NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 19 of 97

mako na ke yi duk da su lafiya ƙalau su ke suna haihuwa abin su...ko Malam dai kina ganin yacca yake rubuce su da ayoyin qur'ani, ya kamata gaskiya dai a duba miki rashin haihuwa ai bala'i ne, ga shi ni Allah ya sani ina ta so inga ƴaƴan Nazifi wallahi, Allah yaji ya gani bana so na mutu banga jikokina daga gare shi ba". nasa hannu na goge hawayen da ya sakko min ba tare da na bari ta lura ba. ban iya cewa komai ba, haka ta rakomu har waje tana ta ƴan maganganu. kan hanyarmu ta komawa gida babu yacca banyi ba ya faɗa min sakamakon gwajin da aka yi min amma kamar ba muminin da na ke ta haɗawa da ubangijinsa ba, ƙememe ma yaƙi min magana. Muna zuwa gida kowa ya wuce ɗakinsa, ni dai ko da na shiga kan gado kawai na faɗa ko hijabin ma na kasa cirewa, kukan zuci na ke yi domin kuwa ruwan hawaye yaƙi sakko min. Ina cikin duniyar tunani wayata tayi ringing, na ɗaga ganin shi ne yake kirana. a taƙaice ya ce da ni,"ki zo ina nemanki". Da damuwa fal a muryana na ce,"me zan maka Hubbi?". "Me za ki min! Kina tambayan mijinki haka!, lafiyarki?". Shiru nayi na ƙi cemasa komai. kiran wayar sai tafiya yake yi, can yay nisa ya ce,"ai kin ji abin da na ce ko?, to ki taso yanzu kar ki ragen lokacin bacci, in kin zo kya ga me za ki min". da faɗar hakan ya kashe wayarsa, tashi nayi na shiga banɗaki na wanko fuskata, ban cire kayan jikina ba haka na fita don karma na sanya kayan bacci ya tsammaci ko ina jiran kaɗan ne. Ina shiga na iske har yay kwanciyarsa ma, na zauna gefen gadon ina kallonsa ta cikin ɗan hasken duhun ɗakin, a hankali nace masa,"gani, ko kayi bacci?". zaune ya miƙe ya fuskance ni sosai, ya sauke numfashi sannan ya kira sunana. sai da na ɗora idona a saman fuskarsa tukunna na amsa saboda yacca naji yanayin sautin muryar tamkar ba nasa ba. "Ina da bukatar haihuwa Sa'ida, so na ke na ganni ɗa". nayi wani guntun murmushi mai ciwo, hannuna bisa kafaɗarsa, cikin tausashshiyar murya na kwantarwa da mutum hankali da sanya natsuwa na ce,"to Hubbi mu ci gaba da faɗawa Allah, shi zai bamu ba wani ba, haihuwa a wurinsa kaɗai take ba ga wani mutum ba, damuwarmu ba ita zata sa mu samu ba, ƙosawarmu ba zata bamu ba, haƙuri da jiran lokaci Hubbi". "kina nufin ke ba za ki iya haihuwar ba kenan?...". Na katse cewarsa da,"Subhanallah, baka ji abin da nace ba ne kake ambaton ni ba zan iya bawa kaina ba. Haba Hubbi kar son wani abu yasa ka yi saɓo, ai ba zancen ba zan iya ba, idan Allah ya kawo mai zai hana kuwa in haifa maka ƴaƴa, in bai kawo ba ina da ikon bawa kaina ne?, haƙurin nan dai da muka saba shi zamu ci gaba da yi, komai lokaci ne, watarana sai ƙalubalen jinkirin kaga ya zama alkhairi mafi girma". aikuwa furucin nawa ya fusata shi, nan ya hau banbami yana faɗin,"fina sanin daidai kika yi da za ki dinga tsara min kalamai, sai anyi magana ki nuna kin fi kowa sanin Allah. to ni dai na faɗa miki ina son haihuwa, so na ke na ganni da ƴaƴa, idan ba za ki haifa min ba kuma ki sanar da ni. kullum burina ne inji an kira ni da Baban wane, na dawo gida inga ɗana ya tarbe ni, to kar ki sa nima na fara zargin wani abun kika sha saboda kar ki haihu, in ba ki haifa yanzu da ƙuruciyarki ba sai kin tsufa kenan?, wannan ai ni kikawa mugunta ba kanki ba, shekara nawa haba". Na ɗago a gigice ina kallonsa, cikin sarƙewar murya na shiga ce masa,"haba Hubbi! haba!, ta ya kaima zaka shiga sahun masu tuhumata akan rashin haihuwa, kar ka fita daga imaninka mana, kar ka zama me shiga hurumin ubangiji, Hubbi akan me zan maka mugunta in sha wani magani saboda dai kar na ɗauki ciki?, cikinka fa Hubbi, shin ka manta irin tsananin son da na ke maka ne". Na tsagaita yayin da na ke goge hawayena, zuwa lokacin kuma kuka yaci ƙarfina, kallonsa na ke yi ta ruwan hawayen da ya taru a idona. "bayan iyayena kafi kowa sanin wace ni, kai zaka bayar da shaidar yanda na ke son yara, tun farkon aurenmu ka san da cewa ina bala'in son ace na haihu, na san kaima yanda ka ke son ƴaƴa tun kafin aurenmu, Hubbi in ace da yanda zan yi in sanya cikin da zan haife maka a cikina wallahi tallahi da duk in da ake samo ciki sai na samo na saka, to amma ya zan yi, lokacina ne bai yi ba...". nayi shiru ina ɗago ido na kalle shi, ba ni ya ke kallo ba, idonsa na manne a ƙasan tiles, hannunsa dunƙule a gefen bakinsa, yanayinsa na nuni da cewar hankalinsa sam bama akaina ya ke ba, ya nutsa ne can cikin tunanin wani abun. na daɗa matsowa kusa da shi, kaina na kwantar a kafaɗarsa, hawayen idona ya sauka ta gefe ya tsarga ta cikin rigarsa, na danne kukana, muryana ya washe wajen ce masa,"na san ɗazu da muka je asibiti gwajin haihuwa aka yi min, sun kuma bamu sakamakon gwajin nan, Hubbi don me yasa ba zaka faɗa min ba domin in san menene matsalatar, idan ta neman magani ce sai mu nema kaman yanda Iyam ta ce, idan ma wata mafitar za'a nema sai a nema, ba zan taɓa ɗaga hankalina ba
🏠