NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 90 of 223

a mai tsawo a cikinsa, dan tun san da aka yayesu suka dawo wurin Kakarsu da ta haifi mahaifiyarsu, shi sarkin wannan masarautar shi ne wanda ya haifi mahaifiyarsu. shi kuma sarki Sheikh Samin bin Hamad Al-Thalis shi ne mahaifinsu, shi ne sarkin ƙasar Qatar tun bayan da yay aure har zuwa yanzu, Aaliyah da Akila shi ne ainihin sunansu, kamar yanda ka nuna min wannan hoton fuskar a yanzu, haka hoton Poster ɗinsu ne zai fara yi maka maraba a yayin daka isa masarautar Qatar, Aaliyah(Babbar Hassana) ita aka nema aka rasa har yanzu babu labarinta, Akila(ƙaramar Hussaina) kuma tana nan, ita ce minister of education a yanzu na wannan ƙasar tamu ta ethiopia da kake karatu acikinta, macece me halin kirki da nagarta, sai dai ƙalubale ɗaya na zagi da ƙananun maganganu da take fuskanta a wurin mutane shi ne na rashin aurenta tsawon shekarun da take da su, wasu ma har na ganin ko harka da maza ne ya hanata aure"._ bayanin wan nan dogarin suka haska acikin kansa da idonsa, ba yanzu ba, ba yanzu ba ya kamata ya sanar mata da komai ba sai yaje Qatar ya dawo. _"Distance ɗin da ke tsakanimu nan Ethiopia zuwa Qatar kilomita 2,121 ne, wanda yake dai-dai da 1,318 miles, 3hours, 18minutes kenan. zaka iya zuwa ayau ka dawo"._ bayanin ya kuma haska masa. ya cije yatsa yana tunani, kamin wani bayanin ya kuma haska masa, _"Ƴa ta huɗu a cikin wannan masarautar ta Harar ita ce take aure a nigeria, inda take auren wani sarki a can da ya aureta a sanda ya kawo ziyara wannan masarauta, sunanta Hauwa ƴaƴanta nace mata Ammi, tana rayuwa ne kuma tare da ƙanwar mahaifiyarta da ta riƙeta a wajenta tun tana ƙarama da kowa ke kiranta da Bella, itama matar sarki ce a baya kamin mijinta sarki Mujahid ya rasu."_ a yanzu zuciyarsa ta yanke shawara ne akan ya fara zuwa Qatar ya dawo sannan ya sanar da Kulu komai, dan haka yay dialling number Abdurrahim, yana ɗagawa yace da shi,"Please come take me to airport ko kuma nace kazo muje tare idan ba damuwa". "ina zaka je?". "Qatar". "Qatar kuma?". muryar Abdurrahim ɗin ta amsa da sautin mamaki. "ehh Qatar". "to amma tafiya babu shiri?". "Abudrrahim kuɗi ne suke aikin komai, ka fito kawai, a yau zamu dawo". "tom shikenan gani nan fitowa". *Abuja, Nigeria, A wan nan ranar.* _If you want to use your investigative skills to truly fight crime, pursuing a police detective career is the best choice for you. It's a great career fit for people with meticulous attention to detail, a strong ethical compass, and the patience and perseverance to investigate criminal cases that may progress slowly. Qualities of a Good Detective include:- (1)The ability to talk to people. (2)job knowledge. (3)Observation skills. (4)Report writing skills. (5)Attention to detail. (6)Ability to think outside the box. (7)Courtroom testimony skills. (8)Positive attitude and tenacity._ Bayanan na fita ne ta cikin system ɗin da ke ajiye a kan stool, yayin da Mairo wacce ke zaune akan kujera a balcony ta tattara hankalinta gaba ɗaya a wajen sauraren jawabin da farar baturiyar keyi tana fahimtarsa daki-daki. taci ado cikin wata armless gown blue, kan nan babu ɗan kwali an baza gashin a gadon baya, ƙafarta ɗaya akan ɗaya tana girgizasu. bata san ya shigo wajen ba, bata san da zuwansa ba, haka bata san da tsayuwarsa a kusa da ita ba, domin hankalinta ba anan yake ba, ya tafi ga bayannan da take saurare da kuma hasashen yanda zata cimma karatunta ne. *Detective Gift Tosin Afafa.* ya kira sunan nata sanda yake saka pause a vedion da ta ke kallo. murmushi tayi da ya tsaya a iyakar leɓenta, a kaikaice ta waigo tare da ɗaga kai ta kalle shi, lokacin kuma da ta saki murmushin da ya bayyanar da haƙoranta. ta kamo hannunsa tana matsa masa kusa da ita ya zauna tace da shi, "what is going on Sir Obi Tosin Afafa?". yay murmushi yana ɗora hannu saman kafaɗarta sannan ya bata amsa,"i salute to the daughter who is willing to find out the secret her father was hiding". [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *26)* ya ɗora zancen da cewa,"amma ba kya ganin akwai rashin dacewa a game da abin da kike shirin aiwatarwa?, Dad mahaifinmu ne, mun sansa da kyawun halinsa, duniya ma ta shaida kyawun zuciyarsa, to akan mene kike tunanin zai iya aikata wani mugun abun?, yafi mu sanin dalilin da yasa yake ɓoye mana koma menene, shin ba kya tunanin ko abin da yake ɓoyewar abu ne da ya dangancin aikinsa ne kasancewarsa na soja?, idan yana ƙoƙarin kare ƙasarsa ne fa?". kallonsa take tun daga lokacin da ya buɗe baki ya soma magana har san da yaja baki yay shiru, sannan ta sauke numfashi tace da shi, "ba wai ina binciken bane
🏠