NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 95 of 223

in ƙafafunta ta fashe da sabon kuka mai tsuma zuciya, tunda har Dad ya faɗi haka to tabbas hakanne dan haka dole ta bar kokoton alaƙarsu da ita. Emanuel ya fito yazo gabanta ya tsuguna, ya dafata da faɗin,"Gift kiyi haƙuri duk ni naja miki". bata ɗago ba, domin ɗagowarta a halin yanzu zai iya janyowa tayi masa abun da zai haddasa tashin hankali fiye da wanda take ciki ayanzu, domin shi ne silar wanzuwar komai da ke faruwa a duniyarta. wayarsa ce tayi ƙara, yasa hannu ya ɗaukota daga aljihu. "Hello Sectery ka ƙaraso ne?". daga can ɓangaren Amadu yace da shi,"eh na ƙaraso, ina bakin layin gidan". "oak ka tsaya ga Obi nan zuwa ku taho tare". ko mintuna goma ba'a ɗiba ba sai ga Amadu da Obi sun shigo gidan, yazo ne a bisa wasu muhimman takardu da ake buƙatar Emanuel ya saka hannu akai, ba'a kawo takardun ba kuma sai a jiya bayan tahowarsa daga can, saboda haka ne kawai ya biya masa kuɗin jirgi yace ya kawo masa dan bai saka lissafin dawowarsa cikin wannan satin ba. "me aka mata take kuka haka?". Amadu ya tambayi Obi san da suka ƙaraso wajen, Emanuel ya ɗago ya dube shi, kamar ba zasu ce da shi komai ba kowa yay masa shiru, to amma rashin samun mafitar da su ke nema dole yasa su sanar da shi ɗin, duk da yasan in ya sanar da Md zai sama masa mafita to amma kamin wannan sai ya gama dagula masa lissafi shi kuma bai shirya ɗaukan hakan ba. saboda haka ya sauke numfashi yana duban Amadu, bai ɓoye masa komai ba ya sanar da shi duk abunda ya faru har zuwa halin da ake ciki yanzu. "karka damu ranka ya daɗe, ko mai zai warware cikin sauƙi insha'Allahu, amma abun da baka so ɗin dole shi za'ai, hotonta zamu ɗora a media a shigar da cigiyar iyayenta ko kuma wanda ya santa". Obi ya jijjiga kai tabbacin ya gamsu da shawararsa, Emanuel kuwa ido kawai ya zubawa Mairo da ke duƙe tana ruzgar kukan da har muryarta ta fara dashewa. Amadu ya duƙa a gabanta, da muryar nan tasa da ta ƙware a iya fitar da tausasan lafuza yace da ita, "ƙanwata ki daina kuka kinji, ki ɗago ni zan kai ki gidanku, nasan su waye mahaifanki...amma sai kin daina kuka fa tukunna". tana jin hakan ta ɗago da sauri tana goge hawaye, gefe na zuciyarta na ƙissima irin matakin da zata ɗauka kamin barinta cikin rayuwar mutanen gidan nan. duk da canjawar da tayi hakan bai hana shi ganeta ba, bai san ya zai kwatanta yanda yaji ba san da idanuwansa suka yi tozali da ita, abu ɗaya kawai ya sani ya razana, razana kuma bata tsoro ba, irin razanar da ta haifar da ɗimbin tashin hankali acikin ƙwayar idonsa da zuciyarsa. _Mairo! Mairo dai ƙanwarsu, yau ita ce tayi rayuwar watanni takwas a cikin ƙedarun arna, kuma ta rayu a tsawon watanni takwas ɗin bata ko kallon gabas?._, ya yasar da maɗaukakin al'ajabin da ke lulluɓe da shi yace,"Mairo ce!". ya faɗa da ƙarfin sauti, ya sauke nauyayyan numfashi ya miƙa hannu ya taɓota dan tabbatar da gezon da yake tunanin idanuwansa nayi. tabbas Mairo ce, Mairo ƙanwarsa, Maironsu da suka fitar da rai da sake ganinta, ashe tana raye kuma a kusa da su. ya ɗaga hannu sama yay hamdala ga ubangiji, tare da ƙara matsowa kusa da ita zai kamo hannunta tai saurin ja da baya, idonsa na kawo ƙwallar tausayinta yace,"me yasa kika baro mu?, kin san tashin hankalin da kika saka mu aciki kuwa?, me yasa kika mana haka?, ko kin san tun ranar da kika barmu har zuwa wannan ranar Gwaggo bata ƙara takawa da ƙafafunta ba, watanni bakwai kenan tana zubar da hawayen rashinki, Mairo me yasa?, me yasa?". ya faɗa kamar zai yi kukan farin cikin ganin nata. ita dai kallonsa kawai take, binsa take da ido ba dan ta gane shi ba, ko kuma wai ta san shi, mamakinta ɗaya ne da ya nuna yasanta ita kuma bata sansa ba, waye shi? daga ina yake? mece alaƙarsu da yake waɗan nan zantukan da suka saɓa masaniyarta?. Obi da su ke tsaye mamaki ya cikasu yace da Amadu,"kana nufin ƙanwarka da ta ɓace ne kwanaki?". jijjiga masa kai yayi tabbacin haka, sannan ya umarci Mairo da ta tashi su tafi amma taƙi tace sam ita ba zata bishi ba, shi ma zaije ne ya biya buƙatarsa da ita ya tozartata. da ya fusata dai ya kai hannu zai kai mata duka, ƙarar bindiga da suka jiyo daga cikin gida yasa duka suka zabura, banda Mairo da tai saurin saka hannu ta toshe kunnuwa tare da rumtse ido gam jikinta na kyarma, kuma acikin muryar kuka, muryar da ke naɗe da firgici da tashin hankali, muryar da babu ƙwarewar hausa acikinta ta fita da ƙarfi wajen furta,"Gwaggo". a lokaci ɗaya duhun da ke cikin ƙwayar idanunta ya hasko mata san da suke gudun fitowa daga cikin dajin nan dan su samu su tsira da ransu daga wurin kidnapers, har lokacin da fito bakin titi tana rangaji, daga nan kuma ba zata ƙara tuna komai da ya faru ba, abu ɗaya da zata tuna sun baro cikin dajin da mutane da yawa, kuma abu na ƙarshe da ta san kunnuwanta sunji shi ne harbin bindigar da ya dinga tashi kamin kuɓutarsu daga hannunsu. *Qatar, A wannan ranar.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattp
🏠