nayi sai kwanciya saboda ba Æaramin gajiyar da ni yay ba, sai da ya Æosar da kans