NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 97

bata da uba. damuwar da na ke ciki sam ba zata barni ɗauko waya in daddana ba don ɗebe min kewa, ga tarin tambayoyi sun cika ƙwaƙwalwata, ko canjin Hubbi bai girgiza ni ba kamar canjawar Iyam a gare ni. kusan tsawon minti biyar Ummaa ta fito daga ɗakinta, ganina zaune ta saki baki tana kallona da mamaki. "Sa'ida zuwan yaushe?". Ina murmusawa na ce,"zuwanmu babu daɗewa kenan Ummaa, Ina yini". "Lafiya lau, to kuma kika zauna ke ɗaya anan kamar wata baƙuwa, ruwan da aka yi da magribar nan ne yasa duk muka wuce ɗaki da wuri, ke ɗaya ce ne?". Nace,"aa tare da shi muke". "to ƙalau dai ko?". Na amsa da,"ƙalau Ummaa, mun fita ne dama sai muka biyo ta nan ɗin mu gaishe ku". "Allah sarki, Nazifin bai shigo ba ne?". "A'a yana ɗakin Iyam, yanzu na fito a ɗakin nima ina jiransa ne zamu tafi". "bari na leƙa ai ban san kun zo ba, ina nemansa dama". Ta faɗi hakan tana min wani kallon hadarin kaji. ɗakin Iyam ta wuce ta barni da bin bayanta da kallo, miƙewa nayi na nufi ɗakin Gwaggoje, tana kwance bacci har ya fara ɗibarta jin maganata yasa tayi saurin tashi tana min sannu da zuwa. na zauna muna ta hirarmu da ita, har tana tsokanata wai bamu iya zuwa ba sai dare kamar wasu korarru, ko da ike wataƙila tuwon gidan muka biyo, ni dai dariya kawai na ke yi. sai kuma ta hau min hirar zuwa ƙauyen da zata yi ƙarshen wannan watan, tana cewa ƙila ma tare zamu je tun da su Asama'u suma duk za su je, mijin Aina'u ne dai boɗararre ya hanata. shirin siyasar kano da aka fara yasa ta maida hankalinta ga radiyon, aifa nan ta fara tsinewa shuwaganni, idan na ce ta daina sai ta ƙara tunzura tana akan me ba zata tsine musu ba duk sun sanya talakawa cikin wani hali, yanda ta haƙiƙance yasa nayi shiru ina dariya ƙasa ƙasa. Sallamar su Iyam ce ta katse maganar da muke yi muka ɗago idanuwanmu kansu. Iyam ta shigo tana cewa da mahaifiyar tata,"ai kamar na sani nace bara in leƙo ba lallai kin saki net ba". Gwaggoje ta ɓata fuska bata ce da ita komai ba, Iyam kuma ta shiga sauke mata net ɗin. Hubbi ya zauna suna gaisawa, har yana tambayarta ita babu wata matsala a ɗakin nata, ta ce da shi babu matsalar komai, ta faɗa tana saka masa albarka. Wajen ƙarfe goma muka yi haramar tafiya, lokacin ne kuma Iyam ke cewa da Hubbi. "Ka kuwa ji haihuwar matar Nasiru?". "Ahh matar Nasiru ta ƙara haihuwa, lallai ne amma kuwa kinga bai kira ni ba wallahi, Allah ya raya". Ta ce,"wallahi dai kaga su matansu sai haihuwa suke yi, ga su nan kowanne da yara uku biyu, kai ne dai shiru har yanzu, ban san menene matsalar ba, kai ɗin dai lafiyayye ne na san ɗan da na haifa, amma ya kamata ita ka kaita asibiti a dubata, ai ba a zauna shiru haka ba ayita zuba ido wa tsammanin da ba tabbas". a hankali yace,"haka ne zamu je ɗin in sha Allah". Da sauri ta cafe,"Shalele ba fa batun wani in sha Allah ba, da zafifi ake bugun ice, in ba'a san abin yi ba yanzu shin sai yaushe?, rayuwar nan fa tafiya take tayi, girma ne ya ke daɗa kamaka, kana so ka mutu ne baka bar ɗan da zai ke maka adu'a ba, haba ai ka samu ganin jininka ma a duniya rahma ne". Sai kuma ta juyo gare ni tana cewa,"kuma ke Sa'ida ba ki sha wani abu ba da zai hanaki ɗaukar ciki ba?". Kaina a ƙasa nace,"ban sha komai ba Iyam, amma ai mun je...". Hubbi yay saurin tarar maganata da cewa,"Iyam bari mu wuce na bar baƙo zai zo ga kiransa naga yana shigowa". Wani kallo tayi masa da cewa,"tana magana kuma ka katseta, ko wani abun ne baka so na sani?". kansa ƙasa yace,"a'a fa ita ai tana maganar mun je wajen wani me magani ɗazu to bamu sami ganinsa ba, dama ina so sai mun gansa ɗin sai kiji komai". "To ai shikenan Allah ya kyauta, sai ku daure ku ƙara zuwa amma kuje da wuri tun da irin su jama'a yawa suke musu. Gwara idan haihuwar ce bata yi muji da wuri ai ba'a ta zama haka ba, sa'anninka dai duk gasu nan da ƴaƴansu, kuma in jin daɗin rayuwar nan ne dai ai ka fisu, dukiya gata nan bata wasa ba, kaima in kana ganin yaronka ai sai kafi farin ciki da kwanciyar hankali, ga shi nan yanzu naga duk ka rame, kuma na san ba zai wuci damuwar rashin haihuwar kasawa ranka ba". ta fuskanto ni ta ce,"ko cikin danginku akwai masu matsalar haihuwa ne Sa'ida irin wanda basu taɓa haihuwa ba haka?, kin san akan yi gado, kuma auren irin waɗannan cuturwa ce ga namiji ba kaɗan ba tun da an yaudare shi ba'a faɗa masa ba, amma dai ko me ke nan ki samu ki faɗawa iyayen naki a nema miki magani ba'a ta zama haka ba, kinga shi mijin naki hidindimu sun masa yawa ba ya ta fama da na magani ba tun da babu tabbas ɗin ma za'a sami abin da ake so, dole dai iyayen na ki sai sun miƙe tsaye sun taimaka miki, abubuwa sun masa yawa shi kam, ga hidimarmu ga taki ta yau da kullum...kuyi magana da Ummar taki, nima ƴaƴan gabana yawa gare su da sai inji da ke, to ba zaune na ke ba kullum cikin nemar musu tai
🏠