NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 2 of 97

______ *_Sannan ga masoyana kuma makaranta littafaina, ba ni da bakin godiya gare ku, ba zan gajiya da yi muku adu'a da godiya ba bisa goyan bayan da ku ke ba ni, Allah ya faranta muku ya yafe muku zunubanku, yasa ku gama da duniya lafiya, masu fuskantar ƙalubale a dalilin jinkirin aure ubangiji yasa hakan ya zama alkhairi babba a gareku, haka masu fuskantar ƙalubale a zamantakewar aure Allah ya gyara lamura...A wannan karon dai tafiyar ta dabance, kusa kuɗi ku siya, ba zaku yi nadamar siya da karantawa ba, a nuna min son so...har kullum ƙofa a buɗe take domin karɓar saƙonninku._* _______________________________ *_All rights reserved. No part of this book may be reproduced or transmitted in any form without seeking permission from the writter. This novel is a work of fiction, Names, characters, business, places, events, and incidents, are either the products of the author's imagination or used in a fictitious manner. Any resemblance to actual persons, living or dead, or actual events is purely coincidental. A person who commits an act of piracy, is liable on conviction to life imprisonment and a fine of not more than N50,000,000...So becareful of copying any part of this story._* *©️Copyright2023 Halimahz.* _________________________________ *SHIMFIƊA.* _A wasu lokutan da bamu tsammaci rikicewar al'amura ba, sai ya zamana al'amuran sun runcaɓe mana babu zato babu tsammani. rayuwa kan canja tayi juyayi da mutum, wasu ta juya da su duniyar rikicewa, firgicewa da tashin hankali har mutum kanji tamkar shi kaɗai aka tsana, yayin da a gefen wasu juyin rayuwa kansa su mance da baƙin ciki, haushi, da damuwa, su dulmiya a jin daɗin rayuwa. babu abin da bai da farko, babu abin da bai da asali, haka babu abin da bai da tushe, kazalika babu abin da bai da ƙarshe, sai dai yarda da Allah kan tafiyar da komai cikin daidaito._ _kamar dai yanda darasi ya ke a matsayin koyarwa da miƙa saƙo, hakan yasa a yau zan rubuta labarin rayuwarmu, sunana Sa'ida Salman, kuma wannan shi ne labarin *ƘAYAR RUWA*..._ ________________________________ *(1)* Kwance na ke akan makeken italian royal bed a cikin tamfatsetsen ɗakin barcina. Wayata ƙirar S22 na gefena ina sauraren karatun alqur'ani mai girma cikin ƙira'ar Muhmood Hosary, idanuwana a lumshe suke tamkar mai bacci, sanyin acn da ke busawa na bin dukkan ƙofofin gashin jikina, yayin da gefe guda hancina yake shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren wutar da na kunna a burner wanda ba ya ko ƙaurin kamawa saboda irin salon yanda nake bi wajen sanya shi. Sanye na ke cikin doguwar rigar material mara nauyi, rigar na ɗaya daga cikin sutturun da nake so sosai a kayana duk da material ɗin ba wai mai tsada ba ne, fuskata fayau babu kwalliya ko ɗiso, sai hakan ya ƙara fito da ramar fuskata. Gaba ɗaya yau jina nake yi kamar mara lafiya kuma kaman an yi min mutuwa, sai dai babu ko ɗaya a ciki, tun safe da na tashi bakina babu ɗanɗanon komai ga tsananin faɗuwar gaba na damuna, hakan yasa tun lokacin nake ta adu'oi da tasbihi, kuma karatun ƙur'anin da na kunna ina saurare ina bi shi yake d'ebe min kewa, to amma dai duk da hakan ina ji a jikina cewar akwai wani babban al'amari da zai girgiza duniyata nan kusa, ina jin kamar nan kusan zata zamar min ƙarshen komai na rayuwata ne. Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi, na juya kwanciyar da nayi inda a yanzu na ke fuskantar bakin ƙofar shigowa, cikin zuciyata ina roƙon ubangiji da yasa komai zai faru ya zama alkhairi, ya kuma ba ni ikon cinye kowacce kalar jarabawa da iya ɗaukan ƙaddara. zoben azurfar da ke hannuna na ke ta kallo ina jin wani abu mai girman gaske na tsarga min, yayin da tunanin wasu shekaru yasa fuskata ƙwacewa da murmushi mai faɗi, murmushin da za'a kira shi da na yaƙe. Wayata na ɗauka don duba lokaci, ƙarfe biyar da mintina na yamma ya nuna min, zaune na miƙe da mamakin gudun lokacin a cikin raina na furta "har biyar?, Lallai duniya na gudu, Allah kasa mu cika da imani". Da azama na zuro ƙafafuna ƙasa ina gyara ɗaurin ɗan kwalina, ji nake kamar zan faɗi saboda rashin ƙwarin jiki, kaman wadda ta sha zawo ya zabgar da ita a yini ɗaya. Tsayuwa nayi gaban tafkeken madubin ɗakin na tsaya ina ɗaukar tissue in shiga goge kwantsar ciki saboda ciwon idon da nake fama da shi daga shekaran jiya zuwa yau. Kallon kaina na tsaya yi a cikin madubin, lallai in har akwai rayuwa da shekaru to tabbas akwai sauyi, gaba ɗayana kamar ba ni ba, kallo ɗaya da zaka min ba sai ka ƙara na biyu ba zaka ga zallar ƙuruciyar da ke kan fuskata, wanda zai bayyana maka cewar shekaruna ba su da yawa. Sai dai kuma in har kayi min farin sani a baya, to a yanzu zaka ce na sauya, ba wai sauyi na ɗabi'a da halayya ba, a'a sauyi na halittar jiki. A baya ni ɗin Æ´ar duma duma ce mai kyawun dirin jiki tubarakallah, ina da irin jikin nan da babu kalar damuwa balle yunwa, saÉ
🏠