NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 82 of 223

atsalar". Kulun ta faɗa sa'ilin da ta miƙa kofin ga bakin Gwaggon, a gefe ɗaya kuma tana saka hannu ta goge hawayenta, Allah ya sani rashin lafiyar ta Gwaggo shi ne dalilin da ya hanata bin sahun ƴarta, duk kuwa da bata san inda take ba, to amma ai tana zaune a gidan saboda rufin asirin ƴarta ya rufu, yanzu kuma da babu ita mene amfani zaman?, zata tafi ne kawai, tayi rayuwar da take ganin ita ce mafita a gareta. "Hauwa bakina ba shi da wani ɗanɗano, duk abun da ku ka bani ina ƙarfin halin cinsa ɗura ne kawai ku ke min, an riga anzo gaɓar da ba zan iya ƙara saka komai a bakina ba". kuka takeyi tayi maganar, ta kamo hannun Kulun ta riƙe tana ci gaba da cewa, "Hauwa ki yafe min, ki yafe min dan girman Allah, ban cika alƙawarin dana ɗaukar miki ba, na ci amanarki, ban san wannan ranar zata zo ba, ban san da zuwanta ba, da ban ɗaukar miki alƙawarin da na saɓa ba, da ban ɗaukar miki alƙawarin zan kula miki da Maryam ba kamar ƴar dana haifa a cikina, da ban ɗaukar miki alƙawarin zanga rayuwarta ta inganta ba, da ban ɗaukar miki alƙawarin halin ƙuncin da kike gudun zata shiga ba ba zan bari ta shige shi ba, da banyi miki alƙawarin Malam zai riƙe ta ba, zai mata riƙon da uba ke yiwa ƴarsa ba. yanzu Maryam ta ɓata, ban san a wanne hali take ciki ba, da ace gawarta na gani da nafi samun lafiya da kwanciyar hankali, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". da ita da Kulun sai aka rasa wane zai taushi wani ya bar kukan, Kuka suke sosai, kukan da idan ka gansu kai ma sai ka zubar da hawaye. sai can ne Kulu tayi nisa tace,"haƙiƙa har mutuwa ba zan taɓa mantawa da ke da alkhairanki ba, bani da bakin yi miki godiya, alaƙawari ɗaya!, alƙawarin nan guda da na ɗauka nayi miki adua a koda yaushe zan cika shi har ranar da ƙasa zata cika min baki...Yaya ki daina ɗorawa kanki laifin ɓatan Hussaina dan Allah, ba kece sila ba kuma ba kece sanadi ba, ƙaddara ce, ƙaddararta ce, Allah ya shirya hakan tuntuni, Allah ya rubuta a lauhul mahfuz hakan zata faru da ita, ko kaɗan bana ganin laifinki, kuma hakan ba zai sa na ƙulle ciki ba, ba ki sanni ba, ba ki san wace ni ba, ba ki san daga inda na fito ba, kuma tsawon shekara goma sha biyar ba ki taɓa tambayata daga wanne ahali nake ba, taimakona kawai ki kai, taimakona kawai kike da kyakykyawar zuciyarki wacce babu tsatsa acikinta, ba ki taɓa goranta min ba, ba ki taɓa hantarata ba, ba ki taɓa ƙyamatata ba, sai ganin kin ƙara ɓoye sirrin da ke lulluɓe dani, abunda ko jinina ba zai iya min ba...ni kaina zanfi farinciki da samun natsuwar zuciya da ta ruhi da ace gawar Hussaina na gani, domin bana so tarihi ya maimaita kansa...". kukan da ya ci ƙarfinta a wannan lokacin shi yasa ta yin shiru. "mutuwa zanyi, mutuwa zanyi Hauwa, ina jin ajikina lokacina yayi, ƙarshen rayuwata yazo, domin Allah yaji ya gani zuciyata ba zata taɓa iya ci gaba da ɗaukan rashin Maryam a kusa dani ba, ina sonta, ina tsananin ƙaunarta fiye da Basma, ji na ke ajiki da ruhina tamkar ni nayi naƙudarta bake ba, Ya Allah ka dubemu, ubangiji ka dubi halin da muke ciki, ya zuljalalu ka kawo mana ɗauki, Allah kai kasan komai, kai kasan abunda ke faruwa da wanda zai kasance, ya Rahmanu ka sauya wannan ƙaddarar, Allah a duk in da Maryam take ka kula da rayuwarta". ta kalli Kulu da hawaye ya gama wanke mata fuska tace, "idan na mutu ki bar gidan nan kar ki zauna, kuma dan Allah kar ki dawo cikinsa, kiyi nesa da shi kiyi nesa da abunda zai sa ki tuna shi, ina ji ajikina kamar Maryam zata dawo wataran, Allah zai kuɓutar da ita, a wannan lokacin kuma da zata yi rashina na san ba za ki juri ganin halin da zata shiga ba, ni kuma bana so, bana so tayi wani kukan da ya fi na mutuwata ciwo...kiyi min wannan alfarmar Hauwa". Sallamar da ake ta kwaɗawa daga ƙofar ɗaki tasa suka yi shiru, Kulu ta shiga goge hawayen nata da na Gwaggo, Zannira ce matar Aminu da akayi auren sati uku da suka wuce, ƙanin Kabiru ne da su ke ciki guda, wanda yake zaune acan Lokoja yana bugabugar kasuwanci tsawon shekaru uku, ana tsaka da alhinin ɓatan Mairo ya dawo kamar wanda aka aikawa da saƙon ɓatan nata, ya tafi can Lokoja ɗinne ba tare da ya san kowa ba, sai kuma Allah ya haɗa shi da uban gida na gari, mutumin da ba ya da ƙyashi, ya samu ya nuna masa kasuwanci har Allah ya buɗa masa bayan yanke tsammani da Aminun ya farayi, Allah ya saka masa albarka ya fara samun abin hannunsa, dan ɗan ƙaramin shagon da ya buɗe acan Lokoja ɗin na sayar da kayan electronics nasa ne wanda ya mallaka bayan sun haɗa hannun jari da uban gidan nasa, da ya ga samun nasa yana faɗaɗa sai ya sayar da shagon ya dawo gida,  ya kuma buɗe sabon shago anan kasuwar singa ta cikin garin kano, kuma da ike da albarkar iyaye sai shagon nasa ayanzu ya daɗa bunƙasa fiye dana lokacin da yake can Lokoja, domin dai-dai gwargwado yana samu. a yanzu haka ya ɗaukewa Baba duk wani abincin da za'a ci a gida, daman kuma Ahmadu yana aikowa da kuɗin abinci duk wata, wannan yasa babu matsalar abinci a gidansu Mairo a hali
🏠