ai da fuska ta kamo hannun Innar, ta soma hawaye tana faɗin,"Allah Inna da gaske nake ina sonsa, kuma wallahi idan ya auri Mairo zan iya kashe kaina, dan zuciyata ba zata juri ganinsu tare ba...Inna ni ina faɗa miki ma yanzu na tsani Mairo dan ashe tuni gonata take shiga ban sani ba, wallahi da nasan hanyar da zanbi na kawar da ita Allah sai nabi". kuka take sosai a san da tayi maganar.
Innar ta tsaya tana dubanta tsawon lokaci, Adawiyya ta san wace mahaifiyarta, dole zata nema musu mafita. Innar ta saki murmushi me cike da tarin ma'anoni tace,"ke ni fa ba shashashar uwa bace da zan zuba ido Mairo ta auri jinin sarauta, nawa Ƴaƴan kuma su ƙare a auren ɗan ƙauye gidan manomi. saboda haka ki share hawayenki ki bar kuka, asiri gaskiya ne, dan haka in dai akwai boka a duniya Yaron nan sai ya bar kan Mairo ya dawo kanki, in ba haka ba kuwa to ya zo da batun auren nata sai ta aure shin na gani, ai sai dai idan bana numfashi, ko kuma ke da ita ɗin duk ku rasa. ba Mairo kaɗai ba har Uwarta wallahi sai sun shiga tsumin wahala, kamar yanda na aika Hajiya lahira to suma tasu rayuwar a tafin hannuna take, ƙiris na ke jira, kuma lokaci yayi, nayi alƙawarin ko zanyi yawo tsirara sai nasa Rayuwar Mairo ta ƙare a tangaliliya.
can dama kece mara wayon, kin nane a gindinsu kina nuna min Uwarta ita ce me ƙaunarki bani dana haifeki ba, na sha faɗa miki ba ƙaunarki suke ba amma yarinyar sai kika yi sautin mahaukaciya da ni, to ai gashi nan ta nemawa ƴartata miji me ido da kwalli ke za su barki a gidan ɗan dako. to wallahi ko da ace ba kya sonsa ba zan bari aurenta da shi ya tabbata ba". Adawiyyan ta kuma fashewa da kuka,"ni dai Inna kiyi duk yanda za ki ki tarwatsa sonta daga zuciyarsa, dan wallahi a yanda na gama fahimtarsa aurenta yake so yayi, ranar ma fa da suka kwana agidan nan ina jinsa yana cewa da Ƙaninsa yaga Matar aure a gidan nan, to na rantse miki da Allah Inna in har baki nema min mafita ba zan kashe kaina, kisa Suhail ya bar kanta ya dawo kaina". Zulai ta kuma dafa kanta, tai ƙasa da murya tana ce mata,"ke na fa ce miki ki bar zubar da hawayenki a banza a wofi, zan tabbatar miki da Suhail ke zai aura ba waccan abar kamar sillan kara ba, yanayin jikinki shi ya dace da gidan hutu, matar manya, na faɗa in dai da boka to hawayenki daga yau ya daina zuba. Suhail zai dawo sonki kuma zai aureki, sannan zan yi amfani da basirata da hikimata wajen ganin na tarwats...". bata ida abun da zata faɗa ba Amadu ya ɗaga labulen ɗakin ya shigo, hakan yasa su kai shiru aka ɗora da wani babin zancen na cewar Kanta ke ciwo, saboda Amadu ya tambayi dalilin kukan nata.
kuma da suka dawo ɗin, Innar tata ta bata labarin bayan tafiyarsu makaranta ko wata biyu ba'a shafe ba Suhail yazo da kansa har ƙofar gida yasa ai masa sallama da ita Adawiyyar, an kuma shaida masa ɓatan Mairo amma ko jaje bai shigo yaywa Uwarta ba, tun da akace masa ai kina makaranta ya koma mota ya bar unguwar.
tayi dariya ta rungumo Uwar tace,"ai yaje har makarantar ya sameni, wallahi Inna a ranar ji nayi kamar nayi hauka don daɗi, ya shaida min yana sona, kuma da zarar na kammala makaranta zai aureni...Inna ranar ban iya bacci ba, yace saboda ni fa ya baro ƙasar Ethopia a lokacin da bai shirya hakan ba, saboda yadda idanuwansa ke masa zugi da zafin son su yi tozali dani".
tunanin Adawiyya ya yanke lokacin da Maganar Yagana ta shiga kunnenta. "ke zan leƙa gidan Hajiya Fatsima, yanzu zan dawo. idan kin gama tankaɗen garin sai ki tafi da shi can gida ki bawa Aisha, kice musu Mujibu ne ya siyo gari yace ai sadaƙar kunu da shi ranar juma'a". ta amsa mata da,"to". Yaganar kuma ta fice, ita kuma ta ɗauki aniyar Garin Kunun nan sai dai ayi asararsa, so take yanda ta manta da duniyar Mairo kowa ma ya manta da ita, dan haka ba zata bari ai sadaƙar nan ba, taga nema su ke su jaza mata bala'i Allah ya amsa adu'arsu ya dawo da Mairo, bayan ta gama sawa a ranta Mairo ta tafi kenan tafiya kuma ta har abada.
a ɓangaren Gwaggo kuwa tun wannan rana da Mairo ta ɓata ta ke a kwance babu lafiya har yau, ciwon hawan jini, kullum kuma ƙara hawa yake ba ya sauka saboda yawan tunanin halin da Mairo ta ke ciki, ta rame sosai sai kace ba Gwaggo da ke da jikin diri ba, wuyan nan nata ya zama dogo, kuma tun daga wannan rana har iyau bata kuma takawa da ƙafafunta ba, ciwon da ya tsorata Malam ya kuma ɗaga hankalinsa, ciwon ƙafar tata tamkar aikin asiri, dan bata iya komai da kanta sai dai ayi mata.
*Dare.*
"Kulu zo ki ɗorani a fo zan yi fitsari". Gwaggo da ke daga kishingiɗe ajikin filo ta faɗa. Kulu ta bar inda take zaune ta taso, ta ɗauko fo ɗin sannan ta ɗauro Gwaggon akai, bayan ta gama kuma ta taimaka mata wurin yin tsarki.
bayan ta sauketa taje ta zubar da fitsarin, ta ɗauko kofin silba mai ɗauke da koko ta kawo mata.
"Dan Allah Yaya kisha kokon nan, yau gaba ɗaya babu abinda kika saka acikinki, Yaya yanda kike ƙara ramewar nan yana ɗaga hankalina, rashin cin abincinki ba shi zai dawo mana da ita ba, sai dai ya haifar da wata m