NOVEL SHARES -
tunaninta, amma har ayau da shi da ɗansa cike suke da fargabar dawowar tunaninta, basa so ko kusa tayi musu nisa, a halin yanzu dai idan akace maka Mairo Adamu Bichi ce zaka rantse da Allah ba ita bace, dan babu ta inda alama tayi nuni da hakan.
ƴaƴan manyan masu kuɗi suntiri su ke akanta, duk da sun san ita ɗin yarinya ce, ba yanzu zaai mata aure ba, amma kuma kowa na so ta saurare shi ne ta ba shi damar shiga zuciyarta, to amma ita tace bata da lokacin wannan shirmen ayanzu, karatu ne nata, karatu na boko burinta.
har ɗan gidan mataimakin shugaban ƙasa Ayamandi Kola sai da ubansa yazo nema masa aurenta, ta buga tsalla da ƙafafunta a ƙasa tace da Dad, da zarar an kuma yi mata wannan batu, daga lokacin zata ɗauke ƙafarta daga gidan ta tafi wata ƙasar ta barsu har sai ta gama karatu zasu ji labarinta, Dad yace to shikenan anyi an gama, ba za'a ƙara ba.
bata samun matsala da kowa a gidan, ta zama cikakkiyar ƴar gida, Joseph ne kawai matsalarta da yake nuna mata tsangwama, dan Allah ne da kullum sai sunyi faɗa, duk ranar da yayi mata dukan da taga ba zata iya jurewa to fa dakuwa suke ita da shi sai kace ƴan restling, randa kuma yay mata lami ƙalau sai ta ɗana masa tarko ta wani ɓangaren, yabi ya mayar da kansa kamar wani sa'anta saboda kawai ba ya sonta, Granny kuwa ido take zuba musu, babu wanda take tsawatarwa tunda baji suke yi ba, shi zuciya da tsokana, ita kuma rashin haƙuri.
kuma kullum a waya faɗawa Mom yake ta dawo gida akwai matsala, idan ta tambaye shi yace sai dai ta dawo ɗin matsalar ta girmi magana a waya. ita kuma tun seminar ɗin da suka yi na oriflame a london na kwana huɗu, ranar ta shirya zata dawo sai tsintar saƙo tayi ta gmail daga office nasu na Fidelity Bank akan an turata course a itally na tsawon wata 6, takaici iya takaici tayi, struggle ta saba da shi, amma a wannan karan kam ta gaji, saboda tayi kewar mijinta sosai, dan haka dole sai Dad ɗinne ya bita can tunda shi ba shi da wata matsala ta office ko wani abu makamancin haka.
*3:00pm.*
ƙarfe uku da rabi na dare bugawar agogo, Mairo ta farka a lokacin dan shan ruwa, ta duba kan table taga babu roban faro da bata rabo da ajiye shi saboda shan ruwan dare. ɗan tsaki tayi ta duba tulin littafan da ke gabanta, karatu take tayi bacci, baccin da ya ɗauketa bata sani ba.
ta sakko daga gadon ta fito, ta sauko parlon ƙasa dan babu ruwa a friedge ɗin parlonta, ta gama shan ruwan zata koma sama sai taji kamar maganar mutum, ta tsorata amma bata fasa dawowa da baya ba ta shiga laluben ganin waye.
ta ɓangaren ɗakin ajiyar littafai take jiyo sautin murya na fita a hankali, ta nufa wajen cikin sanɗa, da mamakinta Dad ta gani tsaye riƙe da waya a kunnensa, yana magana ƙasa-ƙasa, maganar da ta yi kama da ta sirri, ba wannan ne karo na farko da ta sha ganinsa a irin wannan lokacin ba yana waya, karo na kusan huɗu kenan, a yau dai ta gama fahimtar akwai wani abu da Dad ke ɓoyewa a gidan wanda baya so a sani, taji muryarsa ta ɗaga cikin faɗa yake cewa, "kai gaba ɗaya ba zaka gane ba...na gama yanke shawarar zan haƙa rami na binnesu, dan haka a gobe ba sai jibi ba, hakan ne kaɗai zai sa na sami nutsuwa hankalina ya kwanta". sai kuma ya ƙara yin ƙasa da murya yana ci gaba da faɗar abunda bata ji, har sanda ya gama wayar ya buɗe ɗakin littafan ya shiga sannan ya fito, da gudu ta bar wajen ta koma ɗaki.
ta haye gado tana maida numfashi, _zan haƙa rami na binnesu._ maganar ta ƙara haskawa acikin kanta a karo na barkatai, ba wannan ba ma, me Dad ke ɓoyewa?, me yasa take yawan ganinsa a irin wannan lokacin?, tukunna dai, me yake da bindiga a tsakiyar wannan daren?, lokacin da ya shiga store ɗin littafan me ya fito yana gogewa a hannunsa?, *SIRRIN ƁOYE*, tabbas akwai wani sirri da Dad ke ɓoyewa, ba kuma yaso kowa ya sani, menene shi?, taiwa kanta tambayar a sanda maganarsa ta kuma haskawa cikin kanta _zan haƙa rami na binnesu kawai, hakan zai sa na sami natsuwa hankalina ya kwanta._.
jikinta har lokacin bai bar rawa ba, ta miƙa hannu ga landline ɗin da ke kan bedside drower, dole ta sanar da Brother Ema, ya kamata ya san da wannan, ai dama dukansu sun fara suspecting nasa akan wannan keɓewar da yake cikin dare, Obi ma yace sau biyu yana ganinsa, kuma da bindiga a hannu.
sai dai kuma me, har tayi dialling numban nasa sai tunaninta ya sauya, ta sauko daga kan gadon, ta nufa tulin littafan da suke cikin wata drower ta ɗauko wani littafi da ta aro a library jiya, Malaminsu yace musu littafi ne guda da ke ɗauke da bayanin duk wasu stratagies na yanda zaka karanci fuskar mutum farat ɗaya.
*Vote, Comment & Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_The Pages Completely Goes To duk wani makaranci littafin sirrin ɓoye, na gaisheku, ina kuma yi muku Son So fisabilillah...masu text messages da kirana a waya su na yaba min, ku sani ina jin daɗi kuma ina godiya a gareku._
*24)*
*Kan