NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 74 of 223

i lokacin kuma da Emanuel ke gyara mata kwanciyarta yana juyar da kanta, garin juyi hannunta ya sakko ƙasa, ya maida kanta saman cinyarsa dan ya lura bata ji daɗin kwanciyar ba. Amadu dai jujjuya maganar da zai masa yake acikin ransa, dan bai san ta yanda zai ɗauketa ba, sai da Emanuel ya katse shirun nasa ta hanyar sake tambayarsa sannan yace, "Sir dama i want to talk to you about your guest". lokaci ɗaya Emanuel ya saki murmushin da suka bayyana haƙoransa dan ya san inda sauran zancen Sectery zai dosa. saboda haka yace da shi, "ƙanwata ce ita ce autarmu. sun zo escourtion ne daga makaranta sai Dad yace ta zauna idan zan wuce sai mu tafi tare". kunya ta kama Amadu yaji dama bai masa maganar ba, sam bai kawo batun ƙanwarsa bace kamar yanda yaji PA ta faɗa, to amma har ga Allah indai zaman da yake da uban gidansa na amana ne to lallai idan yaga zaiyi ba dai-dai ba ya tunasar da shi kamar yanda uban gidan nasa ya roƙe shi tun farkon zuwansa aiki, ba ya so ya zama kamar Md ko Accounter dan su waɗannan sheɗanu ne, ko a jiya yana jin faɗan wata da Accounter akan zata zubar da ciki. "dint you trust me ne na kira maka Dad ɗin ka tambaye shi?". ya faɗa yana ɗaukan wayarsa.  cikin sauri Amadu ya girgiza masa kai,"a'a na yarda da kai mana...kawai dai naji nauyinka ne akan yi maka maganar, kayi haƙuri ka yafe min". yace da shi babu komai, shi ma kuma ya gode dan saboda yana sonsa ne har yasa ido akan abunda ba shi da kyau. da lokacin tashin Md yayi yazo da kansa ya ɗauki Mairo, sai dai Emanuel ya roƙe shi akan kar ya ci amanarsa, shi dai bai ce masa ƙala ba banda harara da yake binsa da ita. sai da ya bawa Mairo waya yace ta riƙe zai ke kira yaji idan sun je gida, ya kuma dubi Md yace,"in dai na kira wayar nan naji bata yi picking ba to wallahi da police zaka ganni". Md yaja tsaki ya fice yana faɗin,"me zai hana ka haɗata da wanda ka aminta da shi". acan gidan Md ma Favour matarsa ta karɓeta hannu biyu, amma still sai da ta kira Emanuel taji gaskiyar lamari sannan, a duk inda Mairo ta shiga sai sun saba da mutum, ko a yanzu cikin kwana ɗaya tal sunyi wata shaƙuwa da Favour, da yake ita teacher ce duk lokacin da zata tafi school tare suke tafiya. a haka sai da ta kwashe kwana biyar cif a gidan Md kafin Emanuel ya ɗauketa su wuce Abuja. a wajen shiga jirgi ne suka buga dirama da ita, tun haɗuwarsu karo na farko da ya ji ta ɓata masa rai, iya yarfi ta yarfa shi, dan ba ƙaramin bada shi tayi ba a gaban jama'a. saboda haka ko da aka shiga jirgin sai yay mata nuni da economy class seat, shi kuma ya wuce first class seat. kuma har jirginsu ya sauka yana jin haushinta, ita ma kuma tsawar da yayi mata yasa take jin haushinsa, dan haka ko da jirgi ya tsaya ɗaukanta yay cak ya fito da ita gudun karta kuma buga masa hauka irin ɗazu. haushinsa ya ƙaru a ranta, ƙatuwa da ita ya wani ɗaukota kamar tace masa bata da ƙafa, saboda haka cikin ƙunƙuni tace da shi a sanda yake direta bakin mota,"kuma saina faɗawa Dad kayi min faɗa". ya galla mata harara ya shiga mota, sannan ita ma ta zaga ta buɗe baya zata shiga ganin cewar driver ne yazo ɗaukansu, sai dai tana ziro ƙafa cikin ɗagin muryar faɗa yace ta koma gaba. *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *23)* ba ƙaramin daɗi Emanuel yaji ba san da driver yace da shi Mom bata dawo daga tafiyar da tayi ba, dama yayi tunanin ko zata rigasu sauka tunda tace masa ƙila ta biyo flight a yau, to inma dai yau ɗin zata dawo fatansa su rigata zuwa gidan ba wai su je su sameta ba, dan Allah ya sani ba ya ƙaunar faɗanta. driver yay parking, daga Emanuel har Mairo kowanne ya fito cikin fushi ya ɗauki hanyar cikin gida. ba wai dan ta san hanya ba, sai dai ta tsaya ne sai da yayi gaba sannan tabi bayansa tana aukin ƙunƙuni. su na shigowa falo Buky(house maid) da ke aikin goge tv tayi saurin zubewa tana kai masa gaisuwa, kafin daga bisani ta dubi Mairo tace mata,"welcome Maa". Mairo ta murguɗa mata baki, sannan ta nemi ɗaya daga cikin lumtsatstsun cushions ta zauna tana lumshe ido, me aikin ta ƙaraso ta duƙa gabanta ta cire mata takalmin ƙafarta me shegen tsini, har lokacin kuma bata bar ɓata rai da faman haɗe gira tana girgiza ƙafa. Emanuel kam tunda ƴar aikin ta karɓi suite ɗin jikinsa da ya cire, yay upstairs ɗakinsa, ba tare da ya bi ta kan Mairo ba, domin yanda yake jin haushinta duka zai iya biyo baya akanta. sai da ta gama kumbure-kumburenta sannan ta miƙe daga kan kujerar, ta tsaya tana duban parlo da tunanin ma ina ne taƙamaiman hanyar ɗakinta, tayi tsaki tana cire top ɗin da ke jikinta
🏠