NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 97 of 223

anda ke cikin motar, dan haka dole ma yay binciken wanda ya wuce acikin motar. "Driver kabi min bayan waccen motar". abin da yace da me taxi kenan, suka shigo ciki shi da Abdurrahim. Driver faɗi yake,"Yallaɓai ina fatan dai silar hakan ba zai sa na shiga wata matsala ba, domin na lura kai ɗin kamar ma'aikaciɓ bincike ne". "kar ka damu babu wata matsala da zata gifta, ni ɗin ba ma'aikaci ba ne akwai abin da na ke nema dai...ka ƙara speed dan Allah kar su ɓace mana". me motar ya ƙara gudu yana bin bayan motar da irin dabarar da ba za'a gane bin ta yake ba. motar bata tsaya ba sai a wani ƙaton building da ke ɗauke da rubutun Qatar Charity. su kuma tasu motar ta tsaya daga baya, Kabir ya rufe ido yana roƙon Allah akan Allah yasa kar motar tasu ta shiga cikin gidan marayun ba tare da ya ga Al-Hassan ɗin da zuciyarsa ke zullumi ba, ga shi shi ba irin shigar da zata nuna shi ɗin me tsananin buƙatar taimako bane balle yayi amfani da damar hakan a dabarar da ke cikin kansa, yasa yatsunsa cikin sumar kansa ya yamutsa gashinsa yana cije leɓensa na ƙasa. kamar ance buɗe idonka, yana buɗewa yaga motar na bakin gate bata kai ga shiga ciki ba, sai kuma biyu daga cikin security ɗin da ke tsaron wajen su ka zo suka buɗe murfin motar na ɓarin dama da hagun. Kabir ya buɗe motar ya fito ya tsaya daga gefe kamar wanda hankalinsa ba'a wurinsu yake ba, ta gefen idonsa yake kallon matar da ta fito daga cikin motar sanye da baƙar abaya, fara ƙal da ita wadda zai iya kira da potocopy ɗin Mairo ta yanda take takun tafiyarta, fuskarta cike da annuri idanunta kuma na ɗauke da gilashin da zai baka tabbacin medical ne. yes! ba shi da haufin cewa wannan ita ce mahaifiyar su Kulu dan ga kamanni nan sun bayyana, ya leƙa cikin motar yana tambayar me taxi, "dan Allah wace ita ɗin?". ya ba shi amsa da,"Yallaɓai wannan ita ce Sarauniya Asma matar Mai Martaba". maida dubansa gareta da zai yi sai yaga wani ɗan saurayi tsaye a kusa da ita tana mishi bayani yana kaɗa kai alamar yana sauraronta, shi ma fari ne ƙal kyakykyawa, dogo, siriri, gefen idonsa akwai abar da ake kira da tusar jaki, akwai kama ta jini sosai a tsakaninsu, bai yi tambayar da zai sake yiwa me taxi ɗin ba ya sami amsarta daga Umm da sautin muryartata ya sauka a kunnensa tana faɗin,"Al-Hassan". ta kira sunan ɗan saurayin da ya juya zai shiga cikin gidan marayun. anan Kabir ya sami damar ƙare masa kallo, sam basa ma kama da Kulu bama zaka ce ɗanta bane indai ba ka lura da kama ta jini ba, kawai dai a surar jikinsa ne suka yi yanayi da Mairo da idan ka gansu tare zaka iya cewa Yaya da Ƙanwa ne. yay wani sanyayyan murmushi na nuna jin daɗi, sannan ya lalubo wayarsa daga aljihu ya danna kiran lambar Kulu amma sai dai yana ta kiran bata shiga ba, sai can kuma ta shiga a bugun farko kuwa muryarta ta shiga kunnensa. "Salamu Alaikum Kabir". sai ya lumshe idonsa ya jingina daga jikin motar, ƙarshen aikinsa yazo, haka kuma ƙarshen komai yazo. ya amsa sallamartata,"wa alaiki salamu da Aaliyah, barkanki da wannan lokaci". bata yi mamaki ba domin tasan dole ayanzu zai san asalin sunanta in har yay binciken da tasa shi, saboda haka ta amsa masa da,"wane tarihi ka samu ga me da wannan sunan?". har yanzu wannan murmushin na jin daɗi bai bar fuskarsa ba yace,"duk wani bayani ki bari ba yanzu ba sai zuwa anjima...yanzu dai babban albishir zan miki". cike da zumuɗi me ɗauke da fargaba tace, "Allah yasa albishir ɗin da zai yaye min wani kaso na cikin damuwata ne, ina sauraronka ɗan halak". Ya shafi goshinsa yana cewa,"gani a kusa da Umm da Al-Hassan". sunayen da ya ambata suka daki zuciyarta bugunta ya sauya,"Kabir ka san waɗannan sunayen a bakina, saboda haka karka yi wasa da ni dan wanzar min da farincikin da ba zai ɗore ba". "wallahi da gaske nake miki, tsakanina da Al-Hassan ma bamu da tazara, gashi nan ya girma ya zama saurayi kamar yanda Maryam ɗita ta zama budurwa". a ɗan shiru da ta yi zai iya rantsewa hawayen farin ciki take, kuma bakinta yaƙi rufuwa saboda farincikin da ya lulluɓeta, ya katse wannan shirun nata da tambayar,"amma ko kusa ko alama babu kamanninki a tare da shi, banda kamanni ta jini da kuma kasancewarsa tare da Umm da zan rantse nace ba shi ne Al-Hassan ɗinki ba". ta bashi a amsa da,"ai shi kamar mahaifinsa yayi tun a ranar farko da ya zo duniya...Kabir ina so na dawo cikin ahalina sai dai ban san ya zanyi ba, ubansu ya zama silar tarwatsewar duk wani farinciki nawa". ya sauke numfashi yana faɗin,"karki damu in Allah yarda komai zai warware acikin sauƙi". ta amsa da,"Allah ya yarda". sannan ta kuma ce masa,"to baka sami labarin Hussainar ba?". yace da ita, "yanzu tunda na gama da nan da zarar na sauka a Ethiopia wurinta zan fara sauka, ita ma zan gano miki ita da lafiyarta, karki damu". ta sauke numfashi sannan tace,"to baka ce min komai ga me da Abi ba". "nace miki sai na tattara dukkan bayanan komai sannan zan sanar miki, nan Qatar dai na gama da ita, Hussainarki ce kawai tayi saura acan ethiopian ma". kam
🏠