NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 84 of 223

ke bin su kuma bata fasa binta ba, bata sauya ba, sai ma tarihi da take ganin kamar zai maimaita kansa, a tunaninta haɗuwarta da su Gwaggo rayuwar zata dai-daita ko da ba kamar a baya ba, ƙaddarar ta sauya kuma ta tsaya, to amma me?! shekara goma sha biyar, sai rayuwar take nema ta koma irin ta farko. shekaru goma sha bakwai su a rayuwarsu ta duniya su ka fara kallon ƙaddara, ƙaddarar da ta fara binsu a ko da yaushe tana bin takunsu, tun su na guje mata har ta kamasu ita da ƴar'uwarta, ƴar'uwarta da suka zo a mahaifa ɗaya, Hassanarta, Hassanarta wacce su ka zo duniya tare. ashe dai da gaske ne rayuwa bata taɓa biyewa muradin zuciya, a baya bata yarda da hakan ba, amma a yanzu ta yarda da hakan, ta kuma gasgata, dan hakan ta faru da su ita da Hassanarta, sam rayuwa bata biyewa muradin zuciyarsu ba. tunanin da Kulu ke yi ya katse sakamakon wayar da ke jikinta ta shiga Vibration, tayi sauri ta jawo wayar daga jikin zaninta da ta soke gudan kar Gwaggo taji ta farka, ta damƙeta a hannu sannan a hankali kuma ta sakko daga gadon ta fita tsakar gida, cikin sanɗa ta ƙarasa ɗakin girki ta ɗaga wayar san da kira na biyu da ya shigo ke ƙoƙarin yankewa. "Kabir". ta kira sunan nasa a hankali, bai amsa ba sai da ta ƙara maimaita sunan,"Kabir". sannan ya amsa. "ina jinki fa". ta sauke numfashi,"to ya kake ya wajen na ku?". "muna lafiya". muryar Kabiru na fita ne da sautin fushi, ta san fushin yake tun daga yanda yake bata short amsa. shiru daga shi har ita babu wanda yay magana sai can ta katse shirun da faɗin,"har yanzu baka sami shiga cikin masarautar ba?". yay gajeren murmushin da ta jiyo sautinsa,"Har yanzu kema ba ki nemi dabarar da za kiyi ki saka min muryar Maryam naji a kunnena ba?". ya tari numfashinta, "ai na faɗa miki ba, its a deal cewa ba zan ƙara ba ki wani information ba har sai kin jiyar da kunnuwana muryar da take son ji". "to ai yanzu bacci take". ya ɗan daga sautin murya kamar wanda zai yi faɗa yace,"kullum abun da kike ce min kenan, bata nan, tayi bacci, zancen kenan kullum. ina so naji muryarta amma kun hanani, duk ranar da na kira kowa da uzurin da yake bani tsakanin ke da Amadu, shi zai ce min idan yazo gida zai haɗani da ita, amma sai dai naji batun yazo ya koma, ke kuma da dabara kawai za kiyi ba wai ki bata wayar ba amma kin gagara, ance Mu'azzam na da waya kun hanani lambarsa...ƙwarau na fara tantama da wannan yawo da hankalin da kuke min tsawon wata takwas, Amadu ba ya saɓa maganar da mu kai da shi, ku daina ɓoye min ku faɗa min gaskiya idan Baba ya aurar da ita ne". ba wai dan ya gama magar da yake ba, ta katse shi da faɗin,"ko ɗaya ba haka bane, ba'a aurar da Hussaina ba, ai na maka alƙawarin taka ce, ta ya zan yarda a gaban idona a bawa wani ita?, Kabir zan yarda Sirrin da ke ɓoye tsawon shekaru ya bayyana, amma ba dai ka rasa Ƴata ba". daga in da yake ya wani zuƙi numfashi idanuwansa a rufe, tabbas nema yake ya manta da wadda yake magana, dan ɗaga murya sama yay yana magana a zafafe,"kin san kuwa irin zafin da zuciyata ke min?, kin san irin yanda kunnuwana ke bala'in son jin muryarta?, kin san yanda idanuwana ke kewar ganinta?, kuka nake kullum, kuka bana fili ba na zuciya saboda tsananin kewa, kewa ta Maryam. duk safiya, duk rana, duk dare, duk baccina, wannan harufan guda ashirin da shidda da suka bada kalmomi bakwai da suka fita daga bakinta zuwa gareni amsakuwa su ke a kunnena, _Ya Kabiru dan Allah ka tafi dani._, kin san yanda naji a lokacin?, idona sai da ya cika da ruwa, bugun zuciyata sai da ya sauya, haƙiƙa a lokacin ban da Sirrin da ke Ɓoye babu abun da zai min shamaki da kama hannun abata na tafi da ita...har yau idanuna hoton wannan lokacin da takeyi kukan tafiyata ne ke haskawa acikinsu, kunnuwana kuma amon sautin kukanta ne aciki". Yay shiru, yay ƙasa da murya, muryar da ta raunana, muryarsan nan mai taushi, ta koma tamkar ta ƙaramin yaron da ke tsananin buƙatar ai masa abu, ta tabbata a wannan lokacin tsugune ya ke akan gwiwoyinsa, kuma zata iya rantsewa hawaye yake yi. "don Allah, don girman Allah ki taimaka min, ki taimakawa kunnawa da saka musu muryar Maryam a san da take cikin farinciki, ki kuma goge min hoton Kukanta da ke haskawa a idona, na koma ganin fuskarta a san da take murmushin nan nata mai sanyi, ki min hakan tun kamin zuciyata ta taɓu...don Allah, don Allah, na roƙeƙi nima ki taimaka min kamar yanda na ke taimaka miki akan halin da ahalinki su ke ciki...wallahi tallahi ina son Maryam, ina sonta, ina sonta da dukkan gangar jiki da ruhi, karki hanani ƴarki don Allah ki cika min alƙawari".  ɗiff ya kashe wayar, tabi screen ɗin wayar da kallo, ya zata yi?, ya zata yi ta sanar da Kabiru cewar Mairo ta ɓata ba'a ganta ba?, ba zata iya ba, ba zata iya wannan kasassaɓar ba, haka kawai! iyayensa da ƴan uwansa sun ɓoye masa sai ita ce zata sanar masa. har yau bai san da ɓatan Mairo ba, domin Baba yace kar wanda yayi gangancin faɗa masa, duk da da ma ba samun damar wayar suke da shi ba akai akai, sai idan Amad
🏠