i ba fa, ku fara biyawa ta wurinsa, Éazu ma da Æyar ya iya zuwa asibiti duba yaron da ka bige...yauwa Nazifi kaga anata mantawa, AC Éin falon nan da fankar Éakin Gwaggoje sun lalace, ita ma Ummaa naji tana akwai gyara a Éakinta".
Ya ce,"tom shikenan za'a gyara da wuri in sha Allahu".
"Madallah Allah yay muku albarka, ya Æara maka buÉi da wadata ko don taimakawa ahalinka da ka ke yi".
Sashin Malam mu ka wuce, ina saka Æafata a falon sai kuwa Æ´an yaran su ka taso kowannensu da murnar yana faÉin,"oyoyo ga Anti Ca'ida".
Su ka cukwikwiye ni sai farin ciki su ke da ganin nawa, Lubabatu ce me cewa da su,"ba za ku Æyaleta ba sai kun yar da ita".
"Ni dai ce matar Yaya kayami ta bani biccit zan caketa".
cewar Sahura Æ´ar gidan Anti Aisha, cikin muryar gwarancinta me abin dariya.
Abasiyya ta ce,"ai ko to duk wanda bai rabu da ita ba ba za'a ba shi abin da aka siyo ba, tun da duk ba ku iya gaisuwa ba".
da saurinsu su ka sakeni kowacce na gaishe da ni cikin maganarsu ta Æ´an koyo, da yake cikinsu duk babu wacce ta haura shekara biyar, Mansur ne ma da ya Æara wayo kwanan nan maganarsa ke fita sosai.
Shigowar Hubbi falon kuma duk sai suka yi kansa, dama shi gwanin son yara haka ya tarbesu da fara'a yana ba su hannu su tafa. Malam ya fito daga cikin Éakinsa muka gaishe shi tare da yi masa sannu da jiki, yaji daÉin zuwan namu kuwa sosai, nan aka Éora hirar da ake yi da mu, Amarya ta kawo mana abinci, ni dai na ce ta haÉe mana da su Lubabatu mu ci tare, dama shi Hubbi bai tsaya wata wata ba ana kawo masa ya tankwashe Æafafu ya shiga ciki, da ike ma'abocin tuwan masara miyar kuÉewa busashshiya ne. Bayan mun gama cin abinci mu ka miÆe don wucewa, kamar kullum in muka zo Malam yay mana nasihohin da ya saba, da Æara bamu tarin adu'oin da ya kamata mu riÆe a ko da yaushe musamman na tsari. mu ka yi godiya da adu'ar Allah ya Æara lafiya sannan mu ka fito zuwa wajen Iyam.
Can na baro Hubbi ya shiga Éakin Yayan Shago. Shigata falon Iyam babu kowa, don haka na nufi hanyar Éakin barcinta tun da banda shamaki da duk mallakinta, a hankali na murÉa hannun Æofar na sanya Æafafuna ciki bakina Éauke da sallama. tana daga kishingiÉe akan Æaton gadonta ta na kallon wani film a tashar gaskiyaplus, da ike ita Æ´ar gatan Éanta ce tv biyu gareta falo da ta Éaki. tun daga yanayin yacca ta amsa min sallama na sha jinin jikina, wani kallo kuwa da ta watsa min sai da na kusa kifewa a Æasa, anan fa na Æara tsinkewa da lamuran da suke ta faruwa.
cikin mugun tsoro da shakkar yanayin fuskarta na Æaraso ciki na durÆusa ina gaida ita, ba yabo babu fallasa ta amsa min gaisuwar tana miÆewa zaune yayin da ta ke gyara Éaurin Éan kwalinta.
"Ke ce da daddare haka?".
Da mamakin furucin nata na Éago ido na kalleta, to sau nawa muna zuwa a lokacin da ya wuce haka ma, sai yau ne zai zama laifi?, sai kawai na sadda kaina Æasa ina jan yatsu na ce,"tare da shi muke ya tsaya Éakin su Adamu ne. mun sameku lafiya?".
"Lafiya lau". ta amsa a daÆile ta na jifana da wani irin wulaÆantaccen kallo.
Ledar da na shigo da ita na miÆa gabanta na ce,"ga wannan muka zo miki da shi".
"Nazifin ne ya siya ko, na gode masa kuwa Allah ya Æara buÉa masa, yaron ariziÆi irin albarka, haihuwa me gidan rana".
ta Éauka tana buÉawa don duba me ke ciki.
Ni dai nayi shiru raina ina ta jin babu daÉi da yanayin yan da yau ta sauya min, ta fito da duk abin da ke cikin ledar waje tana ta sakawa wanda ya siyo albarka, yacca take faÉa da biyu don kusan magana ce take faÉa min, sai na ji duk na Æagu ya shigo su gaisa mu tafi.
"To wannan tufar dai ita zan fara ci, wannan yogot Éin kuma ba in sanya shi firiji zuwa safiya yay sanyi sai yafi daÉin sha".
Sakkowa tayi a gadon nayi saurin yunÆurawa ina cewa,"haba Iyam ina Éakin sai kin je da kan ki, kawo na saka miki".
Saurin janye ledar tayi tana yarfa min wani kallo, tana min harar Æasan ido ta ce,"matsa ban wuri".
Matsawa nayi ta wuce ta je ta saka abunta a firij, lokacin Hubbi su ka shigo shi da Adamu da Yayan Shago. ganinsa da tayi tamkar an tsundumata a aljannah, bakinta yaÆi rufuwa nan da nan ta shiga gyara masa wajen zama duk da cewa wurin a kimtse ya ke.
gaisawa su ka shiga yi tana masa tambayoyi dangane da lafiyarsa da aikinsa, can ta waigo tana kallona ta ce,"Éan je ki daga can babban falo mana, ai ba kya samu a gaba da kallo ba kamar wasu tv, hirar uwa da Æ´aÆ´anta ai akwai sirri".
Furucin nata ya taÉa ni, na miÆe jiki a saÉule na fita idona duk ya cika da ruwan hawaye, yaran dai har yanzu suna wajen Malam don ina jiyo Æ´ar hayaniyarsu, Æ´an matan kuma suna Éakunansu sai dai ba na je ba su tsammaci faruwar wani abun, idan na zo na saba a Éakin Iyam na ke yini, duk mai son hira da ni sai dai ya sameni acan. ni kaÉai na zauna nayi jugum kamar wata marainiya wacce bata da uwa