NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 78 of 223

ɗin da aka soya da ƙwai, sannan ta buɗe tea flask ta zuba tayi haɗin kauri na madara da bounvita. ta ɗauka fork zata kai bakinta Joseph ya isa a wajen, ya ɗaga hannu ya wanketa da mari yana nunata da yatsa yace,"wace ke da za ki zo ki zauna a dining tun Dad bai sauko ba, to bari kiji na faɗa miki karki sake ki ɗauki kanki matsayi ɗaya da ƴan gidan nan, wuyarta Mom ta dawo za ki gane kuranki, banza ƴar tsin....". bai ƙarasa faɗin ƴar tsintuwar ba Emanuel ya sharara masa maruka kyawawa guda biyu ta kowanne ɓari, a gigice ya ɗago yana duban Yayan nasa da ɓacin rai ke kwance a saman fuskarsa, malolon baƙin ciki ya tokare shi a maƙogoro, ko tantama ba zai ba Yayansa ya hauka ce, kai kowa ma ya haukace akan wannan Yarinyar. "Brother mari na fa kayi bayan ita ya kamata ka hukunta". Ema ya ce da shi,"ba ka kalla ita ɗin bata da cikakkiyar lafiya bane, kuma jiya me Dad ya faɗa maka?, to ka shiga hankalinka Joseph". duka su biyun huci suke kowa a wuya yake da ɗan'uwansa, a fusace Joseph ya bar wajen yana ƙananun maganganu, sai dai a masifar da ya tafi yana yi bai rufe baki ba Granny ta buga masa remote a baki, zafi biyu ya haɗar masa, saboda haka yayi fushi ya fice daga gidan gaba ɗaya. taso ta fahimci wani abu a maganganun da Joseph ya faɗa mata, iyaka haɗe fuskar da ya dinga nuna mata a daren jiya, da kuma hantara duk tayi zaton ko dan ita ɗin tana sakuwarsa ne, to amma a yanzu kuma mari da kalaman da yayi mata ta gane ba faɗan sako da sakuwa bane, rashin so ne zallarsa, da abunda take son ba da tabbacinsa akai, cikin abu biyu kwai ɗaya, ko ya zama ba Mamansu ɗaya da shi ba kamar yanda taji yace Mom zata dawo zata gane kuranta, ko kuma ya zama ba Mamansu ɗaya ba kuma Dad na nuna mata so fiye da shi. sai kuma ɗaya ɓari na zuciyarta yace mata _duk cikin hasashenki babu ɗaya, ki tuna a asibiti Uncle yace miki za'a dawo gida kuci gaba da rigimar da ku ka saba kamar kaji ke da Joseph._, me yasa ne take jin wasu abubuwan kamar bata taɓa sanin da su ba?, ko da yake ai Aunt Deborah ta faɗa mata saboda bugewar da ta yi hakan zaisa ba komai zata ke tunawa ba na baya. Emanuel ya dafa kafaɗarta ya zaunar da ita kan kujera, yasa handkey yana goge mata hawaye yace,"ki ƙyale Joseph mahaukaci ne yana da cutar Bipola disorder, har ma ya kai matakin ƙarshe na Mania, kinga kuwa shi abin aiwa uzuri ne". "what concern me da ciwonsa". ta faɗa tana rufe ido tana girgiza kai. ta yi ƙwafa da faɗin,"Mom zata dawo saita yi mana tsakani da shi idan ba haka ba kuma nake jangwalo ciwon nasa in kulle shi ɗaki babu wanda ya sani, ba zan buɗe shi ba har sai ya jiwa kansa rauni". "shirmen banza kawai ke da shi duk baku da hankalin...ki nutsu tun kan Dad naku ya sauko yasa miki belt ajiki, ai dama ƙafa yake ɗaga miki ganin ba ki da lafiya". Granny tace da ita a sanda take jan kujera ta zauna. cikin fushi ta miƙe zata bar wurin ta kuma cewa da ita,"tabbas kina so kiyi kwanan cell, karki hankalta ki gani, gashi nan sakkowa ai". "ni dai dariya ce tawa dan ko haƙuri ba zan bayar ba akan cuɗa yara". Obi ya faɗa a shi ma yana jan ɗaya daga cikin kujerun ya zauna. lokacin da Dad ya iso ya tambaya ina Joseph, suka haɗu suka rufa masa asiri da cewar Principal nasu ne ya kira shi, dalilin da ya sa yay fitar wuri kenan. har da Obi aka tafi kaita makaranta, Lead British International School Abuja aka kaita, kuma kasancewar speech ɗinta da kyau SS1 suka karɓeta, sai dai sun faɗa mata idan bata dage ba to zata yi repeating tunda yanzu su na ƙarshen second term ne. bata fara attending class ba sai da aka kaita asibitin ido aka mata medical glass, kullum driver ke kaita ya ɗaukota, kuma da yake tana da magana nan da nan sai tayi ƙawaye duk da ba kowacce ƙawa take kulawa ba musamman wadda take ganin ba level ɗinsu ɗaya ba, zaɓa ta ke ta dirje, idan taga wadda kuɗin ubanta yay kusa dai-dai dana su, tukunna zata kulata. to haka rayuwa taci gaba da tafiyar mata acikin tunanin da ta rasa, sosai ta samu sauyin rayuwa na jin daɗi, hutu da kwanciyar hankali, a wata guda curr da tayi a gidan ba zaka taɓa yarda da cewa ita ɗin bace, ta ko'ina ta sauya, irin kalar ingantaccen abinci da take ci da kuma hutu yay bala'in amsar tsarin garkuwar jikinta, hasken fatarta har ɗaukan ido yake saboda sheƙi, kyawunta na tun usuli shi yake fitowa a yanzu, kalar ƙauye ta bar jikinta, ta sami wata wayewa da gogewa kamar ba ƴar ƙauye ba, ta waye da cuɗanya da ƴaƴan manya da ita kanta rayuwar, ta kuma goge da ilimin boko da na addininsu, ayanzu haka ita makaranta ke ɗauka ta wakilcesu a duk wani debate, turanci a bakinta kamar baturiya, idan tana speech har tsuma jikin mutum keyi, kwanaki da aka haska vedio ɗinta a BBC tana fighting against irin taimakon da gwanati ya kamata take bawa ɗalibai da kuma samarwa matasa aikin yi, Dad sai yaji gaba ɗaya duniyarsa ta rikice da daɗi, inama ace, inama ace ƴarsa ce da ya haifa a cikinsa, kuma shi ma sai ya tafi irin fatan da Emanuel keyi akan kar tayi regaining
🏠