n yanzu, akwai abinci wadatacce dan hatta gidan kansa ma gyara shi ake yi, shi da Amadu su kai haɗakar kuɗi akayi facefacen inda ya lalace, dan kowanne ɗaki yanzu da fenti, gidan ya koma kamar ba shi ba, banɗaki ma kansa shi Aminun yasa an maida masan zamani.
"shigo mana Zannira". Gwaggo tace, da ike har a wannan halin Gwaggo dai bata bari Kulu ta nuna tana magana ba, duk da taso yin hakan a san da wani Malami yace da wuya Gwaggo ta kuma takawa da ƙafarta sai dai wani ikon Allah, to Gwaggonce ta hanata da ce mata da hakan kaɗai za ki biyani da abunda nayi miki.
"Gwaggo sannu da jiki". Zanniran ta faɗa tana zama. "Yauwa Zannira sannunmu dai, ya ɗawainiyarku to Allah ubangiji yay muku albarka, an gode Allah ya ƙara arziƙi". "Amin ya Allah Gwaggo, kema kuma Allah ya ba ki lafiya". ta faɗa tana duban Kulu tace,"sannu Kulu kina ƙoƙari kema mun gode Allah ya ba ki lada ya kuma ba ki lafiya". Kulu dai kallonta tayi tai murmushi kawai.
"Gwaggo da ma ganda ce yazo da ita, to yayi niyyar kawo miki da kansa kuma sai Baba ya kira shi yaje masallaci ya same shi, shi ne yace na kawo miki, idan bai yi dare ba zai shigo". ta faɗa tana buɗe kwanon tana saka cokali aciki ta miƙawa Gwaggon. "Allah dai yayi muku albarka". Zannira ta buɗe jaka ta ciro magani a ƴar kwalaba shi ma tace,"magani yaji wani malami ya faɗa a radio shi ne ya taho da shi, Malamin yace za a dinga shafa shi lokaci zuwa lokaci insha'Allahu za'a dace". ta buɗe ta lakuto tana fara shafa mata.
Amarya ta shigo ita ma hannu ɗauke da kwanon abinci, ta ƙaraso tana faɗin,"ai ni nayi zatonma ko bacci ku kai da naji Zannira nata kwaɗa sallama, ni kuma ina banɗaki a sa'ilin".
Gwaggo da ke ta ƙarfin halin magana tace,"gyangyaɗin dai muka fara, ban ma san Kulu ita ma ta kwanta ba".
"to ga abincin, tuwon semovita ne da kuɓewa ɗanya". Gwaggo tace,"ai na kuma kika sami semovita?". Amarya na murmushi tace,"ai biki ji daɗinsa da naji ba, kuma wallahi musamman danke na tuƙa shi tunda lokacin da muka je gidan Gwarzo naga kinyi santinsa. a kayan da Amadu yayo aike jiya ya sako, bamu lura da shi ba ma duka sai da Zulai take ɗiban wake take ce min laa kinga ashe Amadu har da semo ya haɗo".
"amma kuwa Allah yaywa yaron nan albarka. mu dai mun zama ƴan gata yara nata samun buɗi". cewar Gwaggo.
"ai dama ance komai lokaci ne, Allah dai ya ƙara sanya albarka a cikin dukkan lamiransu".
Zulai ta shigo ita da Sadiya da aka tsaida bikinta jiya watan mauludi. tun daga bakin ƙofa Sadiya ta hango gandar da ke gaban Gwaggo cikin kwano, ta ƙaraso ciki tana cewa,"Allah ya kawoni a sa'a, ke dai Gwaggo ubangiji ya ƙara miki lafiya". tai maganar tana zama tasa hannu ta ciro nama ɗaya ta kai baki.
"ɗakinki na leƙa ai ba kya nan". cewar Zulai ga Amarya. "kuma fa shigowata kenan".inji Amarya.
"hala kin manta zamu shiga gaisuwar gidan Hajiya Fatsima, ɗazu ma saida Yagana tayo aiken tuni, tace maƙota na ta shiga mu muna ɗinke a gida babu wacce ta leƙa, to tace dai kar mu wuce daren nan ba muje ba".
"bari na ɗauko gyale na, da ma tunani na Gwaggo, ba'a fita a barta ita kaɗai ba, to tunda Zannira ta shigo shikenan sai mu tafi...ni wannan ƴar ƙaniyar ma ai ban san ta dawo ba". Amarya ta ƙarasa maganar da kaiwa Sadiya duka da ƙafa da ke ta kai lomar nama baki.
Gwaggo tace da Zulai,"wato dai da gaske Adawiyya take ta koma gidan Yagana, yaufa gaba ɗaya ban sata a idona ba, to wallah kice mata ta dawo inba so take kuma na ƙarasa ba, ina zan iya zama babu Mairo ita ma kuma babu ita".
Zulai na gyara zaman mayafi tace,"ai sai dai ki aika Saleh ga shi can a tsakar gida, idan taji saƙon daga bakinki tafi ɗaukansa da muhimmanci...ɗa zu ƙememai tazo tayi dakan yaji babu kowa a gidan amma ƙi tayi, sai ma ɗan aiken da tacewa a faɗa mana Baba Mujibu ya bada garin kunu ta shiga banɗaki awakin Yagana sunbi ta kansa".
Saleh yay caraf ya amshe da faɗin,"ce tayi ma ba zata dawo ba sai ta gama hukunta awakin, yanzu ma dana baro gidan sai yi suke da Yaganar wai Adawiyya ta kar ya mata ƙafar tinkiya".
duk akai dariya. kuma daidai lokacin Malam ya leƙo ɗakin, suka haɗa baki wajen yi masa sannu da zuwa. "ba ku tafi gidan gaisuwar ba?". Zulai tace,"tafiyar zamu yi". yace,"to kuma zaman me kuke yi bayan kun san dare ne, za ku haƙura yanzu ku jira safiya". Amarya tayi saurin amsawa,"rufa mana asiri da faɗan Yagana". ta dubi Zannira tace,"ki shirya gobe kema Sadiya ta rakaki kiyi musu gaisuwa, mijin gidanne ya rasu".
sannan suka fita. haka suke yanzu a ɗakin Gwaggo ake yini jiddan walahairan, aita hira ana shafta saboda su ɗebe mata kewa, kuma hakan kanyi tasiri wataran.
*ƙarfe biyu da rabi na dare.*
Kulu ce a kwance kusa da Gwaggo, ba bacci take ba, a kwance take kawai, tana tunanin rayuwarta, tana tunanin irin yadda rayuwa ke gara mata.
*ZANEN ƘADDARA,* gani take kamar rayuwarta ce kaɗai mai ɗauke da *ZANEN ƘADDARA,* rayuwarta na haskawa ne da ƙaddarori mabanbanta tun a san da su ka shiga shekara goma sha bakwai a duniya, ƙaddara