fice daga gidan muna riƙe da hannun juna.
Tafe muke ni da Adawiyya muna ƴar hirarmu ta rayuwa, hirar bata komai bace fa ce wadda ta shafi cikin gidanmu da yanayin rayuwar yanzu da.ke sauyawa, harma da yanda zamu maida hankali sosai akan karatun boko wannan karon idan an koma, saboda wancan karan ba muci jarabawa ba, dan ni ta tara nazo Adawiyya kuma ta goma sha biyu, Ya Amadu kuma yace ta ɗaya kawai yake so, duk sanda muka wuce ta ɗaya la shakka zai ciremu a makarantar.
muna kan gangarawa kwanar gidan Liman Adawiyya ta ce, "Mairo zo mu shiga gidansu Zainabu, rabona da ita tun da muka wanke Allo yau kusan wata guda kenan". Nace mata, "ni kuwa kinga in dai gidansu Zainabu ne ba zani ba, wai tana ƙawarki amma ita bata damu da ke ba sai ke komai Zainabu Zainabu, ke kenan kullum kina kan hanyar zuwa gidansu, ita kuwa idan zan lissafa zuwanta gidanmu bai fi sau ɗaya ba, to ni ba zani ba, zan yi gaba kya taho".
Ban tsaya jin ta bakinta ba nayi gaba abuna, ita kuma ta shige gidansu Zainabu, a rayuwata Zainabu na bani haushi, ba wai dan wani saɓani ya taɓa shiga tsakaninmu ba, shegen son girmanta ne yake haɗani da ita da kuma faɗin rai, gata aba kamar guntun kashi.
A dai-dai lokacin dana iso ƙofar gidan Liman Naci karo da wata arniyar farar mota a bakin masallacin gidan, ban shiga gidan ba sai dana gama ƙarewa motar kallo, irin waɗannan motocin dana fi cin karo da su a binni irin su na kewa Ya Kabiru da Ya Amadu fatan mallaka, duk dana san mallakarsu sai mai shi, wanda ya tara ya ajiye, su kuwa basu ajiye ba basu bawa wani ajiya ba.
Har na shiga gidan Liman ban bar santin motar nan ba, dan harga Allah ta gama tafiya dani, zanso ace ko ɗana ni acikinta ne ayi. Na jima ina ƙwala sallama a tsakar gidan ba'a amsa ba, dana gaji sai nasa kai na wuce ɓangaren Baaba Lami, a falonta na sameta zaune tana shafa man zafi a ƙafa, na ƙarasa kan kujerarta na zauna, yanda naji iska na kaɗawa ta ko'ina a ɗakin yasa na miƙe akan doguwar kujerar tata ina lumshe ido tare da sauke nunfashi, lokaci ɗaya naji idanuna sun fara rurrufewa bacci na neman ɗaukata.
"Mairo ke har yau dai baki koyo yanda ake sallama ba ko?". Na karkace na gyara kwanciyata ina wani daɗa lumshe ido. "Baaba ni kuwa sallama yau ai nayi harda ta siyarwa a gidan nan. Nayi sallama tafi biyar ba'a amsani ba, shi yasa ko da nazo nan naga ba saina ƙara yin wata ba tunda duka na haɗa daga can...sai dai gaisuwa da ban yi ba, amma yanzu ina yini".
Ta harareni da faɗin,"bana amsawa". Sanannan ta hau mita akan lamarin Mama matar Liman kenan, sai ta shige can ƙuryar ɗaka a shigo gida aita ɗaka sallama shiru, wani lokacinma har ayi zaton ko ba kowa a gidan, a haka ne kwanaki ma aka sacewa Isma'il sabon machine ɗinsa da Yayan Liman na binni yayi masa kyautarsa.
Barci har ya fara ɗaukana kuma saina farka nace da ita,"Gwaggo na gaisheki da yi miki sannu da ƙafa, wai idan ta sami lokaci zata shigo ta gaisheki. Ta ba da Nakiya akawo miki tana wurin Adawiyya zata ƙaraso da ita, tace ki adana mata langarta karki salwantar mata da ita".
"amma dai saƙon ƙarshe naki ne ko Mairo?". Idanuna a rufe nace,"bari Adawiyyan tazo kiji daga bakinta". Daga haka bacci ya ɗauke ni, iskar fankar ɗakin na daɗa kashe min jiki.
Ban farka ba sai ana gab da sallar magriba, a firgice na tashi ina tambayar Baaba Lami ba dai Adawiyya har tazo ta tafi ba. Tace min ita ai ko inuwar Adawiyya ma bata gani ba, dama tasan ƙaryata ce na zancen Nakiya, nasa ta saka rai yawun bakinta harda tsinkewa.
Haushi ya gumeni akan Adawiyya, ni dama nasan idan taje gidan su Zainabu ba zata hankalta da lokaci ba, kuma yanzu da za'aje gida Gwaggo na tashi faɗanta akaina zata sauke, tace ai tasan ni ce uwar shiririta. Banwa Baaba Lami sallama ba nai ficewata fuuuu, ina jinta tana agaida na gaba.
A bakin kwana na tarar da Adawiyya a tsaye ta ƙurawa wuri ɗaya ido, langar Gwaggo kuma a ƙasa, murfin langar yayi gefe guda, wanda ya bani tabbacin ɓari ne akayi. Na ɗau langar ina kallon Nakiyar da duk ƙasa ta baɗe samanta, sannan na ɗago na dubeta da tayi tsaye ƙeƙam kamar gunkin da aka dasa, baki na taɓe na ɗau murfin na rufe, nace da ita mu tafi tunda an fasa zuwa kai aiken.
Sai naga ta juyo ta dubeni hawaye na sauka a fuskarta, na waro ido ina tambayarta lafiya? Me aka mata? Me ya faru?. Tasa hannu ta goge hawayen, bata ce min komai ba ta miƙo hannu dan karɓar langar, sai na ƙi bata, nace wallahi sai ta faɗa min abunda ya faru, garin ma ya akai langar da aka gama mana gargaɗi akanta ta fashe haka? Har ƙasa kuma ta shiga cikin nakiyar, ko tuntuɓe tayi?.
Ta kuma girgiza min kai akaro na ba adadi da nake ta jero mata tambayoyi.
Bata bani amsa ba sai da taga ina shirin tafiya na barta sannan ta ce,"wani ne muka yi karo da shi, kamin na ɗago na ba shi haƙuri ya hauni da zagi iri-iri na cin mutunci wai ai da gangan na bige shi, har da cewa dama mu ƴan ƙauye bamu da ɗa'a, babu ilimin komai a tare damu sai jahilci, banda tsantsar jahilci me zai hanani kallon gabana