ayi haƙuri, Allah ya huci zuciyar Kabir ɗin Maryam".
Kabir ɗin ya ƙaraso wurin da ƙaramin table yake me zagaye da ƙananun kujeru guda biyu, ya zauna su na fuskantar juna yana kaiwa Abdurrahim ɗin naushin wasa a kafaɗa. shi ma yasa wuƙa ya yanki pizzar daidai wadda zata shiga bakinsa. "na gaji da irin wannan cimar ta isheni, abincinmu na gargajiya nake so, dan haka ka shirya gobe zaka fara cin abincin tamu ƙasar, zan mana tuwan dawa da miyar kuka me rai da lafiya, wanda idan kaci kaji garɗinsa sai ka damƙa min Atm card ɗinka kace kullum nake mana irinsa". Kabir ya faɗa yana kai pizzar bakinsa.
"Tuwon dawa! tun a sunan ma ba daɗi ina ga anzo ci, Abbu ya faɗa min san da yaje nigeria abincinsu babu daɗi sam, da niyyar sati guda yaje amma kwana ɗaya tal yaji ba zai iya ba...ko Mima ma da take ɗan zuwa da kayan abincinta take tafiya, dan haka ni ba zanci wani abincinkun ba gwara kake mana ordering kawai idanma ƙiwar girkin kake".
ya faɗa yana kai kofin juice bakinsa.
Kabir yace da shi, "aikuwa sai dai ka koma siyen abinci duk ranar girkina, dan wallahi a yanda nasa Gwaggo tai min aiken garin masara dana dawa da kuma daddawa, to Abdurrahim ka shiga uku da ganin abincin nigeria a idonka, sai dai idan banji yunwar ba...ni ba asararre bane da zanta saka kuɗina akan hanyar siyan abincin da ba ƙoshi nake dashi ba, dama ace irin girkin Leemars Mandi ne a ƙasar taku, to da sai nayita saya nasan duk inda naci plate ɗaya ya wadatar, kuɗina yanzu bana ciye-ciye bane, na ginin gida ne, gidan Maryam".
ya ƙarasa maganar fuskarsa na faɗaɗa da murmushi.
"A dai rage buri, dan rayuwa bata tafiya daidai da muradin zuciya, kai ta adu'a kawai".
Kabir yay masa wani kallo ta cikin reflection glass cup ɗin da ya kai bakinsa yace,"Abdurrahim ka rage baƙin ciki, na faɗa maka kuma shawara na ke baka".
dariya ta biyo baya a duka fuskokinsu, san da kuma suka sauya babin firar.
"Fahad yace an fasa yin lectures ɗin...so kaga sai muje ga tafiyarka, na tambayi wani neighbour ɗinmu ya shaida min ranar friday akan iya barin wasu tsirran mutane su shiga Emirate, Sarki yana bada lokacinsa wa baƙin mutane a wannan ranar, so mu tafi tun yanzu ƙila ka taki sa'arka a yau".
Kabir ya lashi leɓensa na ƙasa sannan yace,"kasan me?". "a'a sai ka faɗa". ya jingina zamansa ga kujerar yana sauke numfashi,"nazo ƙasar nanne da manufofi guda uku kamar yanda na faɗa maka a baya, karatuna, aikinyi da kuma binciken sirri da aka sani. kuma tun zuwana na ke a ƙagauce da na shiga cikin masarautar na samo bayan nan da ake so a sani. to amma kamar yanda ka faɗa cewar zan iya taka sa'a a yau, nima kuma nake jin kamar lokacin sanin komai yayi, sai nake jin faɗuwar gaba da fargaba".
"idan har babu rami to me ya kawo rami Kabir?, ai in dai binciken da zaka yi bana cutarwa bane to ka cire wannan daga ranka, go straight forward to your work, shi ne magana kawai".
Kabir ya buɗe lumsassun idanunsa ya sauke kan Abdurrahim yace,"thank you my friend for encouraging me on so many things...tashi mu fita".
su ka miƙe suka fita, sai da suka je wurin mota Abdurrahim ya shafa aljihunsa yana laluben key ɗin motar.
"wai jiya dana dawo ban baka key ba?". ya tambayi Kabir ɗin yana tsayawa da laluben. "bayan sai da nayi bacci ma ka dawo". ya bashi amsa.
"to Allah yasa ban yasar da shi ba, dan wallahi ko ɗazu dana duba ban ganshi ba, thats why i din't show you those files". "ka koma dai ka ƙara dubawa yana nan, wani wurin ka jefa shi".
Abdurrahim ɗin ya juya ya koma ciki, ya ɗauki wasu daƙiƙu kamin dawowarsa yana faɗa masa ashe a toilet ya barsu.
Kabir ke driving ɗin yayinda Abdurrahim ke zaune a kujerar me zaman banza, yana yi masa bayanin kan yanda su kai da Abbu(mahaifinsa) akan office ɗin da yake so ya fara zuwa. Kabir yace masa ai ya amsa kawai, ba zai ga alfanun hakan ba sai nan gaba, shi kuma gyaɗa kai yay godiya ga shawararsa.
a wani katafaren store da aka rubuta *HAJARA SHOPPING MALL* Kabir yay parking motar daga wurin da ya saba parking a duk san da ya shigo store ɗin, ya kashe motar suka fito suka nufa cikin store ɗin, store ne da ke shaƙe maƙil da kowanne irin abin buƙata, yana daga cikin store ɗin da a watanni biyu da suka wuce ya shiga sahun manyan shopping malls da akeji da su a ƙasar.
shigarsu ciki sun jima sosai, sai dai babu wani abu da suka siyo, dan ko da suka shiga ba wajen ɗaukan kayayyaki suka nufa ba, direct office ɗin Manager da ke acikin store ɗin suka shiga, kuma Managern bada kowa yay magana ba sai Kabir, Kabir ɗin da yay masa tambayoyi game da yanda ciniki ke tafiya a kwana uku da bai leƙo ba, Manager ya shaida masa nasarar nan dai da ake samu a kullum har yanzu ita ce, babu faɗuwa sai Continuancy da ke ta ƙara haɓɓaka, dan jiya ma ya fitar da lissafin kuɗi naira miliyan shida da suke saka ran haɗasu a wata biyu, sai gashi an haɗasu a kwana biyar kacal, ya ɗauko wani file a sanda yake sanar da Kabir ɗin haka ya miƙa masa gabansa.
"Alhamdulillah, Masha'Allah". Kabir y