tsakaninmu shi ma a nasa Éangaren haka, don har da tsokanata ya dinÆa yi.
Tashar kano line muka kai ta, ya zaro dubu bakwai ya bata tayi kuÉin mota, aikuwa ta dinÆa godiya da sa albarka tamkar yawun bakinta zai Æare, to nima Éin dai bata sani ba da tawa Æ´ar dubu ukun da na Æunshewa Jamil a wando sai taje gida zata gani, Hubbi da kansa ya sauka ya samar mata mota ta hau sannan ya dawo muka Éauki hanyar da ban da masaniyar zuwanmu. Sai dai fa tun daga sauke Hassana motar ta koma tamkar ta kurame, Æarar ac da sautin radio kawai kake ji, duk yanda na so in ja shi da hira sai gajiya nayi naja baki na tsuke, haka har muka iso Æofar wani babban asibitin kuÉi UMC Zhahir Hospital anan janbulo 3rd gate.
Zuwan namu ya bani amsar tambayata da na rasa na ina mu ka dosa, ai babu ma Æarin bayani na san me ya kawo mu, ban manta jiya ba, ban manta Yaya da cin mutuncinta ba, don haka zuwan namu asibiti a yanzu na san dalilin duk da bai fito da bakinsa ya ce min kanzil ba.
Aka zuge mana gate mu ka shiga da motar zuwa ciki, bayan kashe motar ya kaikaito da kansa ya dube ni ya ce,"yau ya Éauke ko?".
Na ce,"me?".
"Period Éin ki".
"Ummm". Na amsa masa a taÆaice.
"Ok ki jira ni ina zuwa".
Ban ce komai ba ya fita a motar, cikin asibitin na ga ya nufa, bayan mintunan da ba su haura uku ba sai ga shi ya fito hannunsa riÆe da wata takarda. tun daga nesa yay min alama na in fito daga motar, kafin ya Æaraso na fito, yana zuwa yasa maÆulli ya kulle, idonsa a kaina ya ce,"mu je".
Yana gaba ina biye a bayansa kaman yarinyarsa, ba ka ce mata da miji ba. da shigarmu Éakin gwaje gwaje naga mun nufa, a lokacin da muka tsaya bakin Æofar lab Éin gabana ya yanke ya faÉi, kaina naji yay bala'in sara min, sai naji lokaci Éaya idona na ÆoÆarin kawo ruwa, babu shiri na mayar da su. mun kusa minti biyar zaune a reception naji an kira sunana Sa'ida Salman Madobi. Jin kiran mu ka Éago kawunanmu a tare, yanda na ke kallonsa shima haka, bakina Æunshe da tambaya sai dai ban ce komai ba domin ban san ta ina zan fara ba. girarsa ya Éan sosa kana ya ce da ni,"ki je, ki kuma natsu".
Jiki a sanyaye na ce,"Hubbi har da allura?".
Na faÉa muryana kana ji ka san a tsorace na ke. kafaÉa kawai ya Éaga min alamun bai sani ba shima. Na wuce kamar marar lakka zuwa wani room da nurse ta nuna min. ni dai tun shigata ina ga mun kusa rabin awa sai aikin jagwalgwala ni ake, ai wancan ai wancan, gwaji kusan kala nawa, kalma Éaya na riÆe na dai ji ana faÉin ko HCG ko mene dai oho. bayan kammala komai na fito, Hubbi na inda na barsa, yaga fitowar tawa amma sai ya Éauke ido tamkar ba ni ya gani ba, kuma raina yay bala'in sosuwa da hakan.
Kusa da shi na sami wata ta zauna, fuska haÉe na dubeta na ce,"matarsa ta dawo wurinta".
Kallona tayi sannan ta kalle shi taga idonsa Æyam akaina, na ja tsaki ina daÉa cewa,"ko sai an taimaka miki ne kafin ki sami damar tashi?".
Yanda taji nayi maganar da yanda amon sautin ya fita ta san ko da na faÉi haka ba abu me kyau zan aika ba, domin kuwa a Æule na ke. babu shiri ta miÆe tana faÉin,"yi haÆura".
ta faÉa tana miÆewa ta wuce ta gabana, naja dogon tsaki ina cewa da ita,"shashasha marar kamun kai". ta jini sarai amma sai bata tsaya ce min komai ba ta wuce.
Tsaye na yi na Éan jingina da kujerar bayana ina harÉe hannaye a Æirji, gaba Éaya na cika nayi fam, bala'i kawai na ke so in zazzaga in sami sauÆi, hasko maganar da suka yi na ke da abin da suka tattauna. murya a ciki na ce masa,"nan zamu kwana ne?".
wani kallo ya watsa min yana cewa,"ba ki iya bayani ba ne?".
Da har zan ce masa,"ban iya ba". Sai kuma dai na ce,"wai a jira na awa Éaya".
Agogonsa ya kalla kafin ya ce,"to zauna mana kin wani tsayan aka".
Kaucewa nayi na basa wuri zan sauya kujera na ce,"bana zama wurin da yake da najasa".
Kuma kafin in zauna ya taso yana cewa,"muje mu dawo".
Bayan fitowar tamu daga asibitin wajen masu siyar da kayan marmari mu ka nufa, ina daga cikin mota ya fita, haka aka jido komai na kayan marmari sai da aka cika leda. ya buÉe bayan motar aka zuba su, sannan ya tafi wani kanti, bayan mintuna ya dawo tare da yaron shagon hannunsa riÆe da katan Éin maltina da na madarar gwangwani peak ta ruwa.
Bayan ya dawo motar ya zauna ne ya ke cewa da ni,"sai mai ya kamata akaiwa mara lafiya?".
Na ce,"ko iya wannan ma yayi, amma in da dama a siya kaza gasashshiya ko nama balangu".
"Ok". ya ce, sannan ya tayar da motar muka wuce. Kaji ya siya manya guda uku anan wajen wani cin abinci na albaik, daga nan kuma mu ka wuce asibitin Imamu Wali shi ma anan jan bulo Éin ya ke gaba da asibitin da muka je. Sai da muka isa asibitin ne tukunna ya sami damar buÉe baki yana min bayanin wai yaron da ya kaÉe jiya zamu duba. da "to". kawai na amsa shi muka Éebi kayan dubiyar da muka siya muka wuce zuwa ciki.
Ni dai bin sa kawai na ke zuc