dan in gano shi da aikata wani mugun aikin ba...i have 100% sure ba wani mugun abun yake ɓoyewa ba, kai baka tunanin abun da yake ɓoyewar ya shafi rayuwarsa ne kuma hakan zai iya jefa shi cikin haɗari?, to wannan dalilin yasa nake so na koyi yanda zanyi binciken akan abinda yake ɓoyewar, dan muga ta inda zamu taimaka masa mu warware bakin zaren, mu fitar da shi daga tashin hankalin da yake ikirarin acikinsa yake". tayi shiru sannan ta jinginar da kanta a saman kujerar, taci gaba da cewa,"sai dai kuma akwai wani hanzari ba gudu ba, idan har abun da Dad ke ɓoyewa ya zama shi ne me cutarwa, ko yana cutar da iyalansa ko kuma yana cutar da al'umma ta wata hanyar, to ba zan ƙyale ba, zan gargaɗe shi akai, idan kuma yaƙi ji zanyi ƙararsa ga hukuma ta hukunta shi". Obi yay mata wani kallo na baki da hankali, kamar ya sanar mata da matsayinta, sai kuma dai bai yi hakan ba saɓanin wani tunanin da ya gimla masa, dan haka yace da ita,"a matsayinki nawa za ki ƙararsa?".
tayi wani guntun murmushi tana kora lemu mai sanyi a maƙoshinta,"ba lallai sai na kai wannan level ɗin da nake son kaiwa na Detective ba sannan ne zan iya yin ƙararsa, as far as i got the evidences magana ta ƙare, you know me well akan bigiren gaskiya na ke, kaima kasan da hakan". Obi zai sake magana ƙarar wayarta ya katse abinda zai ce, a shekaranjiya ne Dad da ya dawo daga London yay mata kyautar waya babba mai tsada saboda sakamakon da ta ƙara fitowa da shi me kyau na wannan term ɗin, Emanuel kuma yay mata kyautar system ɗin da take kallo acikinta yanzu. bata ko kalli screen ɗin wayar ba dan ganin sunan me kiran, saboda tuni ta gane me kiran tun a taken waƙar da ke tashi, ringing ɗinsa dabanne dana kowa, Emanuel! Emanuel Brother ɗinta da take so da ƙauna, shi yasa take banbanta komai nasa a wajenta da na kowa.
Obi ya kai dubansa ga screen ɗin ganin taƙi ɗauka, hasalima ɓata rai take. "Brother ne fa ki ɗaga mana". cikin turo ƙaramin bakin nan nata gaba tace da shi,"ka ƙyale shi munyi faɗa". "da Brothern?, Gift kin cika rigima ke dai, to akan mene ku ka yi faɗan?". Obi yay tambayar dariyar fuskarsa bata ɗauke ba. tayi narai-narai da idanu tana shirin fashewa da kuka,"wai haka yake cewa bani da lafiyar tunani, na shirya zai wuce da ni lagos za'a ƙara min hoto a duba lafiyata, Brother Ema ya daina sona at all". kafin Obi yace wani abu Buky ta shigo Balcony ɗin tana sanar musu da kiran Dad.
Da yamma tana zaune a parlo tana bitar karatu, karatun bokon da bata gajiya da shi sam, Dad da kansa har ya fara yi mata faɗan akan ta dinƙa sassautawa, ƙwaƙwalwa na buƙatar hutu. ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ƙwalawa Buky kira tazo,"mai da min da Aljazeera". Buky ta ɗauki remote ta kamo channel ɗin da ta umarceta.
ita kuma ta karkata hankalinta ga tvn gaba ɗaya, tana son labarai sosai, kallonta a tv ba ya wuce sauraron news ko kuma wani program da ake gabatarwa me amfani, shi yasa Dad yake cewa idan aka cire Emanuel to duk tafi sauran wayewa a gidan, ranar taji daɗi sosai kam. Granny ta ƙaraso ta zauna ita ma a ɗayar kujerar, suka ci gaba da sauraran news ɗin tare.
"azumin yau akwai wahala kam". Granny ɗin ta faɗa tana hamma da alamar gajiyawa tare da ita da kuma sautin maganar tata.
Azuminsu ta ɗauka na ƙarfe shida na safe zuwa shida na yamma, ta ɗauka shi ne musamman saboda Dad da ya ce tayi masa adu'a akan wani al'amari da ke neman jagula lissafinsa, tayi masa adu'a Allah ya saita masa kan komai, dalilin da ya sa ta fara azumin tun ayau.
"kema Granny kin san kina fama da ulcer me ya kai ki ɗaukan wani azumi, gashi sai yanzu ma 12 tayi". "azumin Dad ɗinku ne ai". "umm Jesus ya amsa". Mairon ta faɗa tana kai ayabar da ta ɓare bakinta. baccin da ya fara ɗibanta ne yasa ta miƙe, "Granny bari na kwanta a ɗakinki, bana son hawa sama. idan Thomas yazo a taso ni, Dad yace ya fara koya min mota, so nake mu fara a yau saboda zuwa bikin Abigail ina so ace nima na bada gudun mawa wurin kai friends party".
"shi Dad ɗin yace a fara koya miki driving? ina ce yace ne sai kinyi candy?...wayar ma fa ya ba ki ita ne dan ta dinga ɗebe miki kewa ba wai dan kin isa riƙewa ba...kuma shi ne saboda samun guri har kike ikirarin wani fara driving yanzu salon ki daina maida hankali akan karatunki".
ta ɗan doki ƙafa a ƙasa tace,"Ohh Granny cikas, karki ɓata min budget mana. ke dai ba ruwanki ido naki kawai, ai kema kin san wace ni, ina son karatu sosai dan haka babu wani abu da zai ɗauke min hankali akansa". Granny ɗin na dubanta tace,"to naji za ki koya yanzu, amma kike fita da ita kam ba yanzu ba sai after kinyi candy, Yayyanki ma duk haka aka masu, bare ke da kike mace". wannan maganar ta Granny yasa ta wuce ɗakinta ta fasa zuwa na Granny cikin fushi.
around 2:00pm Emanuel ya dawo gidan, saboda PTA meeting da za'ai a makarantarsu Gift, dan haka Dad yace ya dawo ya wakilce shi ba zai sami zuwa ba. ya shigo gidan Mairo na ɗakinta dan haka bata san da dawowarsa ba, shi ma kuma har yay lunch bai nemeta ba a