NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 16 of 97

iyata na ƙissima min wasu abubuwan, emergency ward muka je, ashe da gaske ne yaron ya bige, ai da ya faɗa min ce na ke ya faɗi hakan ne kawai don ya kare kansa. Kuma Allah sarki yaron ƙarami ne ya sha jiki don har karaya ya samu a ƙafa, sai dai jinin ma da Hubbi ke cewa zai bayar an samu wani ƙanin Baban yaron zai bayar. Mun ɗan jima kafin mu yi musu sallama, suna ta godiya kuwa kamar yawun bakinsu zai ƙare, ni ban sani ba ma ashe kusan kowa ya zo a ƴan gidan su Hubbi, uwar yaron har da hawayenta wajen yi min godiya wai mijina mutumin arziƙi ne. A can asibitin da muka je aka min test muna zuwa ya karɓo result ɗin, ya jima a ofishin likita kafin ya fito, ni dai tun da ya fito na kalli yanayin fuskarsa naji jikina yay sanyi, na nemi sukuni na rasa, hankalina duk ya tashi, ko magana bai yi min ba yay gaba na bi bayansa. Motar ma yacca ya figeta ka ce wani bala'in yaƙi za'a yi, da haka muka baro asibitin ni dai na kasa magana kuma maganar na ke so in yi, shi kuwa kana kallonsa zaka san cewar ransa babu daɗi kwata kwata. Lokaci ɗaya idona ya cika da ruwan hawaye, ba'a faɗa min gwajin da aka yi min ba, haka kuma ba'a faɗa min sakamakon da aka samu ba, amma tuni zuciyata ta gama raya min abin da sakamakon ya bayar, shikenan tawa kuma ta ƙare, ta tabbata da gaske bana haihuwa, yanzu cikin wannan tsananin halin wa zai rarrashe ni?, madafar da na ke gani in ji daɗi yanzu bata ni ya ke ba, fatana ɗaya kar aurena ya dagule ta silar hakan. hijabina na saka na goge hawayen da ya sakko min, Allah kaɗai ya san me na ke ji a zuciyata, yanzu shikenan har in koma ga mahallicina ba zan ga jinina ba?, ba zan haifi yaron da zai kalle ni ya kira ni da mahaifiya ba?, zan mutu ban bar wanda za'a ke gani ana tunawa da ni ba in ci arziƙin adu'a ta dalilinsa, shikenan duniya ba zata kira ni da sunan uwa ba?. Ƙwarai na san an buɗe min babin ƙalubalen dangin miji na tsantsar cin mutunci da gori akan rashin haihuwa?, canjin matsayi a wurin miji?, ƙarin aure ya tabbata lahu na sani, don haka dole ne cin zarafi daga kishiya, wani sabon kuka ya zo min, na kifa kaina a saman ƙafata ina rera shi a hankali, na sani tabbas duk wani abu da zai samu bawa daga Allah ne, kuma hakan alkhairi ne a gare shi, fatana ɗaya ubangiji ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar rayuwar. Ina cikin kukan na jiyo muryarsa yana faɗin,"wai ke babu ranar da za ki girma ne?, kina wani kuka sai kace jaririya, mene hakan?, ba'a miki komai ba ki kama kuka, wannan ai shirmen banza ne". Na ɗaga ido ina kallonsa, gaba ɗaya babu wani tausayina a saman fuskarsa, balle a biyo ga batun rarrashi da ban haƙuri da nasiha, dama tuni ya saka hijabi a tsakaninmu kan waɗannan abu ukun. ba a komai ne ka ke da buƙatar ayi maka bayani ba, wani abun hankalinka da tunaninka zaka sa ka fahimta, tsawon watanni ban san matsalar da ta kawo canjin yanayin zama tsakanina da shi ba, amma daga abin da Yayarsa ta zo tayi min jiya na ɗora samun saɓaninmu da shi akan hakan, don na san dai tabbas in har laifi nayi za'a faɗa min, shi mutum ne dai baya ɓoye wannan. hmmm ƙwarai na sani yanzu zan shiga wata sabuwar rayuwa ne, ba fata na ke wa kaina ba, amma na sani na gama rayuwar farin ciki a gidan aurena, domin banga alamun Hubbi zai karɓi wannan ƙaddarar tawa ba, banga alamun zai taya ni mu cinye jarabawar tare ba, lamarin zai zama tamkar ni na gaza ne. Muryata gwanin ban tausayi na ce masa,"Hubbi ba ka faɗa min abin da likitan ya ce ba". "ke kika kawo kanki?". "Ba ni na kawo kaina ba amma kuma tawa lafiyar aka duba ai, ina son sanin abin da likita ya faɗa kaji, ina son sanin abin da yake damuna". Maimakon amsar tambayana sai jan tsaki yay. a maimakon gida sai naga mun ɗauki hanyar gidansu, haka kawai kuma a karo na farko naji ina tsoron zuwa gidan, daga waje ya ajiye motar bamu shiga da ita ciki ba. Ni ya bawa ledar siyayyar da mu ka yiwa Iyam, ginin gidan irin ginin tsakiyar nan ne, babban parlo zaka fara shiga, a ciki kuma kowa da ɓangarensa ta can ciki. shigarmu falon mu ka tarar da Amarya, tana ganinmu fara'a ta wanzu a fuskarta tana tafa hannu wajen yi mana lale lale. Nayi ƙarfin halin ɓoye damuwata na aro jarumtar fara'a da walwala na yafa. na duƙa ƙasa na gaisheta daga bisani kuma su ka shiga gaisawa da Hubbi. nan yake cewa da ita,"na ji gidan tsit". Ta ce,"umm suna can falon Malam ana hira". "Iyam ma tana can?". Ya tambaya a lokacin da yake cire hularsa yana susa. "anya kuwa, kamar dai tana ɗakinta". sai kuma ta dube ni tana cewa,"kin san bamu jima da gama hirarku ba, na ke cewa ya kamata in samu lokaci in shiga in duba ku, ashe ma kuna tafe a hanya. to fatan dai duk kuna lafiya". Ina murmushin yaƙe na ce,"muna lafiya lau, ya muka same ku?". Ta ce,"lafiya lau. Tashi ku shiga ciki nima zan ɗaukowa Malam abincinsa ne". Hubbi zai wuce ta dakatar da shi da cewa,"Malam yini yay yau bai ji daɗ
🏠