ad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*27)*
"me muka zo yi anan?". Abdurrahim ya tambaya a san da ya waigo ba ya yana duban Kabir, yaji tambayar tasa amma sai dai bai amsa masa ba, dan ya tattara hankalinsa gaba ɗaya zuwa ga fuskar masarautar da ke fuskantarsu, ba komai yake kallo ba illa hoton da ke ajikin ƙatuwar fastar da aka manna daga wajen ginin.
ya san akwai identical twins, amma shi tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin twins ɗin da su kai tsananin kama da juna ba irinsu, kai ko a labari ma bai taɓa ji ba, duk kamannin da suke da su dole akwai ta hanyar da ake gane su, amma su waɗannan kamanninsu ya zarce tunanin mutum ko hasashensa, idan har ba sa ni kayi ba to zaka rantse da Allah mutum ɗaya ne shege editing ya maida shi biyu.
gaba ɗaya ya rasa wacce a ciki zai nuna ya kirata da sunan Kulu, to ko dan ba'a kusa da hoton yake sosai bane yake ganin hakan?. ya ɗauke kallonsa daga barin kallon hoton fastar ya dawo da kallonsa ga hoton Kulu da ke cikin wayarsa, ya jijjiga kai yana mai ƙara jinjinawa sarautar ubangiji, a sannan kuma hoton Mairo ya haska a cikin idonsa, lallai ne maganar hausawa da suka ce sai kasa aka sannan kake ɗauka, in ba haka ba ai akwai tsananin kama a tsakanin Mairo da Kulu, ana sakata a tsakiyar hoton nan zasu tashi a sahun identical twins su koma identical triplet, banbancinta da su ɗan kaɗan ne fuskarta tafi tasu siranta sun kuma fita hasken fata, amma daga wannan ba zai iya kawo wani abu da zai ce ya banbanta kamanninsu ba.
kunna datar wayarsa yayi ya shiga goggle inda ya tafi kan map yana duban ta yanda zai tsarawa shiga gidan ba tare da tambaye tambaye ba har ya isa ga inda Kulu ke so ya isa, wato turakar mahaifiyarta. yana shafa wayar yana dariya ƙasa ƙasa saboda mitar da Abdurrahim keta zabgawa, shirun da yay masa kuma na ƙara hasala shi har da buɗe motar ma ya fice ya tsaya daga waje, Abdurrahim ɗin faɗi yake,"Kabir inda nasan da wannan walaƙancin naka wallahi da ban biyoka ba, kazo ka shanyamu a waje kamar waɗanda aka sassaƙa, ana tambayarka kuma ka share mutane saboda rashin mutunci". bakinsa kuma ya ɗauke da maganar lokacin da idanunsa suka kai masa kan fastar hoton kyawawan ƴan matan su biyu, kana ganinsu kaga larabawan asali, ga shigar da suka yi ta abaya ta ɗaukesu.
ya murza hannayensa yana me leƙo da kai ta glass yay knocking Kabir ya zuge,"Kabir kaga wasu zuƙa-zuƙan ƴan mata anan, la'ila ha'illallahu ka fito malami ka gani mu san yanda za ai". Kabir na jinsa yay masa banza bai tanka shi ba, shi kuma bai fasa surutan da yake ba, har tambayar me taxi ɗin da ya ɗaukosu yake wai ya bashi shawarar da zai shigar da kansa cikin masarautar ko kuma inda zai sami numbar ɗaya daga cikinsu, shi ma Babansa na da kuɗi dan haka Al'amarin aurensu ba zai yi wuya ba, Me taxi ɗin dai murmusawa kawai yay.
Kabir da ya jishi yay tsaki da cewar,"ashe dai bani kaɗai ne mahaukacin ba". "Malam ban sa da kai ba, kai sabgarka nayi tawa". Kabir ya ƙyalƙyale da dariyar da ta ƙular da shi ya ƙara hawa sama da mitarsa.
_"yallaɓai akwai tsaro sosai a wannan masarautar, in dai ba kana da alaƙa da ita ba to ƙofar wajen ma baka zuwa dan hakan zai iya jefa aka a haɗari...yanzu ma ko da munje daga tsallaken titi zamu tsaya saboda ba'a parking a wajejen"._
maganar mai taxi ɗin da ya ɗaukosu daga airpot ta haska masa acikin ka, ehh tabbas kamar yanda ya faɗa akwai tsaro me tsauri ma kuwa...ba ya jin akwai ta yanda zai yi ya sami shiga cikinta, saboda haka zai haƙura ne kawai ya koma, tunda in har ba shiga ɗin yay ba, ba zai sami abinda yazo nema ba, kuma idanma zai sami bayanin da ya ke so ɗin daga wajen wani to dole sai wanda yake mazaunin cikin masarautar ne.
ya buɗe murfin motar ya fito ya jingina da jikin motar, hannayensa harɗe a ƙirjinsa yake kallon masarautar da tunaninka mabanbanta acikin kansa. fitowar wata farar mota ƙirar BMW daga cikin masarautar ya ɗauki hankalinsa, bin motar yake da ido har san da ta hau kan titi idonsa ya sauka akan lambar motar da ke ɗauke da rubutun sunan *Al-Hassan Bin Samin Al-Thalis* da manyan baƙi, ta ke anan maganar Kulu ta gifta a cikin kansa. _"ina ji ajikina Al-Hassan yana tare da ahalina, duk da cewar mahaifinsa ya ƙwace shi daga hannuna, amma na san ba zai iya ɗaukar nauyin riƙe shi ba, so dole ne ma cikin biyun ɗaya, ko ya salwantar da rayuwarsa ko kuma idan da sauran wannan ɗison imanin da na fara saninsa da shi a zuciyarsa to zai miƙa shi gidanmu, zuciyata na cikin zullumin son sanin a wane irin hali Al-Hassan ke ciki, wallahi bana iya bacci saboda tunaninsa, ka taimaka min Kabir"._ bai san ata yanda zai kwatanta yanda yaji ba da ganin wannan motar, suna kawai ya gani ba shi da tabbacin w