an tabbas wanzuwar abin da zuciyarsa ke ƙissima masa sai ya faru.
Da yamma su na zaune dukansu anan main parlo suka ji maganar Mom akansu, babu zato ba tsammani dan babu wanda yasan da dawowarta, ba gaban Emanuel kaɗai ba, hatta Obi sai da gabansa ya faɗi, ya san Mom, ya san Mom sarai da abunda zata aikata, a yau wani ikon ubangiji ne kawai zai sa Mairo ta ƙara kwana a gidan.
ita kuwa shigowar tata ma sam bata lura da Mairo ba, tana ta amsa sannu da zuwa daga bakin ƴaƴanta da kuma sirikarta, da ƴar me aikin da ta zo karɓar jakar hannunta.
Mairo kam ko kallon inda take bata yi ba, balle dawowarta ta dameta, haushin Mom ɗin take ji tun a ranar da Granny ta shaida mata ba ita ta haifeta ba, ita Mom dinta ta rasu tun tana jaririya. ta rutsa Granny da tambayar ne san da ta kasa danne damuwar da ke ranta na nuna halin ko in kula da Mom ɗin keyi akanta kamar ba ƴarta ba, sai dai taga kowa na waya da Mom amma banda ita, kuma ko ta yo waya zata tambayi kowa banda ita, sannan ko da aka bata waya numbar Mom ɗin ta fara kira amma sai tace ma ta ai tayi ɓatan number, ita bata haifi wata ƴa mace ba balle ƴa me suna Gift.
wannan maganar yasa ta ɗorawa kanta ayar tambaya in har wannan alamun da suke bayyane da kuma furucin da Mom ɗin tayi mata to tabbas akwai wani ɓoyayyan abu, ta san dai Dad shi ne mahaifinta, to ita ina tata Uwar?. sakkowar da ta yi babu shiri daga sama kenan ta sami Granny da tambayar ina tata Mahaifiyar, Granny kanta tayi mamakin tambayar dan alokacin tsayawa tayi kawai tana bin ta da ido, kuma Mairon bata ba ta damar yi mata wata tambayar ba ta fashe mata da kuka akan ta sanar mata ina tata Mom ɗin, dan Mom ɗinsu Joseph ta shaida mata ba ita ce Mamanta ba, dalilin da ya sa Granny tayi mata ƙarya kenan da cewar Mamanta ta rasu lokacin haihuwarta, kuma Mom ɗinsu Joseph ita Ƴaƴanta kawai take so, kamar bata yarda da zancen Granny ɗin ba dan taga alamun rashin gaskiyar maganar ɓaro-ɓaro a tare da ita, to amma da Dad ya dawo ya tabbatar mata da hakan dole ta yarda, ranar kuwa tayi kuka kamar zata shiɗe, kuma da ta tambayi hoto sai suka bata hoton Cousin Sister ɗin Dad da Granny ta riƙeta ta mutu shekaru uku kenan.
sam batayi niyyar mata sannu da zuwa ba dan a ƙullace take da ita, to amma haɗa idon da suka yi da Emanuel yasa taci wata daraja ta ɗanta, sai ta ɗauke kai gefe tukunna tace,"welcome back Mom". a sannan ne Madam Gloria ta juyo a sukwane daga ɗaukar hanyar stairs da take ƙoƙarin yi, sabuwar murya ce taji, muryar da bata taɓa ji ba balle kuma zamanta a gidan, saboda haka ta shiga bin kan kujerar da kallo har ta sauke ganinta akan Mairo.
sai ta tsaya da bawa Buky jakarta tace,"what are my eyes seeing?, what is this thing?". ta faɗa tana nuna Mairon da hannu kamar wadda taga abin amai, kamin kowa yace mata wani abu ta ƙara da cewa,"heyy who are you?, me ya kawoki gidana?, zaman me kike min a parlo?". duk a cikin saurin murya ta jefa mata tambayoyin, kuma duk a lokaci ɗaya ta maida kallonta ga su Emanuel cikin shouting tace,"kuna ji ina tambaya kunyi shiru da bakinku anan kaman na kwaɗi".
Joseph yace da ita,"tafiyarki da kwana biyu tazo gidan nan". da ƙifƙiftawar idanu dan son ƙara tabbatarwa ganinta da kuma abun da ɗanta ke faɗa ta buɗi baki tace. "you mean all these while that am not around tana gidan nan?". "yes Mom".
"to me take yi?, ina da ƴan aiki wadatattu nasan bata da wani space da zata karɓa, so zaman me take yi?, ina tambayan ne ga dukanku kunyi shiru sai Joseph ke bani amsa". tayi maganar da dukansu a tsawace.
"wai sabuwar daughter ce a gidan nan". ya ƙara amsa mata. ita dai Granny tana jinta, tayi shiru ne kawai har ta gama kumfar bakin sannan ta faɗi abunda idan ta faɗe shi ya zauna.
amsar Joseph ɗin ce tasa ta jefar da jakarta saboda gigita, da sassarafa me kama da gudu ta ƙarasa gaban Mairo ta kamo hannunta ta miƙar tsaye, ta kai hannu idonta tana faɗin,"kin wane kafeni da wannan ƙwalaƙwalan idanunki za ki cinyeni, to kurwana yafi ƙarfinki...this house is for only me and my childrens, so kinga hanya bi ki koma inda kika fito". ta faɗa tana nuna mata ƙofa.
Mairo ta ƙwace hannunta, ita ma tana cije fuska tace,"ni da gidan ubana ace na fita, to babu inda zani...kawai saboda Mamana bata raye sai ace za'a tsangwameni, daɗin abin my Dad loves me, and he can do anything for me. so kibi a hankali, ke matarsa ce, ni kuma ƴarsa ce, akwai tazarar matsayi me nisa a tsakninmu. ke zai iya rabuwa da ke, ni kuma ƴarsa ce da ba zai taɓa rabuwa da ni akanki ba, saboda...". sauran maganarta ta katse san da taji saukar mari a fuskarta, Mom ɗin ce ta kifeta da shi, kamin ta ɗago gaba ɗaya Emanuel ya ƙara kwasheta da wani marin,"she is my Mom ki iya bakinki akanta, zan iya zuba miki ido akan komai amma banda ita...dama ko Mom bata tambaya ba nasaka araina cewar duk ranar da ta dawo za ki san matsayinki a gidan nan, uzuri ɗaya zan miki na rashin sanin komai amma da sai kin gane ba ki da wayo akan abin da kika aikata". ya