NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 94 of 223

faɗa yana huci akanta. Mom ta kama hannunta tana janta, dai-dai lokacin da Dad ya sako kai parlourn. Sakin baki da hanci yayi yana kallon yanda Mom ke janta ita kuma tana turjewa. "Gloria mene hakan?, wai ke me yasa sam ba ki san baƙo ba, ba kya kallo ita ɗin yarinya ce, kuma mara lafiya". ta dube shi tana yatsine fuska tace,"baƙuwa! yarinya! mara lafiya!...baƙuwar ce zata zauna a gidana a rufe min saboda munafurci?, ko kuma yarinya ce zata kalleni ta faɗa min cewar nan gidan ubanta ne sai dai ni na fita ba ita ba?, mara lafiyar ce ke tsaye da ƙafafunta haka har tana yunƙurin karawa da ni?...to what ever dai zamanta a gidan nan yau ya ƙare, in har kuma ba kana so na tabbatar da zarginka da zuciyata ta fara a yanzu ba". ta faɗa tana sake figo Mairo da ke ta son ƙwacewa amma ƙarfin ba ɗaya ba ne. Dad ya dakatar da ita acikin tsawa, "wai ke wace iriyar macece mara tausayi, an faɗa miki bata da lafiya she miss her tought, idan kin kwantar da hankalinki tana zaune damu ne zuwa ranar da zata sami lafiya akaita wurin iyayenta, ki tsaya a fahimtar da ke abu amma kin tsaya kina hargagin banza". a fusace tace da shi,"wane irin alaƙa ne tsakaninka da ita da ka ɗora alhakin kulawa da lafiyarta akanka?...Major ka faɗa min gaskiya tun ban aika da ita lahira ba, aina ka samota da kake cewa da Yarana sister ɗinsu ce, ko hakan na nufin kaci amanata ne?". ƙarashen maganartata ya fito da sautin karaya da kuma tsantsar tashin hankali acikinsa gami da fargabar jin amsarsa, Dad cike da takaici yace da ita,"ke kin san ni ba irin wannan mazan bane, kin san da cewar ni me kare mutunci kaina ne...kuma har kullum ina faɗa miki ba sai kana da alaƙa da mutum kake taimaka masa ba, balle ɗa wanda yake na kowa, ke uwa ce kuma irin uwar da ke tsananin ƙaunar ƴaƴanta, ki kimanta aranki in ace ƴarki ce a irin situation ɗin da take ciki ya za kiji idan wani ya wulaƙantata?, to ni na ɗauketa matsayin ƴata tun a ranar da ta shigo rayuwarmu, saboda haka zata ci gaba da zama acikin gidan nan har zuwa ranar samun sauƙinta...gida nawa ne bana kowa ba, ni ke da ikonsa". Gloria ta saki wani murmushi me ciwo,"kaga Major, just go streight to the point kace min kaci amanata ka munafurceni ka samar da wata ƴar a waje, ai dama you have said, kana haihuwa har yanzu dan haka zaka haifi ƴa mace ko min daren daɗewa". sai kuma ta ƙara fusata a cikin ƙarajin murya tace,"saboda naƙi baka haɗin kai shi ne ka fita waje kaje ka auri wata?". Dad ya tsinka mata mari rai a ɓace yace,"you know me well ni ba sakaran namiji bane da zan tsaya jin surutan banzanki akaina ba, ga ɗanki shi ne sanadin zuwanta gidan nan, sai ki tambaye shi a inda ya samota". Ya faɗa rai ɓace yana barin wajen bayan ya nanata,"Gift ba zata bar gidan nan a yanzu ba, saɓa maganata zai haifar da babbar matsala tsakaninmu da ke". Madam Gloria ta juya to dubi Emanuel da ya sunne kai a ƙasa yana murza yatsu tace da shi,"dama nan police station ne?". yay saurin girgiza mata kai alamar a'a. tana ƙara matsowa kusa da shi ta kuma cewa,"nan gidan ophanage ne?". nan ma yace a'a. "So i din't get you well, mene alaƙanka da ita daka maida ita ƴar gidan nan?". "Mom bata da lafiya ne kuma ni ne silar ciwonta". "Ohh yaushe ka zama likita banda labari?, you are just telling me ka bigeta kuma kai ne sila, and so?, da ka bigeta shegiya ce ita da ta rasa iyayen da za su kula da lafiyarta?, shashasha kana 33years amma baka haɗa hankalinka ba, to mace shaiɗaniya ce, kana kallonta haka sai ta jefa ka a ruwan zafi ta wuce ta barka aciki, mumu kawai". ta ƙarasa zancen tana dungure masa kai, sannan ta juya ta koma kan Mairo, ɓacin rai fiye dana ɗazu tace,"yanzu tun da kin gane ba gidan ubanki bane sai ki fita, ki warke acan waje amma ba'a gidana ba...idan kuma kinƙi ji to tabbas zanyi reporting naki to police nace kin maƙalewa ɗana da mijina, su na san za suyi mana tsakani". bata jira wani Abu ba tasa duka hannu biyu ta watsa ta waje, ita kuwa ba komai ya haddasa suman tsayen da tayi ba sai furucin da ta ji anayi akan ita ba ƴar gidan bace. masifar Madam Gloria da jarabarta ya hana kowa motsi, faɗa kuwa kamar zata zane Emanuel, Granny ɗinma bangajeta tayi ta wuce tana faɗin,"kowa ma munafiki ne a gidan nan, anci amanata kuma ba zan yafe ba...Joseph biyo ni ɗaki". sai kuma ta nuna Emanuel da Obi,"kar wanda ya kusantoni acikinku, tun da da ku zaa haɗa baki a cuce ni...har kun saka na fara tantamar anya ku jina ne?". Mairo dai tunda aka wurgota waje ta zube a entrance na shiga parlon tana kuka, kukanta bana korar da akayi mata bane, kukan bala'in da take ciki a tata duniyar ne. idan har da gaske nan ba gidansu bane to ina ne nasu gidan?, kuma Dad ba mahaifinta bane?, Brother ba Yayanta bane?, Granny ba kakarta ba ce?, to su wane iyayenta?, and me ya sameta da har ta kasa tuna komai bacin rayuwar da tayi a lagos zuwa yanzu. tarin tambayoyin da ke haskawa kenan acikin kanta, sai dai bata san ta ina zata samu amsarsu ba, saboda haka ta kuma cusa kai a tsakan
🏠