NOVEL SHARES -
na baro shi shagon ɗinki yana nan tafe".
Gwaggo ta wuce dan ci gaba da hidimarta, shi kuma ya buɗe kwanon abincin bayan ya wanko hannu ya fara ci da bismillah, ba ma'abocin cin abinci bane shi dan haka kaɗan yaci ya aje gefe kusa da shi yay masa adani mai kyau yanda wani ba zai shigo yagga saura ba yace masa zaici, domin nawa ne ya ajiye min, haka muke da shi a gidan, idan banci sauran abincinsa ba to zamuci tare.
Ɗagowar da zaiyi muka haɗa ido sai nayi saurin saka hannu na rufe bakina zuwa hancina, murmushi me bayyanar da haƙora yayi ya ƙura min ido yana kallona tare da min nuni da ƙunshina da idonsa da kuma ledar da ke hannunsa.
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*MissAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
*3)*
Inna Amarya na ƙoƙarin saka min leda kawai na miƙe, ƙafar da akasa lallen a ɗage, na taka da wadda ba'a saka ba, na nufin wurin Ya Kabiru da ƙaguwar son ganin tsarabar daya taho min da ita.
Tangal-tangal nayi zan faɗi, Kulu da ake gefe ta miƙe da sauri dan zuwa ta tareni amma sai Gwaggo ta dakatar da ita da riƙe hannunta, sai Ya Kabiru ne wanda ya taso cikin azama ya riƙoni jikinsa, ya sunkuya ya ɗaukeni ya ajeni kan kujerar da ya tashi, Gwaggo cikin faɗa tace masa.
"wai Kabiru sai yaushe zaka gane wannan yarinyar ta girma ne, shekara goma sha uku fa ba wai shekara uku bane". Yana ɗora ƙafar da aka samin lalle saman kwano ya ce, "ni Gwaggo wannan girman da kuke ta faɗa ne har yanzu ban gani ba". Gwaggo taja tsaki tana ƙara cewa, "Ai shikenan sai kayita biye mata. ke kuma Amarya da kika ga ta tashi ai sai ki taɗo ƙafarta ta koma ta zauna, ni bana son wannan rashin natsuwar tata".
"yo ni ina ma nasan zata miƙe ɗin, kamar fa wacce aka fincika haka ta miƙe".
Ya Kabiru na dubana ya ce,"yanzu Mairo da ƙunshin ya dagulefa shikenan sai ƙafarki ta koma ta tsaffi". Ina dariya na ce,"ba zan bari ai yayi kamawar da zai zama dungulmi ba, kana bani tsarabata zanje na wanke sai Inna ta kuma samin wani". Inna Amarya ta sako baki da cewa, "Mairo yanzu ko ai sai dai ki tashi da ƙafa ɗaya, dan ba zan ƙarasa saka miki ba, kyata yawo da ƙafar haka ɗaya da lalle ɗaya babu". Nayi shiru kawai dan nasan tunda tace haka ta zauna, na ɓata fuska ina cewa Ya Kabiru, "to ka bani tsaraban na gani sai naje na wanke lallan kar ya kama sosai".
Ya miƙe daga tsugunon da yake yaje ya ɗauki leda kusa da Inna Amarya ya dawo yazo ya ɗaure min ƙafar. "ki saki ranki zansa miki na ɗaya ƙafar ai na iya. Kamin Hajiyarmu ta rasu ni nake saka mata, lokacin ba'a haifi mace ko ɗaya ba a gidannan". Ya buɗe baƙar ledar da ya shigo da ita, takalmi ne ya fito da shi kambos na makaranta fari ƙal sai ɗaukan ido yake, mai kyau da adon fulawoyi ajikinsa, ban san lokacin dana saki wata ƙara ba saboda murna, tsananin farinciki ya kamani, ta ko'ina ni ƴar gata ce tunda Allah ya bani Yayyu masu sona, ya kuma bani Inna Amarya bayan kyauta mafi girma da darajar da ya bani ta mahaifina.
ya kama ƙafata da babu lallai ya saka min, takalmi tamkar an auna da ƙafata tun kan a ƙera shi, adu'a na shiga kwaranyowa Ya Kabiru babu ƙaƙƙautawa, Domin ko a mafarki ban taɓa zaton ƙafata zataga irin wannan takalmin ba, dan nafi ganinsa a ƙafafun ƴaƴan masu kuɗin garinmu, ni ko a makarantarmu ma ban taɓa ganin mai irinsa ba, sai dai a ɗaliban makarantar kuɗi ta garin bichi. Ban gama wannan murnar ba ya kuma kasheni da wata murnar, ta hanyar ɗauko min dalleliyar jakar goyo ta makaranta mai bala'in kyau, itama dai nafi ganinta ajikin ɗaliban makarantar kuɗi, wayyo daɗi yanda kasan an tsundumani a aljannah, na tarairayo wuyan Ya Kabiru na ruƙnƙume shi ina daɗa masa godiya da adu'a, yana ta murmushi yace, "to Mairo acika min wuyan karya ɓalle". "Ya Kabiruna farincikin da kake sani kaima Allah ya saka acikinsa, takalmin da jakar sun yi min kyau sosai, Allah ya biya maka, Allah yasa karatunka ka sami aikin gwamnati". Na rungume kayana ajiki kamar wadda akace za'a ƙwacewa, har Alla Alla nake gari ya waye mu tafi makaranta.
Gwaggo da Inna Amarya suma sai godiya suke mishi da jerin adu'oi, Inna Amarya na cewa na kawo ta ɓoye min ina cewa ta bari zan adanasu a wajena kar wani abu ya taɓasu, Adawiyya ta ce, "idan ba ki bata ba ai kya ɓata su da lalle".
Sai Yamma sannan na cire ƙunshina, ina gama wankewa kuma Gwaggo tace mu shirya ta aikemu gidan Liman wajen Baba Lami, saƙon Nakiya ne ta bayar akai mata, Baba Lami ƙawar Hajjo ce mahaifiyar Gwaggo.
"Adawiyya ki riƙe min Langar nan da kyau kinga sabuwa ce, gadarta nayi a wajen Hajjo, bana son abunda zai taɓa lafiyarta, har kuje ku dawo ban yarda yaje hannun Mairo ba, dan zata iya salwantar min, tunda ita abun ɗaukar magana ba wuya yake mata ba idan ta fita...kuce da Baba Lami ɗin ina gaisheta kuma ina yi mata sannu da ƙafa, insha'Allahu ina nan shigowa na dubata".
Muka amsa da to, kafin ta juyo kaina da cewa,"saura ki tsaya siyan faɗan da banaki ba". Na amsa da to sannan muka