NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 89 of 223

a faɗa bayan ya gama duban takardar da ke ɗauke da lissafin adadin kuɗaɗen da suka shigo da kuma wanda aka ware za'a ƙara fitarwa wajen yin wata ordar, duk acikin watan kawai, fuskarsa sai fitar da murmushi take. Hajara Furnitures shi ne kantin da Kabir ya buɗe a tun watan farko na zuwansa ƙasar, da kyautar kuɗaɗen da ya samu daga wurin Bella da kuma kyautar gidan da suka bashi, a tahowarsu ne ya sayar da gidan naira miliyan ashirin da shida dan ba gidan banza bane duk da cewar flat house ne, to amma zubin ginin kaɗai zaka kalla ka sami tabbacin bada ƙaramar dukiya akayi ginin ba. shi a wurinsa zai riƙe kuɗinne dan buƙatun yau da kullum har ya kammala karatunsa, to sai bayan saukar tasu ne kuma ya sami saƙon check na wasu adadin ethopian birr daga wurin Bella, adadin kuɗin da idan ba ɓarnar banza zai yi dasu ba za su ishe shi gama rayuwarsa, yaji daɗin kuɗin sosai ya kuma ƙara jinjinawa mutumci da karamci irin na Bella, macen da bata manta alkhairin mutun a gareta ko mai ƙanƙantarsa. dan haka ne yaga da abu ɗaya ya dace da shi, wanda zai kankarowa kansa mutumci da ƙima shi ne ya gina kansa, ginin da ba shi kaɗai zai amfana ba, har na kusa da shi ma. Abdurrahim shi ne abokinsa da suka fara haɗuwa a lectures, kuma halinsu yazo ɗaya, shi ya wuce masa gaba wajen taya shi neman hayar shago, sannan ya ƙara wuce masa gaba ya kaishi inda aka bashi haske aka kuma wayar da shi da shigo da kaya daga ƙasashen waje. Furnitures ya fara zubawa a shagon, kamin wata uku ta rufa kuma tuni ya maida kuɗaɗen da ya zuba, bai fara komai ba sai da ya kira waya ya nemi albarka da adu'ar mahaifinsa da ya rage masa, ya sanar da Gwaggo ma, ya kuma sanar da Malaminsa, shi ma kuma adu'ar yake babu dare babu rana, da sadaƙa, da yin ƙiyamullaili a kowanne dare, saboda haka yake ta ganin bunƙasa ta yacca bai yi tsammani ba. bayan barinsu store ɗin kai tsaye Emirate of Harar(masarautar ethiopia) suka nufa, da zuwansa ya taki sa'ar da ya ke fatan samu, dan shi ne mutum na biyar a mutanen da akaiwa izinin shiga su sami ganawa da Sarki Abd Ash-Shakur. sai da ya ɗauki tsawon awa guda acikin fadar sarkin da ke ta amsar bayanai daga wasu makusanta shi kamin ya sami damar ganawa da sarkin ya sanar masa shi ɗin masoyinsa ne na haƙiƙa yazo ne na musamman dan miƙa masa gaisuwa, Abd Ash-Shakur yaji daɗi sosai dan har hoto sai da ya sa akayi musu tare, bai baro cikin fadar ba sai da akayi sallar juma'a tukunna. da fitowarsa kuma ya sami wani dogari da ya kwashe duk wani tarihi da ya kutsa acikin masarautar shekaru goma sha biyar da suka shuɗe har zuwa yau, yaji daɗin samun duk wasu bayanai daga bakinsa, irinsu ne ake jin daɗin samu a harkar bincike, dan sai sun feɗe maka biri da wutsiyarsa a duk abin da suka ji suka gani saboda tsabar iya gulma da sa ido. ba a haka kawai ya sanar masa da komai ba, aikin kuɗi yay masu yawa, shi yasa ko da ya kammala sai da ya ƙara tambayarsa idan yana buƙatar ƙarin wani abu na koma menene yasa shi ya nemo masa zai ji bayani. murmushi kawai Kabir yayi, ya gama samun abunda ya shigo da shi cikin masarautar, dan haka ya ɗauki hanyar fita a hanzarce, sam ba neman taimako yaje ba, ko kai ƙorafi ba kamar yanda ake kallon duk wanda ya shigo a wannan lokacin. acikin fadar ma sai da ya dinga ɓoye fuskarsa da p-cap gudun kar su haɗu da Suhail ko Jawad idan su na ƙasar, fitowar tasa daga ciki kuma yayi daidai da ƙarasowar Abdurrahim da ya kira ya sanar masa ya gama yazo su tafi. Abdurrahim ya so, kuma yana son ya san akan me yayi binciken da kuma dalilin yinsa, to amma a yanda ya gama lura Kabir baya so ya san komai duk da yarda da amincin da ke a tsakaninsu, saboda haka bai takura kansa akan sai ya tambaye shi yaji ba, may be it is a matter that belongs to him alone, and he does'nt want anyone to know. tunda Kabir ɗin ya shigo mota bai yi magana ba, haka idanunsa a rufe su ke har suka iso gida. duk da cewar Abdurrahim ɗin nata zuba zance amma sai ya lura Kabir ɗin yana sauraronsa ne Absentmindendly, dan haka yay shiru yana bin waƙar da ke tashi ta recorder ɗin motar cikin yarensu na Amharic. lokacin d suka isa gidanma Kabir ce yayi ya barshi a mota zai shigo daga baya, yaso ya matsa masa yaji akan meke faruwa dan yaga ƙyallin damuwa a ƙwayar idonsa, to tambayar ba a wannan lokacin ta dace ba, ya ɗan huce tukunna, kuma may be ya iya sanar masa ko da bai tambaya ba. Abdurrahim na fita a motar ya zaro waya daga aljihunsa ya lalubi nunbar Kulu, shin ya sanar mata kaso 50 na aikinta ya kammala ne ko ƙaƙa?, saƙa da warwara yake akan yin kiran, ya kira ko ya bari?, zuciyarsa ta rasa wanne side zata ɗauka, kiran na da muhimmanci ta wani ɓangaren, ta wani ɓangaren kuma ba shi da amfani. tun wancan ranar yake fushi da ita, fushin kuma da yay zuciyar ba zai ƙara kiranta ba sai dai idan ita ta kira shi. _"Ranka ya daɗe su din Ƴan biyu ne, su kaɗai Allah ya bawa mahafinsu, mahaifiyarsu ma ita kaɗai ce, nan ba shi ne ainihin gidansu ba, amma kuma sunyi rayuw
🏠