ma ta buɗi baki da cewar,"welcome back Dad". ta ƙasan siririn medical ɗin da ke idonsa ya kalleta ya amsa mata.
"sai yaushe Gloria zata dawo ne, this time aroud ta jima da yawa".
Dad ya kalla Granny da ta yi masa tambayar yace,"they had just arrive back, sai suka sami saƙon za su yi presenting seminar na oriflame a london, amma tace ba zasu wuce 3-4days ba zasu dawo". "Yayi kyau". ta faɗa tana miƙewa tare da cewa Gift ta tashi ta wuce ɗaki ta ajiye kayan.
Mairo ta sami tarba me kyau daga wurin Dad, wanda ya ƙudurta ɗaukanta tamkar yarinyar da ya tsuguna ya haifa, ya ɗau alƙawarin zai kula da ita har zuwa ranar da zata sami lafiya tunaninta ya dawo su maidata wurin iyayenta.
a ɗazu da ya dawo niyyarsa a saka hotonta a media da kuma sanarwa a gidan radio, ko Allah zai sa wani nata yaji, to Emanuel ya hana shi ya kafa masa hujja me ƙarfi akan rashin aiwatar da hakan, inda yace masa wani kidnapper ɗinma zai iya gani yazo ya karɓeta ba tare da ansan wane shi ɗin ba tunda ita ba'a cikin tunaninta take ba, Dad ɗin kuma ya gamsu, Obi ma ya goyi bayan Yayansa.
ƙarfe tara da rabi na dare suka hallara a dining area yin Dinner kamar yanda suka saba, tun daga breakfast, lunch and dinner duka tare suke yi. tun zamansu Joseph ke aikawa Mairo harara, balle da yaga kowa na haba-haba da ita, kamar ɓarauniya zuwan yau kaɗai ta sace zuciyarsu, a hankali ya saki ƙwafar da ita kaɗai ta ji da take kusa da shi, suka haɗa ido ta turo masa baki gaba, cikin zafin nama ya daki dining table ɗin ya fuskantota yana nunata da yatsa da cewa,"Dad yarinyar nan ta raina ni, kalla fa yanda take murguɗa min baki". Dad ya ɗaga masa murya,"mene hakan kake yi Stupid Brother kawai, is she not your sister...kuma baka kallon bata da lafiya". yabi kowa da kallo da yanda suka yo kansa, abun ya ɓata masa rai ya ƙara jin tsanar yarinyar a ransa, shi ne auta a gidan, zai iya rantsewa da wayonsa dai Dad bai taɓa ɗaga masa murya ba sai a yau, yana masifar sonsa kasancewarsa ɗan auta, amma saboda zuwan wannan banzar yarinyar Yau Dad ne ke yin kamar zai duke shi, dama yasan za'a rina ai, tunda Brother ya basu labarinta yasan sai ta ƙwace masa fada a wurin Dad, saboda yana so ya ganshi da ƴa mace kuma Allah bai bashi ba, yana yawan faɗan yanda yake so ya ganshi da ƴa mace.
ba dan yana gudun kar Dad ya hana shi motar da yake so a siya masa ba, da babu abinda zai hana shi ɗaga waya ya kira Mom ya sanar mata da zuwan wata ƙazamar stranger gidansu, to matsalar ɗaya Dad ya gargaɗe shi yaja masa kunne akan cewar ya sake ya faɗawa Uwarsa sai yaga yanda zaisa ayi da shi a barrack, shi kuma Dad ba ya hane shi bane saboda gudun fitinar Gloria ba, sai dan ya barta ta kammala agenders ɗin da ke gabanta hankai a kwance, idan ba haka ba yanzu tana jin labari zata baro duk wasu activities nata ta dawo gida.
har aka kammala cin abincin acikin ɓacin rai yake, yana jin kamar ya shaƙeta. ɗazu da yamma da Emanuel ya fito ya tarar su Granny basa nan, ya saka ƴan aiki suka gyara extra room ɗin da yake a sama na kusa da ɗakin Dad, both the bedroom and parlo, ya zama shi ne ɗakin Mairo. saboda haka yanzu da za'a tafi kwanciya su uku suka haura sama, da ita da Dad da kuma Emanuel, duk yanda Granny tayi da ita akan tazo su kwana tare taƙi tace,"a'a ni bana kwana da tsoffi, snoring su ke yi a bacci". basu Obi kaɗai ba, har Dad sai da yay dariya.
su na hawa stairs ɗin Dad ne ke agaba sai ita ke bin bayansa Emanuel kuma na biye da ita, ta cewa da Dad,"ɗazu Uncle yay min faɗa akan nayi mistake wurin hawa flight, har yace zai zane ni". Dad ya kira sunan Emanuel ya amsa, yace da shi,"baka san ita ɗin Auta bace, kuma ba'a yiwa Auta faɗa, karka sake idan ba haka ba raina zai yi babu daɗi...ko kaima baka kalla saboda first born bane Mom ɗinka ko hararanka bata yi". shi dai Emanuel murmushi kawai yake, Dad ɗin kuma yace da Mairo,"kiyi haƙuri ba zai ƙara ba daga yau...kuma duk wanda ya kuma yi miki faɗa kice Dad ya hana ke auta ce yana sonki da yawa". "tom shikenan Dad ena nima ina sonka". ta faɗa tana mintsilar hannun Emanuel tana dariya ƙasa-ƙasa, ya kai mata ranƙwashi dai-dai lokacin da suka hayo saman gaba ɗaya kowa ya nufa ɗakinsa dan kwanciya.
****a washe gari ƙarfe shida da rabi Emanuel ya leƙa ɗakin Mairo yace ta shirya da wuri zai kaita school, jiya Dad ya sanar masa a yau ya kaita makaranta, shi mutum ne da ba ya son zaman yaro a gida.
ita dai tunda ya tasheta ɗin ya juya ya fita ta koma baccinta, bata farka ba kuma sai quater to 8, tai sauri tayi wanka ta shirya sannan ta fito, ɗakin Dad ta shiga ta tarar shi ma yana shiryawa, ta gaida shi sannan ta fito ta sauka zuwa ƙasa.
sakkowarta dining area ta nufa, Eze(me girka musu abinci) har ya kallama girki ya jera a dining ɗin, a yunwace take, dan haka taja kujera ta zauna, ta rasa irin cikinta ita kam ci kamar gara, tana da saurin jin yunwa kuma a asibiti an gwadata babu ulcer. bata tsaya tunanin jiran fitowan kowa ba ta buɗe flask ta fara zuba irishi