ri ta Hindatu".
wata wawiyar ajiyar zuciya na sauke ina hamdala ga ubangiji, yayin da Hubbi su ka shiga gaisawa da ita yana shaida mata rikicwar da nayi akan rashin Éaga kiran nata, bayan sun gama Æ´ar hirarsu ya miÆo min yana murmushin leÉe tare da tsokanata, wanda hakan ni kuma yasa raina sanyi, domin rabona da ganin annuri a fuskarsa har na manta balle kuma murmushi irin haka.
cikin wani irin jin daÉi mara misaltuwa mu ke waya da mahaifiyata, kira kawai tayi taji ya muke, ashe ma ko da ta bar min miscalls da yawa ba ita tayi kiran ba Yahanasu ta bawa, ita kuma dama bata iya kiran hankali ba, kusan kullum sai Abba yay mata faÉa akan hakan. muna wayar naji duk damuwata ta gushe, tana ta bani labarai masu daÉi, ni kuma ba ni da wani labari da zan bata wanda zai sanyata farin ciki, sai da naji muryarta ta fara sauyawa wadda ke shaida min tana ÆoÆarin gano cewar ina cikin matsala ne, sai nayi saurin gusar da tunanin hakan a ranta nima na bata labarin su Atika da aka bani, ina shaida mata cewar ma yau za a kawo su, aiko farin ciki kamar tayi me, taji min daÉi sosai tana ta yiwa su Yaya godiya da shi albarka, ta ce ma na bawa Hubbi shima tayi masa murna, ni kuma tayi min nasiha sosai a game da ruÆon yaran. sai kuma kawai naji ta koma ambaton wannan kyauta ce daga Allah na sameta ya bani ta silar wasu, na riÆe Æ´aÆ´ana da amana kar in cutar da su, yarda da aminta cewar zan kula da su yasa har iyayen yaran suka bamu duk da cewar sun yi domin Éan uwansu ne, amma duk da haka don suna da yaÆinin matarsa mutuniyar arziÆi ce yasa su ka ba shi.
nasihohinta su ka karayar min da zuciya sosai tun ma inji tana ambaton Æ´aÆ´anki, sai na dinga jin wani irin yanayi na tsarga min a dukka jikina, haka zuciyata ta dinga motsawa, ban san ma ta yanda zan kwatanta abin da na ke ji ba a tare da ni. hawaye naji na sakko min, nasiharta ta Æarshe abin da tace min,"ki so su tamkar ke kika yi naÆudarsu, kar ki cutar da su, kar ki dinÆa musu kallon ba ke kika haife su ba, ki kuma yi haÆuri da duk halinsu domin ko Éan da ka haifa sai kayi haÆuri da shi, Allah ya tayaki ruÆo ya albarkaci zuri'a, idan kina da rabo kema Allah ya kawo lokacin muna raye".
da haka muka yi sallama da ita, kuka sosai na saki, sama sama Hubbi ke lallashina da ike ma yaji duk wayar tamu. haka na miÆe ina jina wani iri na shiga aikin tarbar Æ´aÆ´ana, har na hau sama zan fara gyara musu Éakinsu sai kuma na ga dai gwara in fara Éora abincin. na sakko na shiga kitchen.
ba ni na gama girki ba sai azahar duk da cewa da wuri na Éora, to amma da yake dashishi ne yafi dambu wahala shiyasa na jima. ina kitchen Éin ne na ke jiyo kamar tashin hayaniya daga falo, na wanke hannuna na fita cikin sauri.
tsaye na tarar da su Anty Aisha. da fara'ata na ke gaisheta, ta amsa min babu yabo babu fallasa. hannu na buÉewa su Rumana ina murmushin jin daÉi, jikina su ka shige ina rungume su tsam. ba tare da sani ba naji saukar hawaye a kumatuna, na janye su a jikina muna gaisawa da su, yaran suma sai murna su ke yi, dama dai in dai yara ne suna son zuwan gidan Yaya Æarami.
Anty Aisha ta ce,"ce na ke gidan ma ba kowa da mu ke ta sallama ba'a amsa ba, wannan ai sai a shigo ayi sata ba ki san anyi ba".
shirunta ya haÉe da sakkowar Yaya daga saman bene, tana watsan wani kallon banza ta ce,"da kina ciki amma kina jin mutane kika kasa fitowa".
"wallahi Yaya banji ba, da yake na kunna radiyo ne ina girki. sannunku da zuwa".
"yauwa". ta amsa a daÆile kafin ta Æara cewa,"Baban yaran nan ya ce Éakinsu na sama, na hau da kayansu kuma naga ba wani Éaki gyararre".
cikin fargaba na ce,"ehh Éakin kusa da nawa ne na su, aikin da na ke yi ne ma yasa ban samu na gyara musun ba. da ike za'a kawo gadajensu to su ma masu kawowar shiru naga basu zo ba".
Anty Aisha ta ce,"gyara ya hau kanmu kenan, to bara muje mu gyara musu...".
na yi saurin tarar numfashinta da cewa,"haba Anty Aisha ban isa ba, saboda su wallahi na ce gwara in gama dafa abincin. amma ai nama gama yanzu zan je in gyara musu".
ta wuce ni tana faÉin,"a'a gwara dai kiyi abin da kika saba ki dafa kici ki kwanta. ni ai bana iya tafiya in bar su haka ban ga sun sanya haÆarÆarinsu a makwanci ba, ba zan samu sukuni ba sam, ba da sauÆi nayi naÆudar ba, don ma dai Nazifi ne ban da haka ai wallahi da Æ´ata zan juya. ka yi sadaukarwar abin da ka haifa sukuntum guda kuma tun ba a je ko ina ba an nuna maka kulawa zata yi wuya, ko da ya ke sanin ciwon Éa sai wanda ya haifa. Yaya ni nayi nan".
zuciyata ta matse sosai da zafi, na mayar da ruwan hawayen da ya cika idona, ban iya cewa komai ba, Yaya ta bi bayanta su ka haye saman su ka bar ni nan da yaran. na maida kallona ga yaran da ke tsaye a gabana, na dafa kafaÉunsu ina ÆaÆalo murmushi na ce,"yaran albarka in zuba muku abinci?".
Atika ce ta ce,"Matar Yaya Æarami me kika dafa?".
na kama kumatunta ina cewa,"abu me