fita office sai 6pm idan tana ƙasar kenan.
Granny ta shiga tashinta da kiran sunanta da suka raɗa mata Gift, da yake me nauyin bacci ce har sai da tasa hannu tana ɗan taɓa ƙafarta sannan ta shiga buɗe idonta a hankali tana murzasu har suka buɗe duka ta saukesu kan Granny tana miƙa.
Granny ta sakar mata murmushin da ya bayyanar da haƙoran tsufanta sannan tace mata,"get up and take shower, we are going out". ta gyaɗa mata kai kawai tana ziro ƙafafunta ƙasa su ka fito tare, zata shiga bedroom Granny ta dakatar da ita da faɗin,"a'a ba nan za ki shirya ba". ta faɗa holding her hand to make her way to her own room after she called Buky tayi informing nata tayi fixing Joseph's bedroom.
bata jima a wanka da ta shiga ba ta fito ta shirya cikin tsangallalun kayan da suka koma kayanta a yanzu, ita da Granny suka fito a tare riƙe da hannun juna, a parlo Granny ta danna landline ta kira wayar driver akan ya tada mota zai fita da su anguwa.
*Acorns & Gold Boutiques, Abuja.*
Granny ce keta aikin jidar kayan sawa acikin store ɗin kamar me shirin haɗa akwatin lefe, kaya masu kyau da tsada take ɗiba, tun daga kan gowns, mini skirts, t-shirts, bomshots, bras, high hill and flat shoes, wrist watch, earings, bangles da sauransu, haka ta dinga ɗiba tana zubawa a basket ɗin da Mairo ke biye da ita, sai da ta ɗibi kayan da take ganin zasu isa Mairo sakawa zuwa ɗan zaman da zatayi sannan suka isa wurin biyan kuɗi tai payment da Atm card.
ma'aikacin store ɗin da kansa ya ɗauki kayan ya kai har mota saboda yasan wace Granny, a kaf Abuja yankin Asokoro anyi ittifakin babu wani family da suka san darajar ɗan Adam su ke martaba shi da girmama shi irin gidan General Tosin Afafa, ahali ne da suke kyautatawa kafiri ɗan'uwansu harda musulmi, Allah ya wadatasu da arziƙi me yalwa, kuma basu kasance cikin irin masu arziƙin da suke ƙam ƙam da dukiyarsu ba, dukiyarsu su na bada ita ga kowa ne, wannan dalili na kyautatawarsu ya saka suke samun adu'a iri-iri daga musulmi akan Allah yasa su karɓi hasken musulunci.
daga nan kuma suka wuce Perfect Trust Cosmetics, anan ma kayan kwalliya ne kit guda ta kwasa sannan suka fito suka wuce Agabason Perfumery, anan ma turaruka ne ta kwasa masu tsada da ƙamshin gaske, kafin daga bisani kuma su wuce wurin saloon, aka wanke mata kai, aka wanke ƙafa akai gyaran farce tare da fixing nails, a taƙaice dai ta ko'ina sai da Granny tasa aka gyara Mairo ta ƙara fitowa sak a ƴar kafirai. sai da su ka biya suka sha ice cream daga bisani kuma suka wuce gida, ba su koma ba sai ƙarfe takwas da rabi na dare.
lokacin da suka dawo kowa na zaune a parlo ana hira, ba hirar komai mahaifin nasu ke musu ba sai ta rayuwa, su bar ganin shi me arziƙi ne, ya tara musu kuɗin da ko bayan ransa ba zasu yi talauci ba, namiji yay tunƙaho da dukiyar kansa bata ubansa ba shi ne ya cika namiji, kuma dukiyar kanka ita kake bugun ƙirji da ita, mutum ba ya kaiwa high level sai ya zama ɗan gwagwarmayar rayuwa sannan, shi ma ba haka ya sami wannan dukiyar da yake ganin ta masa yawa ba, sai da yay aiki da jininsa da ƙarfinsa, tun yana ɗan 13years yake fita waje yay cuɗanya da mutane iri-iri, shi ne dako shi ne aikatau, shi ne wanki da guga, shi bai sami gatan da uba zai ɗebi maƙudan kuɗi ya bawa ɗansa ba wai saboda kar ya rasa na kashewa, a'a, tun da ya kai 15years idan ya tambayi kuɗi a gida Babansa cewa yake da shi ka nemi na kanka, su tambayi Granny zata ba su labari. ya tsaida kallonsa akan Joseph yace masa,"saboda haka ka sake buɗe idanuwanka, ka farka daga baccin da kake, har yanzu acikinku kai ne baka da hankali...kaƙi ka tsaida hankali kayi karatu kana biyewa abokan banza su na ɗoraka a motar da zata kaika tashar dana sani...ball kawai ka saka a gaba Joseph, ball kawai, nasha faɗa maka duk sunan da zaka yi sai da ilimi duniya take yayinka, na maka faɗan na maka nasihar kaƙi kaji, kaƙi karatun, na rabu da kai na kai ka company nanma kaƙi zama, ya kake so nayi maka Joseph?, ranar da polive suka biyoka kasan yanda naji?, sai da na rasa jina da ganina na ƴan sakanni, zuciyata har yau bata bar ciwon wannan abin kunyar daka ja mana ba, amma shikenan kaci gaba idan kana ganin hakan shi ne dai-dai, akwai ranar da zaka wayi gari kaga babu ni a duniyar, na mutu an rufe babin rayuwata, na bar maka duniyar". Joseph ya hau ciccin magani, faɗan Dad kullum akansa yake ƙarewa, kamar kullum shi ya ke yin ba dai-dai ba, ya kamata Dad ya ƙyale shi akan batun karatu tunda yace masa ba ya so, ya ƙyale shi da maganar zuwa aiki tunda yace ba zai yi ba, ai su na da kuɗin da yafi ƙarfin ya fita yay aiki ako ina ne, shi ba za'a masa dole ba, yana da ƴancinsa.
a gajiye liƙis su ka shigo Mairo na riƙe da handbag ɗin Granny sai lanƙwashe jiki take a lallai ita ta gaji da yawa, a kusa da Joseph ta zauna tana miƙe ƙafafu tare da fadin,"Uncle am very tired". ta faɗa tana kallon Emanuel da su ke facing juna, hararta kawai yayi. Granny taji tana welcoming Dad sannan ne ma ta lura da shi, ita