aga min hannu,"kuma a hakan kike tunanin za ki fita, makarantar fin mijinki muhimmanci tayi ko me?. to dawo babu in da za ki je sai kin yi duk abin da kika saba kafin ki fita, in kuma ba haka ba ki haÆura da zuwan gaba Éaya kyaje gobe".
sai kuma can yay gajeran tsaki ya ce,"ke bama za kije ko ina ba, yau na soke zuwan".
cikin sadda kai na ce,"don Allah kayi haÆuri Hubbi, wallahi bana so nayi fashin zuwa, bari nayi sauri na dafa maka, me zan Éora?".
na faÉa ina kallon agogon da ya kaÉa Æarfe tara har da minti goma, to yanzu ko da ace ma fitar nayi kafin in je makarantar ai tara da rabi ta wuce, kuma a dokan makaranta minti biyar ka Æara ba zaka shiga aji ba, kuma ba za'a barka ka dawo gida ba sai dai ka zauna a waje har lokacin tashi, don ma matan aure ne mu ba yanda su ka iya wajen duka. haÆura kawai nayi na cire hijabina na ajiye, na je na mayar masa da kuÉin da na Éauka.
"dashishi za ki dafa da rana, akwai tsakin alkamar ko?".
"ehh akwai".
"to ki dafa da yawa saboda akwai baÆi".
na amsa masa da,"to". zan fita a Éakin ya dakatar da ni da cewa,"ki gyara Éakin kusa da ke na sama, Rumana da Atika za su dawo wajenmu, anjima za'a kawo su ko idan na fita in Éauko su. na sa a kawo musu gado, ban san lokacin da za su kawo ba idan ina nan shikenan, in bana nan sai ki kula".
tamkar an kafe ni haka nayi Æyam a tsaye da jin furucinsa, Rumana da Atika!, za su dawo gidan nan da zama?. anya kuwa?, Hubbin da ya ce ba zai taÉa riÆe Éan wani ba saboda mahaifiyarsa ta riÆe bata ji da daÉi ba, don haka shi ma matarsa ba zata riÆi Éan kowa ba saboda sanin halin Éan ruÆo da ke da wuyar sha'ani. to amma ta ya akai farat Éaya haka ya ce yaran za su dawo gidan nan?.
ya katse min tunani da cewa,"kika kafe ni da ido, Rumana ce Æ´ar gidan Yaya sai Atika Æ´ar Anty Aisha, cikinsu wa ye baÆon fuska a wajen ki?".
a rauna ne na ce,"duk ba baÆuwar fuska, amma Hubbi gaba Éaya gidan nan za su dawo ko hutu za su zo?".
"iyayensu sun bar min su halak malak, kinga kuwa ba hutu zai kawo su ba. zan koma Babansu ke kuma Mamarsu, sai ki shirya tarbar Ƴaƴan da aka ba ki".
ƳaÆ´an da aka ba ki! kalmar ta Æarshe ta daki Æirjina. Rumana da Atika, gaba Éayansu ba su wuce shekaru takwas ba, yaran ba su kunya ga rashin ji shisa jininsu ya zo Éaya, ko iyayensu kuka su ke da halinsu, shi ne ni kuma yanzu zai ce zai Éauko min su in riÆe a wannan sanyin halin nawa?, salon wataran su fusatani in sauke musu fushina in Æara baÆin jini, dama ya lafiyar kura bare an taÉota. na san dole akwai wata a Æasa, sai dai ina roÆon Allah ya Éora ni a kansu, ya kuma sauya duk wata baÆar manufa da aka Æulla akan hakan.
murmushi na ÆaÆalo na ce da shi,"ai ko dai muna godiya matuÆa, Allah taya mu ruÆo, naji daÉi sosai, ko ba komai ma rage kewa".
na faÉa ina nuna jin daÉin da bai kai har zuci ba, domin cike na ke da fargabar rayuwarmu tare da yaran.
bai ce da ni komai ba yay shiru, na sauke ajiyar zuciya na fita daga Éakin. Éakina na koma na canja kaya, dama a falo na bar jakata da wayata, kuma da zuwan nawa na tarar da kiran Ummani, sai naji gabana ya faÉi ganin miscalls har guda biyar, take na fara tunanin anya lafiya don bata taÉa min miscalls irin haka ba, Ummani duk in da ta kira waya sau biyu ba'a Éaga ba haÆura take yi, sai tace bata san uzurin mutum ba, idan ya gani zai biyo baya.
zama na yi kan kujera jiki na rawa na bi bayan kiran, sai dai ko da kiran ya tafi a lokacin kamfani ke shaida min bani da kati. Æaramin tsaki nayi na Æorafi tuna fa ashe tun shekeranjiya muna waya da matar Yashaik katin ya Æare.
ina zaunen Hubbi ya fito, ina kallonsa Éacin ran hana ni zuwa makaranta ya Æaru, na kawar kawai na kasa share shi saboda ina so ya bani aron wayarsa. cikin shakkar masa magana na ce,"Hubbi don Allah aron wayarka in kira Ummani".
yana zama kan kujera ya ce min,"me ya sami taki?".
"babu kati".
har zai miÆo min wayar tasa sai kuma ya fasa ya ce,"bari in saka miki katin, wanne layin?".
"Airtel Éin".
cikin wasu Æ´an sakanni sai ga saÆon katin Éari biyar ya shigo, nayi masa godiya sosai. na danna lambar Ummani na kira sai dai haka ta gama ringinga har sau biyu ba'a Éaga ba. take gabana ya tsananta faÉuwa, ban san lokacin da nayi mazauni a gefen Hubbi ba ina damÆar gefen rigarsa.
"lafiya?".
a ruÉe kamar zanyi kuka na ce masa,"bata Éaga wayar ba ne, kuma kaga miscall Éinta biyar na tarar".
ganin yacca jikina ya Éauki Éari ya karÉi wayar daga hannuna, yana ÆoÆarin Æara kiran sai ga kiran Hindatu na shigowa. ya Éaga ya miÆo min amma sai na kasa karÉa don ban san me kunnuwana za su jiye min ba. shi ya amsa kiran sai dai maimakon muryar Hindatu naji muryar Ummani na cewa,"Sa'ida ina hanya ne shiyasa ban Éaga ba, kuma na shigo gidan babu kati a wayar sai na a