NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 86 of 223

da duka hannayensa biyu ta bayan kansa, idanunsa a rufe, zararan gashin idon nan sun miƙe, in banda shi Abdurrahim ɗin da yasan halin abokinsa, kowaye ya ganshi a wannan yanayin ba zai ce ba bacci yake ba. yaja tsaki tare da ɗan ɗaga sautin muryarsa yana faɗin. "waƙa ɗaya! kullum baka da aikin sauraro sai na waƙa ɗaya. to ka miƙe haka kayi wanka lokaci na tafiya, you know very well Malamin nan ba shi da mutumci". ya sani, ya sani wannan tsakin na ƙorafi da ya zama ɗabi'ar abokin nasa a halin yanzu dole sai yayi shi, dan haka ya murmusa yana ƙara faɗin,"ni dai nace ka tashi, ka tashi kawai Malam. watanni nawa suka rage?, watanni shidda ne kacal suka rage ka koma hutu ka ganta, ka sata a gaba kana kallonta da sauraron muryarta ba waƙar da kake cika min kai da ita a kullum ba". shirunsa ya haɗe da buɗe idon Kabir ɗin ya saukesu tar a kansa, idon da ya rufesu tun a sanda sautin waƙar ya soma tashi, haka yake a duk san da ya kunna waƙar, waƙar tana tafiya ne da bugun zuciyarsa, yayin da hoton Maryam(Mairo) ke haskawa a idanun nasa. kallon Abdulrahim ɗin yake, kallo na ka taɓu, kana buƙatar ganin likita. "watanni shidda kace?, watanni shidda nan gaba da za'a haɗa su bada shekara guda da wata biyu, su zan ƙara kaiwa ban sakata a idona ba?, da wanne haƙurin?, daga ina juriyar tawa take?...ba ka da hankali, ba ka da hankali sam Abdurrahim, kaje kaga likita ya duba maka ƙwaƙwalwarka". Abdurrahim ɗin ya zauna akan sofa yana kallonsa yace,"ko makaho ya shafa tsakanin ni da kai zai faɗi wanda yafi cancanta da ganin likitan ƙwaƙwalwa Kabir, kai ka dace da ganin likita bani Abdurrahim Yusuf ba, saboda ni ban zauce ba kamar kai". a lokacin da Kabir ya miƙe yana sauke ƙafarsa a ƙasa, yake cewa da shi,"baho kawai, na tabbata da ace kana da wadda ta shiga zuciyarka tayi bake-bake ba zaka dinƙa yi min wannan shirmammun maganganun naka ba. har yanzu baka san SO ba, ji kake ana faɗansa, ana kuma aiwatar da shi a aikace, amma baka san daɗinsa da zafinsa a zuciya ba, baka sansa a gangar jiki ba, baka sansa a ruhi ba. dan haka idan ka ƙara furta min zancen zan ƙara wata shidda anan gaba ban koma ƙasata naga Maryam ba sai na daki bakinka ya fashe yayi jini, karka fasa kaci gaba, kaga yanda zanyi da kai acikin gidan nan da muke rayuwa mu biyu". ya san hakan zata kasance, masifa!, wannan faɗan nasa sai yayi shi, ba a haka Kabir yazo ƙasarsu ba, a me haƙuri yazo, amma yanzu SO yasa ya tashi daga Kabir ɗin da ya sani tun wasu satika na fara rayuwarsu a makaranta tare, ya rikiɗe ya koma wani Kabir ɗin na daban, zautacce wanda ya haukace akan soyayya, soyayyar da yake ganin kamar ta kusa yi masa illa. gajeran murmushi me sauti ya tsaya a iyaka leɓen Abdurrahim ɗin a sanda Kabir yay shiru da maganarsa, sautin murmushin da ya sa Kabir ɗin dakatawa daga tafiyar da yake zai wuce bedroom, ya juyo ya kalle shi, kuma wannan karanma a zafafe ya shiga magana kamar zai rufe Abdurrahim ɗin da duka. "banda kuɗin jirgin komawa shi kake wa dariya right?". Abdurrahim ya ɗago da kansa daga barin danna wayar da yake ya kalle shi, tabbas Kabir ya haukace da gaske ba wai a faɗa ba, banda ya haukace a yaushe yaji yayi dariya, murmushi fa kawai yayi. "to daɗin abin dana zo ƙasar taku ba zaman banza nake yi ba, ina karatuna ina kuma sana'ata, kai ka sani, kuma shaida ne, ka kuma san ayanzu zan iya biyawa kaina kuɗin jirgi kaima kuma na biya maka. ofcourse ni ɗan ƙauyen Bichi ne, amma idan ka tashi rubutu a sabon update list naka na bin ƙwaƙwaf ka rubuta KABIR ADAM BICHI a sahun farko na masu kuɗin garin bichi, labarin baya daban, na yanzu ne ke tafiya, kuma ita ake magana, ka san da wan nan, ka kuma bawa wani labari". yana gama maganar ya juya a fusace ya wuce bedroom, Abdurrahim kuma yabi bayansa da ido yana dariya, yana ba shi dariya idan yana wannan masifar, duk da cewar yana bashi tsoro a wasu lokutan saboda yanda idanuwansa ke sauya launi daga asalinsu, to amma shi wallahi a yanzu Kabir ɗin ya zame masa comedian. gemunsa nan dai me ɗan tsayi shi yake tajewa kamar yanda ya saba ko da yaushe a ƙarshen shirinsa. ɗinkin habesha kemise ne ajikinsa, farar riga da akayi aikin jiki da baƙin zare, da kuma ratsin golden, red and blue, sai baƙin wandon plane yadi me kauri, ɗinkin ƴan ethopia ne, shigar da tun ranar da ya fara yinta yawanci idan suka ganshi sai suce dama shi asalin ɗan ƙasar ne, ba da kayan kaɗai ba, hatta ga zubin halittarsa ma. ya ajiye ƙaramin cumb ɗin san da ya gama tazar, abu na ƙarshe da ya ɗauko ya saka ayau baƙin glass nasa me O shape, hannaye zube cikin aljihun wandon ya tsaya yana kallon kansa a madubi. Yayi kyau, irin kyan da ke haska ƙyalli a idon me kallo, ya fito a cikakken ɗan gayun birni ba ɗan ƙauye mazaunin can ba. ya ƙara haske akan asalin wanda yake da shi, sumar kansa me zubin ta buzaye ta ƙara cika da baƙi, siririn hancinsa ya ƙara tsayi, sai wannan doguwa kuma siririyar fuskar tasa da ta rame, ramin idon ya faɗa ciki, duk a s
🏠