nan kuma ni Hassy menene shi, haka fitilun falo ma wai ai ita ba zata iya kwana ba gani zata yi kamar zasu faÉo kanta taga haka ake yi a film Éin indiya...cikin hirarmu take bani labarin mutuwar mijin Firdausi itama Æ´ar group Éinmu ce a makaranta, na ke ce mata wallahi ban sani ba amma zan samu in shiga a satin nan in mata ta'aziyya. Hirar tamu kuma ta juya kan kasuwancin da uwar bari tasa mata su ka durfafa, har take neman shawarata akan sana'ar da take so ta fara na kiwon kifi, ai kuwa nan na Æarfafa mata gwiwa akan tayi Éin na kuma daÉa nuna mata muhimmancin sana'a a wajen mace. Taji daÉin shawarwarina sosai, mu ne har la'asar anata zuba ana shewa, sai lokacin ne tayi Éan jim ta kalle ni tace,"don Allah kiyi haÆuri da tambayar da zan yi miki".
Nace mata,"tambayan me Hassana?".
Ta numfasa tace,"kiyi haÆuri ba sa ido ba ne, damuwa da ke ne wallahi, ke dai kin san yanda Allah ya jarabce ni da sonki, domin ni ba matsayin Æawa kike garen ba, ganinki na ke tamkar Hussaina da na saki Nono ta kama".
Na murmusa kuncina na ce,"na sani Hassana kar ki damu faÉi abin da yake cikinki".
"Me yake damunki naga kinyi uwar rama haka?".
"Wai da gaske ramewa nayi?, Sai aita na rame ni kuwa banga ramar da nayi ba, Hubbi ma ce yay nayi Æiba".
Galla min harara tayi tana faÉin,"ban sani ba Æ´ar rainin hankali, ga fa Æashin da ke wuyanki Sa'ida abin da babu a da".
Dariyar da ta bayyanar da haÆorana na yi nace mata,"kar ki damu ba wata damuwa ba ce, jinya na sha kwana biyun nan, watana biyu a kwance".
Aikuwa ranta ya Éaci ta nuna min rashin jin daÉin hakan. ta fara mita akan me yasa ban taÉa faÉa mata ba, ta ya za'ai ace har na sha jinya irin haka bata sani ba, ko bata zo duba ni ba adu'a da sannu ai suna da daÉi. Ni dai haka nayi ta bata haÆuri, ta gama mitar sai kuma can ta doka tsalle ta rungumoni tana murmushi cikin fara'a tace,"kinga ki bani wanga albishir kawai kar ki ja min rai".
Nayi lakato ina kallonta domin na san in da zancen nata ya dosa, ta zame a jikina tana daÉa cewa,"wata nawa?".
Na waro ido na ce,"keee mene wata nawa?".
Tayi min wani kallo na kar ki raina min hankali. Na ce,"Allah kuwa, idan shi ne ai tun a waya zan sanar miki, wallahi bani da komai Hassana har yanzu shiru, sai dai a ci gaba da samu cikin adu'a".
Jikinta a sanyaye tace,"to Allah yasa jinkirin Alkhairi ne. Amma dai ai ba kya fuskantar wata matsala ko, kin san sha'ani na dangin miji".
Murmushi nayi na ce,"ko Éaya fa, ai kin fi kowa sanin surukai na. Ita Iyam ma da kanta take nema mana magani".
Tace,"Allah sarki. To Allah yasa a dace, ke kam Sa'ida ai kinyi dacen suruka wallahi, ga dangi miji kamar kece Æ´ar tasu".
Ni dai murmushi kawai nayi na kuma san yanda nayi na katse maganar haka. ta miÆe tana faÉin,"bari nayo fitsari in zo in Éauki hanya yanzu za kiga magriba tayi".
Tashinta ba daÉewa naji Maganar Hubbi akaina yana cewa,"ina jiranki".
Bayansa na bi da kallo wanda tuni ya wuce yay komawarsa Éaki, nayi godiya ga Allah da yasa Hassana bata nan, da haka zai fallasa lamarin da na ke Éoyewa. Kaina na girgiza cike da takaici da baÆin ciki na tashi, na Éauki Jamil na tafi da shi. A Éakin na same shi yana kaiwa da komowa, na tsaya daga gefe na ce,"gani".
Tsaye yayi yana Æarewa Jamil kallo, ban sani ba burge shi yaron yay kome masa ne oho, yana dai ta kallonsa kamar ma zai miÆo hannu ya karÉe shi. shirunsa yay min yawa na Éago kaina na kalle shi naga bai Éauke ido daga kallon Jamil Éin ba, muryata a hankali na ce masa,"Éan gidan Hassana ne".
Sai sannan ya Éauke idonsa akan yaron yana cewa,"wace hakan?".
Na kalle shi nayi guntun murmushi na ce,"Hassana Tijjani dai Æ´ar ajinmu".
"Ohhh, haihuwa ta Æara yi?".
"Ehhh shi ne wanda aka haifa ranar da zaka tafi Hajji ban samu zuwa barka ba".
Ya sake cewa,"ohh Allah ya raya". Na amsa da,"amin". jimm na Æ´an sakanni kuma sai ya sake cewa,"ashe Yaya ta zo jiya".
Furucin nasa yasa gabana ya faÉi ras, duk sai na nemi na daburce da yay maganar wacca ta fama ciwon jiya na cin mutunci da Yaya ta yi min. Idona na rumtse gam nace,"ehh na manta ne ma ban faÉa maka ba".
Cikin fusata ya ce,"wai ke mene matsalarki ne, iskanci ko kuma rashin mutunci?, Yayan ta zo jiya, jiyan ma da daddare amma saboda rainin wayo za ki buÉi baki kice kin manta da zuwanta. dama har haka kika fara raina min Æ´an uwa?, Ashe maganar da na ke ji na cewan kina wulaÆanta su gaskiya ne ba Æarya ba, to bari kiji na faÉa miki, zan iya Éaukan komai amma ban da cin zarafin Æ´an uwana, ba zan Éauki hakan ba Sa'ida ke kin san waye ni, akan Æ´an uwana ina iya rabuwa da kowa ko da ace Éan cikina ne...".
Furucinsa na Æarshe yasa na kalle shi babu shiri, Éoye raunina nayi na tari numfashinsa ina basa haÆuri, saboda yacca yake Éaga murya tsab Hassana da ke falo zata iya juyo komai.
Daka min tsawa yay wacca