aboda kewa, kewa kuma ta Maryam, Mairo ta ƙauyen bichi.
ya saki wani murmushi me tattare da tarin ma'anoni, bayyanuwar siririyar wushiryarsa a sanda yay murmushin sai wani kyawun na daban a tare da halittar tasa ya ƙara fita. tana son kyau, tana tsananin son kyawun da Ya Kabirunta yake shi, ya san da wannan, to wane kalar jin daɗi da farin ciki da murna zatayi a sanda fararan idanuwan nan nata masu kyau suka yi tozali da shi a KABIR ba a KABIRU ba?, ta kalle shi a irin yanda take ta hasaso shi a wata rayuwar ta daban, ba irin wadda suke ciki ba, rayuwa ta hutu da jin daɗi, rayuwar cikin birni bata ƙauye ba, rayuwar wayewa da gogewa, rayuwar da kuɗi suka zauna masa ajiki.
_"Ya Kabiru wai idan mutumin da ya haɗa nagarta da cikar kamala ya samu hutu da jin daɗi da kuma kwanciyar hankali, mutum dai irin wanda ba zai rasa wata ƴar mitsitsiyar matsala ba, me gogewa a fannin ilimin addini dana boko, to wai kyau yake yi irin me ɗaukar hankali, haka naji ana faɗa, to wai hakanne?."_ kalaman Mairo a wani lokaci can baya suka haska a kwanyar tunaninsa, a lokacin ya bata amsa ne da, _"ki cire wai ɗin, maganar haka take."_ ta ƙanƙame shi a sannan cikin murna tana cewa,_"Allah ya kai min kai wan nan matakin, matakin da kowa ne ya ganka zaiji ka burge shi...idan Yagana tayi tsawon rai ta tofe min kai da tofin Allah tsine saboda ƴan hasidin iza hasada"._ murmushi kawai yay mata a sannan bai ce komai ba, amma ayanzu zai ce wani abun, dole ma ya faɗi wani abu.
kamar kuma tana kusa da shi ne, kamar kuma da ita ɗin yake magana, kamar kuma tana sauraronsa ne, acikin muryar nan tasa me taushi da zurfi ya faɗa a fili ba a zuci ba,"Kabir ɗinki ya samu, ya samu wannan abun da kike masa fata, na cikin mafarkinki da kuma hasashenki, domin ya kusa kaiwa matakin, ƙiris ya rage, dan komai ya kammala, linta ɗaya ce tai saura acimma ginin, ita ma kuma lintar ba me tsayi ba, kwalin degree da shiga office ne kacal, ofishin nan da kika ce kujerar cikinsa zata ke juyawa dani, irin sanyin ɗakin Bella da ke fitowa daga inda ba'a sani ba yake sauka ajikina, jin daɗi da annashuwa da annuri su ke bayyana a tare dani...daga nan mafarkinki ya tabbata, ya gama tabbata Maryam".
yay shiru yana me tsuke baki, inda wannan pink lips ɗin nasa su kai wani kyau a tsukewar. zancen da ya gama a fili kuma ya koma na zuci da wata maganar ta daban. _a sa'ilin da nawa mafarkin kuma zai tabbata, lokacin da kika gama makaranta, lokacin zan bayyanar da manufata akanki ga su Baba, su aminta da sun bani ke. a ɗaura mana aure na ɗaukeki na kai ki gidana, mu tabbata abu ɗaya, rayuwarmu ta sauya, ta sauya zuwa ta ma'aurata, na daɗa killaceki a zuciyata kamar yanda na killaceki acikinta na tsawon shekaru goma, na fito da wannan ɓoyayyar ƙaunar dana ke ɓoyeta na nuna miki ita zahiran miraran, a lokacin zan koma miki tamkar yaro, zan zame miki tamkar ƙaramin yaro a sanda nake faɗa miki kalmar SO, irin son da muka cimma a yanzu ba irin na waccen lokacin ba...dan zan shayar da ke madarar so da ƙaunata, ki kasance a kwance a ƙirjina a duk san da muke tare, ki kasance goye a bayana a duk san da na dawo wurin aiki...Alƙawari, Alƙawari ne nai miki da duk irin tsarin gidan da kike so acikinsa za ki zauna._
sai dai me zai faru?, zuciyarsa ce yaji tayi wani irin duka da bai taɓa jin tayi ba, lokacin da yake tunanin ai ya rabu da duk wani challanges na rayuwa, ashe fa a lokacinne zai fuskanci babban ƙalubale mai girma, lokacin da al'umma za su shaida auren KABIR ADAM BICHI da MARYAM ADAM BICHI, ƙwayayen halittar da kowa yake da masaniyar cewa ciki kawai suka raba a wajen fitowa, Uwa daban-daban ta ƙyanƙyashesu, amma abun da aka zuba a samar da ƙwan halittar tasu na uba ɗaya ne, Uba ɗaya Malam Adamu Me Faskare, to wanne mahaukacinne zai karɓi waliccin wannan auren? kuma waɗanne mahaukatan ne zasu tsaya shaidar auren da za'a gina akan haramci?, bayan sarki Allah, sai shi, sannan Baba da Gwaggo da kuma ita Kulun da tayi sanadiyyar zuwan Maryam ɗin duniya, babu wani mahaluƙi da ya san Mairo ba ƴar gidan bace, ba ƴar Baba bace, ba kuma ƴar Gwaggo bace, ba kuma ta gadon komai a gidan...to ta ya shi da mahaifiyarta za su tsira daga hakan su cimma burinsu bayan basa son kowa ya san da SIRRIN ƁOYE?.
zancen zucin ya katse, walwalar fuskar kuma ta sauya, wata walƙiya ta gifta acikin idon nasa, sannan tsawa ta sauka a tsakiyar kansa duk a lokaci ɗaya, lokaci ɗaya da shigowar Abdurrahim cikin ɗakin, saboda haka ya* lumshe idonsa yayi kamar bai san da shigowar tasa ba, duk kuwa da sun haɗa ido ta cikin mirrow.
"Pizza nasa akayi order ba zan iya shiga kitchen ba, kazo muyi breakfast cikina ya fara ƙugi".
ya jisa, kuma Abdurrahim ɗinma ya san ya jisa amma yay kunnen uwar shegu da shi, sai dai ya zai yi da halin abokinsa kuma amininsa a halin yanzu?, haka zai ta binsa ta yanda ya sauya ɗin.
yasa fork ya yanki Pizza ɗin ya kai baki ya tauna, har sai da ya haɗiye sannan ya ƙara cewa da shi.
"fushi?, baka sakko ba kenan?, to k