NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 20 of 97

domin na san komai nufin ilahu ne". Bai ce da ni komai ba, har tsawon wani lokaci duk mun yi jungum jungum, janye jikinsa yay ya miƙe akan gadon. lokacin nima na tashi jiki a sanyaye, har ga Allah ina son kusantuwa ga mijina, nayi kewarsa da soyayyarsa. "Hubbi". Na kira sunan nasa murya a hankali. "Ina jinki". hannu na kai na kamo nasa ina cewa,"Hubbi mu da muke son haihuwa kuma mu ke raba makawanci, mu ka sani ko rabon samun cikin na a dararen da muka tsallakewa". Muskutawa yay ya gyara kwanciyarsa da cewa,"ba'a ɗau ciki a darare kusan dubu uku ba sai a dare ɗaya?, mtssww ni bani da matsala da rashin kusantarki haka kema na san ba ki da matsala za ki iya riƙe kanki, me amfanin mu'amalar da ba za'a ɗau ciki a haifa maka ba...mun gama maganar zan yi bacci". Miƙewa nayi zan bar ɗakin ya ce,"ina kuma za ki?". "zan je in kwanta ne". "nan ba wurin kwanciya ba ne?". na waigo na kalle shi ban ce komai ba. cikin muryar ɓacin rai ya ce,"Malama kar ki buɗe min ƙofar ɗaki". numfashi na sauke, nayi tattaki gaban wadrobe na buɗe na ɗauko kayan baccinsa riga da wando na saka, gadon na hau na kwanta nesa da shi, ina jinsa yana tofemu da adu'a kafin yaja bargo ya rufe mu gaba ɗaya. washegari da asuba muna cikin karatun ƙur'ani ni da shi, wayarsa da ke kan gado tayi ƙara, na yunƙura na miƙe naje na ɗauko masa, sai dai ganin sunan Yaya a jiki nayi mamaki matuƙa da tambayar kaina kiran ko na lafiya da farar asuba haka. tun bayan sallamarta da ya amsa da gaisheta da yay naji yay shiru bai ƙara cewa komai ba, sai dai ina iya jiyo sautin maganarta amma bana ce ga abin da take cewa ba, tayi kusan minti biyu tana magana can naji ya ce da ita. "ehh mun je, bamu dawo da wuri ba ne sai dare, sai na fito zan biyo ta nan ɗin". yay shiru kafin ya ƙara cewa. "sai na zo ɗin dai Yaya". ya ƙara yin shiru na Æ´an sakanni kana ya ce,"tom shikenan ba matsala. Allah ya ƙara lafiya, a gaida yaran". ba don karatun ƙur'ani mu ke ba bana tunanin zan iya ci gaba da zama, saboda yacca lokaci ɗaya naji gabana na faɗuwa tun gama wayar tasu, to gwarama in ci gaba da karatun ko ba komai damuwa da ɗacin ƙasan zuciyata sa wanke. da yake yau asabar ban koma baccin safe ba kasancewar akwai tahfeez, ƙarfe tara mu ke tafiya sai ƙarfe ɗaya, kuma bana tafiya sai na girka na rana na ajiye masa, ga shi yau ɗin ya ce kunu da ƙosai yake son ci, bayan ya san bamu da garin kunu da ƙosai a ajiye, ya dai ɓata min lokaci da rai kawai, saboda haka yana gama min ƙarin karatu na shiga kitchen. sai a lokacin na jiƙa gero, sannan na shiga gyaran waken ƙosai, Allah yasa ma akwai bilenda ban da haka da ba ƙaramin lokaci zan ɗauka ba kafin in gama, kuma rashin gamawar da wuri ya zamar min ɓacin rai tun da shi ƙa'ida ne cin abincin safensa kafin ƙarfe takwas, in har kuwa ya wuce haka sai in ba lafiya ko kuma wani ƙwaƙwƙwaran dalili. sauri sauri na ke tayi na gama ganin takwas ta doso, ga shi ko abincin ranar ma ban samu na ɗora ba, dole haka zan bari sai na dawo tun da kunu da ƙosan da yawa kuma zai riƙe masa ciki har in dawo. na kwashi kayan abincin na kai ɗakinsa na ajiye, tashinsa nayi na sanar masa sannan na koma ɗakina, wanka nayi na shirya cikin uniform din makarantata, ganin yanda lokaci ya ƙure na sakko a gaggauce. ina komawa ɗakinsa na tarar har ya gama karyawa, nima yunwar na ke ji sai dai ina tunanin zama in ci gudun ƙara ɓata lokaci. tun da na shigo bai ɗago ido ya kalle ni ba, zama nayi na zuba kaɗan na ci, ina kammalawa na dube shi na ce,"Hubbi na gama". kallona ya tsaya yi da tambayar,"ina za ki je?". mamakin tambayar yasa na kalli jikina don in ga ko bai lura da yunifom ɗin da na saka ba ne, tambayar ta shi ta rainin hankali ce, kawai lurar da nayi so yake ya ce ba zanje ba, ko kuma ya tabbatar min da na daina zuwa makarantar, kuma take tsoron hakan ya kama ni. fuskata a narke na ce masa,"makaranta mana Hubbi, yau fa asabar". idonsa ya mayar kan waya yana faɗin,"ohh na sha'afa ne. ki ɗauki kuɗin mota yau ba zan sami damar kai ki ba". hakan ma ya wadatar ni kam a wajena, ai da ya hana ni zuwa gwara bai kai ni ɗin ba tun da duk tsiya dai zan iya zuwa da kaina. kawai dai nayi mamakin rashin kai ni ɗin. tashi nayi na je na ɗauki wallet ɗinsa, na buɗe ina cewa. "nawa zan ɗauka?". "nawa ne kuɗin motar dama?". "ba na ce ba tun da kaga ban taɓa zuwa daga nan ba". "ɗauki ɗari biyar". na san kuɗin ya wuce haka zuwa dai da dawowa, kuma shi ɗin ma ya sa ni, amma ban ce komai ba na ɗauka ina godiya. na sanya hijabina na ɗaura liƙab, yay min adawo lafiya, sai da zan fita a ɗakin na tuna ban fa bar masa abincin rana ba. a ɗarɗarce na juyo ina cewa,"Hubbi kaga saboda naga na makara ban samu na girka maka na rana ba amma..." ban kai ga ƙarasawa ba ya É
🏠