NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 23 of 97

daɗi, har sai kunnenki yay rawa". su ka ɗanyi dariya Rumana na cewa,"ferfesun kaji?". kai na gyaɗa na ce,"ehh har da shi, sai kuma dashishi". Rumana na tsalle ta ce,"irin wanda Ummaa ke yi?". na ɗaga mata kai tabbacin haka. duk ɗin su suka kama murna, ina riƙe da hannayensu muka wuce kitchen. a tray na zuba musu na sanyo musu ferfesun naman kazar a bowl, su ka taya ni ɗauko wasu muka fito, nan kan carpet na ajiye musu su ka zauna su ka fara ci ni kuma na juya kitchen ɗin don zubowa su Yaya na su. kiran Hubbi ya shigo wayata na ɗaga ya ke shaida min ga masu furnitures ɗin nan sun zo. na fita na hau saman na shaidawa su Yaya, sai sannan na ke ƙara ganin ashe ma basu kaɗai ba ne har da nasu baƙin wanda su ka zo da su suyi musu gyaran. cikin su biyun dai babu wacca ta tanka min bayan waɗancan da su ka gaishe ni. na juyo na sakko ina faɗawa me gadi yaywa ma'aikatan iso, ai na fita hakkinsu tun da na sanar musu za'a shigo. ina ɗakin Hubbi na jiyo muryar Yaya na kwakwazon faɗa,"mene haka na ke ganinku zaune a ƙasa kamar wasu almajirai, don me Nazifin ya siyo wancan dining ɗin ya ajiye, ko dama na kwalliya ne?, kai ku tashi ku koma can ku ci abinciku, kar a ƙara baku abinci ace ku zauna kan kafet ku ci. ba baƙi ba ne ku, nan gidanku ne gidan Babanku, kuyi yanda kuke so yanda ku ka ga dama kar ku ji shakkar yin komai, duk abin da ku ke so kuyi magana da Babanku, idan Antyn tayi muku wani mugun abun ku dinga faɗa masa kun ji ko". sai kuma Anty Aisha ta ɗora da faɗin,"umm ni dai Yaya ban da kin ce wallahi yaran nan ba za su zauna ba. ji fa don Allah yanda aka barsu su kaɗai a falo kamar wasu marayu, wallahi ko baƙo aka yi sai ya ce ƴaƴan ruƙo ne bana gida ba, don an bambamta ƙiri ƙiri. to ni dai har ga Allah ina ganin wani canji da ban gamsu da shi ba zan zo in ɗauke yarinyata, ba zan cutar da kaina ba akan yiwa ƙanina kara". da babbar murya Yaya ta ƙwala min kira, kamar wacca aka hankaɗo daga ɗakin sai ga ni na fito jiki sai ɓari ya ke yi. a dabarbarce na ce,"kun sauko, ga abincin...". "ke dilla can dakata banza mara mutunci, ba yunwatattu ba ne mu, da fari ma in tambaye ki, nan gidan waye?". kaina a ƙasa murya na sarƙewa na ce,"gidan aurena". tayi wani makirin murmushi da sake cewa,"to gyara zancenki, domin ko yanzu ba sai anjima ba kina iya barin gidan nan ki tafi a fanko, nan gidan Nazifi ne, Nazifi kuma ƙanina ne, ba ƴan uba mu ka haɗa ba uwa ɗaya uba ɗaya tafi gaban wasa, duk abin da yake mallakina yana da iko da shi kamar yanda duk mallakinsa ina da iko da shi. soyayyar da mu ke yi masa da tausayinsa yasa mu ka ɗauki ƴaƴanmu mu ka ba shi, wannan yaran da kike gani ba bare ba ne yanzu, ba ki da ikon kallonsu ki ce nan ba gidan ubansu ba ne balle kiyi musu iyaka da shi, yanzu Nazifi ne uwarsu ubansu, su kuma ko yau Nazifi ya faɗi ya mutu sun zama magadansa. saboda haka kinga kuwa sun fi ƙarfin ki ci mutuncinsu, ba marayu ba ne ba ƴaƴan kishiya ba ne ba kuma ƴaƴan tsintuwa ba ne. ko da kika ganki matar gida ba wai ke aka bawa su ba, mai gidan aka bawa, don haka ki tsaya iyaka matsayinki". ni dai take takensu da na lura yasa naja baki ban ce kanzil ba, don haƙurin ma idan na bayar zai iya zama wata rigimar, ƙarshe ma ƙanin na su ya dawo su haɗa masa ƙarya da gaskiya, shima ya juye min nasa rashin mutuncin. yaran su ka tashi daga inda su ke suka bi bayan budurwar da Yaya tasa ta kwashe abincin nasu ta kai musu kan dining, can su ka ci gaba da cin abincinsu. yayin da su kuma su ka koma saman don ƙarasa gyara ɗakin yaran. ni dai tun da nayi komawata ɗaki ban ƙara fitowa ba, ina jin duk wani kai komo na su da su ke yi, ba wasu yawa gare su ba amma yanda ka san masu jeran kayan amarya duk sun cika gidan da hayaniya. qur'ani na ɗauka ina karantawa don shi zai mantar da ni babinsu, sai bayan sallar la'asar na daina jin motsi, a sannan ne na fito na lura da sun tafi, tafiyar da ko arziƙin sallama ban samu ba. ɗakin yaran na buɗe na leƙa, zaune na gansu kan gado ɗaya suna kallo. Atika tayi murmushi da ganin nawa ita kuwa ɗayar ta haɗe rai tana juyar da fuska gefe. na ƙarasa wajen na su, ɗakin na su yay kyau, gadon yara ne guda biyu aka saka kowacce da nata, sai drowern kayansu ma kowacce da nata, ɗakin ya burgeni sosai kam dan dama in ta ɓangaren gyaran gayu ne Anty Aisha ba daga nan ba, zama nayi cikinsu ina masu hira wanda har sai da Rumana ta saki ranta, dama ita ce me bakin magana, nan kuma aka shiga bani labarin ƙawayen makaranta da malamarsu me sa kamun kunne, har tana faɗa min tun da sun dawo nan ga makarantar da zan ce Yaya Ƙarami ya saka su. a haka Hubbinya dawo ya same mu, annurin fuskarsa kaɗai ya shaida min yana cike da tsananin farin ciki, sai naji tausayinsa duk ya kama ni, ya kenan yau in ace ɗansa ne na cikinsa?, hannu na kai saman
🏠