NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 99 of 223

awo garesu su na raye ba bayan ta Allah ta kasance ba...kin san me?". tace,"a'a ina dai jinka". ta faɗa tana goge hawayen da ke sakko mata. "Hussainarki tana da kirki sosai, naje ma ta a matsayin ɗalibi me neman taimako har ta saka min hannu a takardar da na kai ma ta, kuma tun shigata office ɗinta har fitowata tana kirana ne da Ɗan'uwana. tace min tayi min taimakon dan Allah ne, amma tana buƙatar adu'a daga gareni akan Allah ya bayyana ƴar'uwarta da ta ɓata, na kuma yi ma ta alƙawarin hakan, ita ma kuma ina miki albishir ɗin tana nan cikin ƙoshin lafiya sai dai kallo ɗaya zaka yiwa fuskarta kasan tana ɗauke da wata damuwa a ƙasan ranta, bakinta kuma yana faɗin idan har ta mutu baku gana ba, ba zata yafewa kanta ba". tana tsayar da kukanta tace,"Kabir ta yi aure ne?". "a'a ba tayi ba, kuma a dalilin hakan tana ta fuskantar ƙalubale daga wurin mutane...ita kuma ta yiwa kanta alƙawaarin ba zata yi aure ba sai san da kika dawo". sai kuma ya ƙyalƙyale da dariyar da ke nuna yana cikin nishaɗi, tace da shi,"ni ina hawaye kai kana dariya, mene abin dariyar a cikin wannan yanayin Kabir?". "kiyi haƙuri, da aka ce ne ana cigiyarki within ƙasashen larabawan nan shi ne abin ya ban dariya, nace to dama taya za'ai a ganki alhalin kina ƙasar bichi ƙunshe a wannan gidan ƙasar tamu ba um ba umum sai kallo da ido". ita kanta bata san lokacin da dariya ta suɓuce ma ta ba, daga haka kuma tai masa godiya sosai sannan suka yi sallama da cewar idan Yagana ta tafi zata ƙara kiransa. sauke wayarta daga kunne ta jingina da ƙyauren banɗakin, tana son komawa cikin ahalinta, amma kuma tana tsoro saboda Hassanarta, Hassana zata rusa ma ta duk wani shiri da suka yi idan ta koma, allura ce zata tono garma idan ta koma, saboda Hassana Adamant(kaifi ɗaya) ce, idan ta kafe a abu babu wani mahaluƙi da yake sauya ra'ayinta ko da iyayenta ne, ta inda suka sami banbanci a hali kenan, shi yasa idan Mairo ta kafe a abu takan kalleta tayi murmushi aranta tace Babarki kika yo. *CardioCare Specialty Hospital, Abuja, Nigeria, A wannan ranar.* "to kinji dukkan abin da ya faru da ke tun daga ranar da kika ɓata".  Amadu ya kai ƙarshen zancen da wannan maganar, tun harbin bindigar nan da suka jiyo ta cikin gida, wanda Mom tai silarsa akan fusata Dad da tayi na korar Mairo, tsananin ɓacin ransa da zuciya ke sa shi aiwatar da komai acikin fushi ya ɗauki bindiga zai harbeta, Granny tai saurin ɗaga hannunsa sama ya harbi saman, amma da babu abunda zai hana shi alburushe Mom. kuma Joseph ya fito a rikice yana sanarwa da su Obi Mom tace in har Mairo bata bar gidan ba, to ko Dad bai koreta ba ta rantse da jesus sai ta kashe kanta. dalilin da ya sa suka rikice kenan Obi ya roƙi Amadu akan ya ɗau Mairo su bar gidan da hanzari, dan Mom tana faɗar abin da zata aiwatar ne ba abin da ke tsayawa a iyakar fatar bakinta ba, gwara Dad idan ya fusata ne yake aikata koma menene, amma da zarar Granny ta shiga lamarin shikenan. Obi da duk ya rikice yace da Amadu,"Friend ka ɗauketa ku tafi ko ba dan komai ba sai dan lafiyarta, kaga yanzu ta dawo cikin tunaninta, wannan rikicin zai iya haifar ma ta da wata matsalar, ko ta koma gidan jiya ko kuma wani abu makamancin hakan ya faru". ita Mairo a lokacinma duk a ruɗe ta ke, kuka take kawai tana kiran sunan Gwaggo da Baba da Ya Kabiru, dan tun san da ta ɗago kai taga ƙaton compound ɗin fayau sai shuken fulawowi ta ko'ina ta daɗa hargitsewa, tunaninta har yanzu bata bar wannan ƙaton jejin da suke ciki ba, ko da taga Amadu sunkuye a gabanta sai ta fashe da sabon kuka ta rungume shi, sai kuma ta fara complain ɗin ciwon da kanta keyi ma ta kamar zai rabe gida biyu. dalilin da yasa suka zarto da ita asibiti kenan, likitan da ya dubata ya tabbatar musu da cewar,"ehh ta dawo cikin ainihin tunaninta, amma duk da haka ba wai zata manta duka abubuwan da suka faru da ita a san da take cikin ciwon bane, a'a wasu abubuwan su na nan zaune akanta, kamar yaren da bakinta ya kama, karatu da kuma giftawar wasu tsirarrun al'amuran da ta sakasu a ranta sosai". abu ɗaya ya saka Amadu jin daɗi shi ne karatun da tayi, yana adu'ar Allah yasa karta manta da shi. tun a lokacin da aka cire ma ta drip, lokacin da ke nuna ta gama dawowa gaba ɗaya cikin tunaninta, tambayar da ta farayi masa itace,"Ya Amadu ya akai ka tsinto ni?, hanyar dajin fa da aka kaimu babu kowa sai mu kaɗai da muke rayuwa, har na fito titi ma na rasa wanda zai taimaka min". ya sauke numfashi yay mata nuni da Emanuel da ke tsaye shi ma hannayensa sarƙe a ƙirjinsa, zuciyarsa cike fal da tarin abubuwa mabanbanta, yace ma ta. "bani na tsintoki ba, wannan shi ne ya tsinto ki". ta ɗago ido ta dubi Emanuel, wani irin kallo ta ke masa mai kama da kamar ta san fuskarsa sai dai ba zata iya tunawa ba. "shi ne uban gidana, shi ya bigeki da mota ya ɗaukeki ya kawoki asibiti...". daga nan kuma ya shiga zayyane ma ta labarin duk abin da ya faru har zuwa gaɓar da ake kai yanzu, to amma da mamakinsa tun daga lokacin da ya soma maganar ha
🏠