ya gagara ya sanar da ni, sai kuma kawai na bagarar nace,"Allah ya Æara sauÆi".
Yace,"amin, ya zubar da jini da yawa yau zanje a Éibi nawa a saka masa".
Kallonsa nayi ta Æasan ido nace,"Allah ya taimaka".
Ina faÉar hakan na bar masa Éakinsa na fita. Samu nayi ana ÆwanÆwasa Æofan falo, na Æarasa na buÉe, ganin wadda ke tsaye a gabana nace,"Hassana Tijjani".
Na faÉi sunan nata da muryar bayyana murna da jin daÉin ganinta. hanya na bata ta Æaraso ciki tana ta nishi alamun ta gaji da yawa, jakar hannunta ta wancakalar kan kujera tare da kwance goyon bayanta, sannan tace da ni,"me gidan yana nan?"
Nace,"Yana ciki". sai ta fasa cire mayafinta tana sake cewa,"ke Æaro gudun Acn nan, jina nake kamar a garwashi".
Na wuce wajen makunnin AC na Æaro ina cewa da ita,"daga ina kike haka ne?, Naga sai zufa kike haÉawa...bari na kawo miki ruwa".
Kitchen na wuce ina jiyota tana faÉin,"ke dai bari tafiyayya nayi tun daga Shanono, naje gidan wan Mamarmu gaisuwar Éansa, muna shigowa kano kuma muka wuce gidan Æanwata Saratu anyi mata tiyata an ciro yaro babu rai, nace dai to yau tun da Allah yasa nayi kusa da unguwar su Sa'ida in sha Allahu sai na zo mun gaisa".
Ina ta murmushi na ajiye babban farantin hannuna da na sako ruwan sanyi da lemun Éawo da ayaba,"sannu da hanya, to ya aka yi kika gane gidan?".
Tana goge zufa tace,"na kira wayanki ban samu ba sai kawai na kira Ummani ta min kwatance".
Nace,"kar ki ce min sai da kika je gidanmu".
"Wallahi sai da naje, ai ba zan iya zuwa kano dai in yawace yawace ban je na gaida Ummani ba, tace ma in gaida ke".
Na kuwa ji daÉi matuka da cewarta, fuskata ta washe da annuri ina cewa,"Maimuna ina godiya da yanda kike girmama mahaifiyata, Allah ya bar zumunci". Ta amsa da amin, ni kuma na Æara cewa,"ya Æarin haÆuri?".
"haÆuri mun gode Allah, kwanakin nan anata rasuwa wallahi, rasuwar ma ta matasa".
Nima cikin jajantawa nace,"wallahi kuwa sai fatan Allah yasa muyi kyakykyawan Æarshe. Dama Saratu lokacin haihuwarta yayi?".
"Ina fa bakwaini ne, to Éan ma sai yazo babu rai".
Nace,"Allah sarki Allah ya bada rayayya".
Naje na Éauki yaronta da ke bacci na kwantar da shi kan wata Æaramar katifa da na Éauko gudun kar yay fitsari akan kujerar. Ni dai har raina naji daÉin ganinta, rabona da ita tun kafin mu dawo gidan nan, Æ´ar ajinmu ce tare muka yi sakandire, tana cikin abokan arziÆin da aka yi zaman mutunci da su, Æ´an gidanmu kaf babu wanda bai san Hassana Tijjani ba, kafin muyi aure yawan lokuta ta kan zo gidanmu, bini bini ta kira Ummani su gaisa, saboda tana sonta sosai, ko ina ta shiga ta yabi mahaifiyata taita bada labarin mutuncinta. duk da ni ina Éan shashshareta saboda ban cika son Æawaye ba, amma hakan bai sa ta ja baya da ni ba, ko da bikina tun daga Zariya ta zo sai da ta kwana uku, haka da su ka dawo zama kano ta jajje gidana ba zai Æirgu ba, amma ni kuwa tsabar kirkina zuwana gidanta bai fi sau uku ba.
"Sa'ida ban fa yi sallah ba. In fara yi kafin mu zauna wannan hirar tamu ta yaushe gamo". Ta ce bayan ta ajiye jarkar ruwan da tun da ta kafa kai bata sauke ba sai da ta kusa shanyewa.
Na kalleta murmushin fuskata bai Éauke ba na ce,"to ko sama zamu hau, kyama yi wanka kiji daÉin jikinki".
Tana dariya tace,"wanka Sa'ida kamar wacca ta zo kwana, raba ni, na dai yi sallar kawai. Sallar ce in baka yita ba babu natsuwa kwata kwata".
Tashi nayi na Éauki yaron nata da na ke ta jin kunyar in tambayeta sunansa, lokacin da ta haihu har hotonsa ta turo min da sunansa, haihuwanta biyu duk babu wacca naje mata barka, amma hakan baisa ko kaÉan Hassana ta nuna min rashin jin daÉinta ba ko Æorafi, ita ce ma mai yawan nemana a waya taji ya nake.
Ina nufar sama ta ce da ni,"Sa'ida ku fa gidan nan na ku na Æ´an gayu ba a rasa ku da banÉakuna a Æasa, saboda haka ki taimaka ki rabani da hawa dogon benen da idanuwana ke gani, ba za ki gane yanda Æafafuna su ke a gajiye ba".
Gajeriyar dariya nayi na maida yaron na kwantar, bedroom Éina na Æasa na rakata, sai da na takurata akan tayi wanka. Na fito na barta a ciki na wuce kitchen na haÉo mata kayan abinci, lokacin yaronta ya tashi na Éauke shi ina ta masa wasa, yaron tubarkallah Éan kuÉulÉul da shi ga shi tsab tsab, babu ko irin Æarnin tumbuÉi a jikinsa sai Æamshi yake yi, daÉina da Hassana kenan tsabta gaba ta bata ba baya ba.
Dawowarta tana murmushin jin daÉin da ya kasa Éoyuwa a fuskarta take cewa,"au Jamil tashi ya yi?".
Aiko nan naji daÉin faÉar sunan da tayi, ina murmushin nima nace,"ai yanzu na ke cewa Jamil har haka yayi wayo sai dariya yake yi abinsa, ga shi babu ruwansa da rigima".
Haka ta zauna ta shiga cin abinci, tana ci muna ta hira abinmu, sai zuba santin gidana take yi, faÉi take wannan ai shi ake kira da aljannar duniya, dama gata Æ´ar barkwanci duk in da na zagaya da ita sai tace wan