NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 85 of 223

u yazo ne zai ce musu Kabiru yana gaishesu sannan ya haɗa su. ajiyar zuciya ta sauke ta fito daga kitchen ɗin, sai taga kamar giftawar mutum dan haka tayi saurin nufar hanyar banɗaki, daga wajen banɗaki kana hango ƙofar ɗakin Gwaggo, mutum ta gani ya shiga ɗakin, babu jimawa kuma aka fito, ba zata ce waye ba, ko wanda take tunani, tun da lulluɓe yake da babban zani hatta kansa baka gani. to waye?, ta fara tsorata fa! wancan satinma ta tashi sallar dare ta shiga uwar ɗaki, fitowar da zata yi taga kamar mutum ya laɓe a bayan ƙofa, saboda sallar da zata yi sai batabi takan ta duba ba, dan lokacin gab ake da ai kiran farko, kasancewar bata farka da wuri ba, kuma tana cikin sallar zata tafi sujjada sai inuwar mutum ta gani ta fita, abun ya ɗaure mata kai a sanda ta sallame tana dube-dube bata ga komai ba. sai ta barshi a cewar idonta ne ya haska mata hakan, gizou kawai take gani, shaiɗanne ke so ya sanya mata wasi wasi, ai dama taji wani Malami ya faɗi hakan, idan shaiɗan ba ya so kayi ibadar cikin dare sai ya dinga sanya maka tsoro. to amma ayau dai tabbas mutum ɗin ta gani, idonta ba gizo yake ba, kuma koma wane shi ɗin me cutarwa ne, gabanta ya faɗi, tai ɗakin da gudu, tana zuwa ta ƙaro hasken fitila, a sa'ilin ta ƙara ganin inuwar mutum ta gimla ta jikin labule, ba so take ta san wannan ba, lafiyar Gwaggo, dan haka tayi kan Gwaggo da sauri tana taɓata har ta farka, Gwaggo ta bita da ido ganin duk ta rikice, kuma yanda take dudduba jikinta kamar me neman wani abu. Gwaggo ta farka tace, "Hauwa lafiya?". "kina jin wani abune ajikinki?". ita ma ta jefa mata tata tambayar ba tare da ta amsa tata ba. "babu abun da nake ji, wai menene hala?". Kulu ta haɗiyi wani yawu a maƙoshi tana aikin sauke numfashi da sauri sauri. "kuma da kina bacci ba ki ji wani abu ya taɓaki ba?". "ke ko dai mafarki kika yi ne da ya tsorata ki kika tashi a hargitse haka?". bata so ta ɗaga mata hankali, dan haka dole ta ɓoye mata ainihin abunda ta gani, kuma idanma tace zata faɗi hakan babu mai yarda da ita don babu hujja. "mafarki nayi mara daɗi, kiyi haƙuri na tasheki". Gwaggo kallonta take da rashin yardar abun da ta faɗa, tace, "fuskarki bata bani tabbacin abunda kika faɗa ba Hauwa, gaya min gaskiya". "babu komai fa Yaya, ance ba'a son faɗar mummunan mafarki". a yanda take maganar a tsorace da kuma nuna rashin gaskiya sai tayi mata sak Mairo. kai ta gyaɗa,"to Allah ya sauya shi ya koma mai kyau...kinyi sallah ne?". "a'a, yanzu dai zanyi". "to kiyi adua sosai, ni bana jin ma zan iya yi saboda ƙafata tana min zafi, kamar ana caccaka allura nake ji". Kulu ta tsareta da ido,"to ko kiyi sallar ƙila ta daina ciwon". "ba zan iya ba, ki dai ƙara shafa min maganin da Aminu ya siyo, dan naji daɗinsa ɗazu, har na kwanta ba irin tsamin nan da take yi". hannu na rawa Kulu ta ɗauko maganin, ta kwalɓato shi sai da ta kusan juye mata rabi sannan ta bari, saboda taji Zannira tace maganin da tsada ɗari takwas aka siyo. bayan ta idar da sallah ta jima zaune akan sallaya, hankalinta ya karkata gaba ɗaya kan mutumin da ta gani a ɗazu, waye?, waye?, so take tasan waye?, macece ko kuma namiji?, daga ina yake?, tana da tabbacin koma wanene Gwaggo yake son cutarwa, ai na zata ganshi ta faɗa masa da kakkausar murya matsawar tana tare da Gwaggo yayi kaɗan ya cutar da ita, saboda haka ya sake sheƙa, ba anan ba, ba anan inda take tare da ita ba, cutarwarsa ba za tayi tasiri akan Gwaggo ba.       Please vote again and again and again. *Comment,Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *25)* *Kirkos, Legacy Luxury apartment Addis Ababa, Ethiopia.* *06:30Am.* _Here in silence i wait, there's nothing else i can do, it feels like my heart gonna break, and all i can think of is you, and how many aching arms long to hold you, and show you how much i care, but i'm counting the hours without you, and i dont know how much i can bear, becouse i miss you morethan words can says, and i need you hear in my life always, yeah i miss you._ sautin waƙar i miss you ta Beverley Craven ce ke tashi a hankali acikin madaidaicin living room ɗin, waƙar da ke tafiya haɗe da bugun zuciyarsa, kuma a dai-dai lokacin da kalaman waƙar su ka ɗan tsaya, a dai-dai lokacin ne Abdurrahim ya kashe laptop ɗin da waƙar ke tashi daga ciki, hannunsa ɗauke da ƙaramin towel na wanka yana goge ruwan da ke sumar kansa, yaja tsaki a lokaci ɗaya. yaci gaba da tsayuwa a kusa da center table, ya ƙarasa sharce sauran ruwan da ya rage a sumar tasa, sannan ya tsaida kallonsa akan Kabiru, wanda ke miƙe akan sofa bed yayi matashi
🏠