NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 75 of 223

ta yasar kan kujera, sannan ta ɗauki hanyar dining area, ta ɗaga zara-zaran labulayen da ke rufe da wajen, anan taga ƙofar kitchen don haka kai tsaye ta shiga ciki, ta isa ga oven ɗin da ta gani a kunne ta kashe sannan ta buɗe ta ɗauko kazar da ke ciki tasa a plate, ta sake isa friedge ta buɗe ta ɗauko youghrt me sanyi. ta wani entrance ɗin daban da wanda ta shigo ta fita, ta ɓullar da ita ga wani part na daban me ɗauke da ɗai-ɗaikun shuke-shuken fulawowi masu kyau. ƙofofin ɗakuna guda huɗu jera da wurin, biyu daga ɓarin hagu biyu daga dama, du ka doors ɗin colours guda ne, dan haka tasa kanta tsaye ga ƙofa ta biyu da ke a ɓarin dama ta buɗe ta shiga. bedroom ne me girma da medium italian bed acikinsa, wadrobe na fuskantar gadon sai mirrow daga jikinsa, da kuma wani medium glass table a gaban gadon, rabin bangon bedroom ɗin manne yake da stickers na hoton Ronaldo, ɗakin ya haɗu sosai dan sai zuba ƙamshi yake, komai nasa blue and white ne, ta ɗaga labulen da take tunanin window ne sai taga wata ƙofa ce ta daban, nan ta murɗa handle ta buɗe, toilet ne wanda ya haɗu iyakar haɗuwa, komai na cikinsa daga waje akayi order ɗinsa kamar yanda duk wani kaya na gidan yake nunawa, sai ta janyo ƙofar ta rufe. da guntun tsaki ta fito daga bedroom ɗin ta buɗe ƙofan kusa da shi, nan kuma parlo ne me ɗan girma shima, yasha wasu azababbun kujeru da kayan ƙawa na decorating parlo, sai medium plasma manne daga ɓarin gabas, da hotunan ronaldo a mammane a jikin bangon parlon kamar dai na bedroom ɗin, alamu dai sun gama nuna mamallakin ɗakin cikakken ɗan ƙwallo ne kuma masoyin Ronaldo, ta maida ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin parlon da ya gwauraye da sanyin Ac haɗe da wani daddaɗan ƙamshi. zama tayi kan kujera tare da kunna tv ta nemo channel ɗin da ake wani american film, tana kallo tana cin kaza tana kurɓar youghrt irin na wadda hankalinta ke kwance duniya tayi mata daɗi. tana gamawa ta jawo tissue ta goge hannu sannan ta jinginar da kanta ga kujerar taci gaba da kallon, can idanunta suka fara rufewa ta miƙe ta koma bedroom ta kwanta, a yanda take zazzaƙewa ka rantse dama can ƴar gida ce. gidan tsit kake jinsa kowa na ɗakinsa, sai tvn parlo da ke kunne with low volume, ƙarfe biyar na yamma Granny ta fito daga ɗakinta, ta ƙwalawa Buky kira sai gata ta bayyana a gabanta, tana dubanta tace,"where is Gift?". a ɗazu da suka shigo Emanuel sai da ya faɗa mata sunan Mairo(Gift) kafin ya wuce ɗakinsa, dan haka bata tafi tunani ba akan ɓaƙon sunan da ya zo gidansu, kanta a ƙasa tace da Granny,"tun ɗazu ta bar nan, may be she is in her room". Granny ta kaɗa kai, sai dai a tunaninta wanne ɗaki ta wuce dan Emanuel yace da suka shigo bai nuna mata inda zata zauna ba, shi dai kawai ya barta a parlo, ita kuma abunda ya hanata fitowa ta sami Mairo a lokacin kanta na mata ciwo, kuma ko da tace Emanuel ɗin yasa Buky ta kira mata ita tazo ɗakinta sai yace ta kwanta tayi baccinta kawai, in dai Gift ce tazo ƙara mata zafin ciwon zata yi, ba dan taso ba ta kwanta ɗin bata ga Mairo ba a time ɗin, amma tunda Emanuel ya shigo ya bata labarin komai taji zuciyarta ta shiga zullumin son ganin Yarinyar. a ƙasa babu wani ɗaki bayan nata da na su Joseph da Obi, Emanuel da Mom da Dad duka a sama suke, saboda haka tasan da wuya idan ba part ɗin su Joseph tayi ba, tunda hanyar da upStairs yake indai ba kai ɗan gidan bane ba sani zaka yi ba, haka nata ɗakin ma kamar ba'a parlo yake ba, sai ka san gidan sannan zaka iya sanin ta inda ƙofar part nata yake. kitchen ta shiga ta sada kanta ga ɓangaren su Joseph, bedroom ɗin Obi ta fara buɗewa da ke ɓangaren hagu taga bata ciki, dan haka sai ta nufa na Joseph tana buɗewa kuwa ta ganta tana bacci hankali kwance, taja blanket ta rufe jikinta, Granny ta godewa Jesus a ranta da bai dawo da Joseph a wannan lokacin ba ya sameta akan gadonsa, dan shi mutum ne irin mahaifiyarsa da basa son baƙi sam, idan da ya shigo ya ganta sai ya mammaujeta kafin ya kai ƙorafin a sauya masa komai na ɗakin, tunda har wata stranger da basu san daga inda take ba zata taɓa kayansa. fuskarta na bayyanar da siririn murmushi ta ƙaraso ciki, dama acikin bayanan da Emanuel yayi mata akanta ɗazu, ya shaida mata tana da bacci kamar me laulayin ciki, wuyarta taji ta ita kaɗai ko kuma taji mutum a kusa da ita zata ɓingile a jikinsa. ta isa gadon ta zauna daga gefe tana kallonta, tasa hannu ta shafi gefen fuskarta, yarinyar tana da kyau sosai, a yanda fuskar baccinta ya nuna zaka san me ƙiriniya ce ba irin ƙiriniyar yara ba, tun a ɗazu da Emanuel ya bata labarinta taji ta shiga ranta tun bata ganta ba, tana sonta da tausayin halin da take ciki da dukkan zuciyarta, haka kuma tayi farin ciki da zuwan yarinyar duk da bawai zama ne na dindin ya kawota gidan ba, ko ba komai gidan zaifi mata daɗi yanzu ta sami ƙawar ɗebe kewa, dama basu da mace a gidan ƴan mata. kullum ita kaɗai take zama a gidan tunda Gloria itama ba zaman gida take ba, ƙarfe 7am take
🏠