ar tana gabansa a lokacin ta gyaɗa masa kai,"to shikenan na gode Kabir". ta tari numfashinsa akan maganar da zai yi da faɗin,"ina ɗaga wayarka kenan Malam ya aiki su Hussaina, sai dai idan ta dawo zuwa anjima zan kiraka".a sannan wani annuri na fuskarsa ya ƙaru yace da ita,"tom sai na jiki...amma nan da 3hours dai ina jirgi". daga haka kuma suka yi sallama.
ya koma mota drivern yaja su zuwa airport, a duniyar tunaninsa ta yau gaba ɗaya cike take da tausayin Kulu, in banda ƙaddara me tsanani me zai baro Kulu daga cikin daularsu ta koma rayuwar ɗan akurkin gidansu.
*Ethiopia, 2:00pm.*
zaune su ke shi da Abdurrshim su na cin abincin rana, Kabir abincin kawai yake ci amma hankalinsa ba awajen yake ba, yana can wata duniyar ta tunanin ƙalubalen da zai fuskanta akan tabbatuwar mafarkinsa, Aure! aurensa da Mairo.
ya furzar da iska daga bakinsa yana maida kansa jikin kujera, idanuwansa a lumshe ƙirjinsa na motsawa. "wai dan Allah ba zaka faɗa min abunda ke faruwa bane Kabir?, a ranar yau kaɗai na fuskanci akwai damuwa a tare da kai kuma kake ɓoye min...duk da ban sani ba amma zan iya cewa akwai alaƙar damuwarka da masarautar Qatar da muka baro, dan Allah ka faɗa min ko zan iya baka tawa gudunmawar wajen ganin komai ya warware maka". idanun Kabir har yanzu a rufe suke bai buɗe ba, yace da shi,"karka damu Abdurrahim, damuwar ƴar kaɗan ce wanda ba zan iya maganceta ba ko wani ya magance min, Allah yana sane da lamarina, shi zai shiga cikin lamarin ya warware min matsalar". rufe bakinsa yay daidai da shigowar kira a wayarsa, Kulu ce dan haka yay saurin ɗagawa, muryata ta fito a hankali da ce masa,"ya ake ciki ka sami ganin Hussainar?". nauyayyan numfashin da ke ƙunshe a zuciyarsa ya saukar, sannan ya fesar da numfashin daga bakinsa. "komai ya kammalu, fallasuwar ɓoyayyen sirrin kawai ya rage...ina jin wani nauyi a ƙasan zuciyata kamar an ɗora min babban dutse, ki saka min muryar Maryam ko zan iya samun ƙarfin jikina ya dawo daidai". daga cikin banɗakin da Kulu ta ke ta dafe goshi a ranta ta furta Ya Salam, yanzu ya zata yi, ɗazu ma fa ƙarya tayi masa, ita dai ko ta sanar masa da gaskiyar ɓatan Mairo ne ta huta da kwane-kwane?, ɗayan ɓarin zuciyarta ya kwaɓeta akan faɗa masa hakan, tana cikin neman mafitar ƙaryar da zata sake yi masa Yagana ta shigo gidan, maganarta kuma ta karaɗe cikin gidan, Kulu ta sauke wata ajiyr zuciya da yin hamdala ga ubangijinta, sannan ta maida wayar ta kara a kunnenta tana ce masa,"Kabir anya kuwa karaɗin Yagana zai barka ka ji muryarta?, ka kalla tunda ta shigo gidan ta ke sababi ta hana kowa magantuwa, ga shi nan ma fita zasu yi da Mairon". bai san ya akai ya tsinci guntun murmushi a fuskarsa ba, murmushin da ya haifar da shan jinin jikin Kulu dan tasan bai yarda da maganar tata ba, amma sai taji yace,"naga ranar da Yagana zata shigo gidan nan bata yi sababi ba, shikenan ki nutsu kamin wani ya shigo banɗakin zan miki bayanin komai".
gida biyu ta raba hankalinta, kaso ɗaya a tare da Kabiru kaso ɗaya a tare da Gwaggo wacca ke can ɗaki likita ke kanta jikinta yay tsanani.
"kin san me ya faru?".yay mata tambayar yana miƙewa daga living room ya wuce zuwa bedroom, Abdrrahim ya bi bayansa da ido da son gano wani abun. Kulu tace,"a'a sai ka faɗa". yace,"ban taɓa ganin abinda ya tsoratani ba irin kamanninku ke da ƴar'uwarki, na tsorata ainun a lokacin da na shiga office ɗinta na sameta, tsoro fa bana wasa ba, saboda a tsammanina ma kece, Allah da iko yake, bayan kamarku hatta muryarku ma iri ɗaya ce". tai murmushin da ya sauka a iya leɓenta,"da kamanninmu da muryarmu iri ɗaya ne, amma kuma idan ka ganmu tare zaka iya banbance mu". "ta ya ya kenan?, to kin san Allah san da nai tozali da ita nayi zaton ko wasa kike da hankalina, ƙila kina so ki haɗa min gadar zare ne, san da na kiraki banyi magana ba ai dan na tabbatar da bake ɗin bace yasa na kira, gaskiya ga duk wanda yake da saurin firgita idan ya ganku tare to zai iya suma". tai gajeriyar dariya da cewa,"ka jira ka ganmu a taren tukunna, da kanka zaka zaƙuloni ba tare da rikicewar lissafi ba, akwai abin da ya banbantamu".
yace,"to ai shikenan...kamar yanda kika sani nayi duk abin da kika ce, na shiga masarautar Al-Harar harma na sami ganawa da Mai Martaba, sannan naje Qatar ma amma shi ban sami shiga cikin masarrautar taku ba saboda tsaron da ke cikinta, amma naga Al-Hassan kuma naga Umm da idanuna, sannan na sami labarin Abi daga wurin limamin wani masallaci.
da ka duka waɗannan ɓangarorin an sami saɓanin tunaninki akansu, daga ta kowanne ɓangare cike suke da kewarki da kuma cigiyarki da basu daina ba har yanzu, liman Shaik Albani ya shaida min ko a sallar asubahin yau sai da Me Martaba yay hawaye akan rashinki, yana adu'a iyakar adu'a akan idan har kina raye a duniya to ubangiji ya bayyana musu ke a duk inda kike...Umm ma akan yawan kukan rashinki ta kamu da matsalar ciwon ido...duk abun da ya riga ya faru ya riga ya faru, burinsu a yanzu na ki dawo garesu ne, fatan iyayenki ki d