su kawo wata manufar sai ya bata amsa a taƙaice.
"Little daughter of the family". "wow". ta faɗa tana duban Mairo saboda zuzuta zance har da cewa aikuwa ga kamanni.
"our little what is your name?". ta tambayi Mairo tana shafo fuskarta. Mairo dai aikin yatsine fuska kawai take. jin tambayar da ta yi mata da sauri ya juyo ya bata amsa a taƙaice, "Gift". sannan ya kamo hannun Mairo suka yi ciki. saboda matsawar ya barta da PA har ta yanda aka haifeta sai ta tambaya.
su na shiga office yay mata nuni da wurin zama, ta ƙarasa ta zauna tare da cire takalmi, shi kuma ya shiga toilet ya fito sannan ya ɗauki suite ya saka. sannan ya dubi Mairo da ke kan doguwar cushion ɗin office ɗin tana bin ko'ina da ido, murmushi yayi ya isa friedge ya ɗauko 5alive ya aje agabanta.
"Beb zan fita but i will be back soon, ga laptop nan the passwrd is Ema1988. if the landline rings, you pick up its me oak". Bai jira me zata ce ba ya juya ya fita dan MD jiransa yake zasu fita tare.
ta buɗe 5alive ɗin ta zuba a cup tayi masa shan gayu, sannan ta ɗauki ɗan ƙaramin bible ɗin da ke kan center table ta shiga karantawa, kamin daga bisani ta ajiye shi ta kunna system ɗin, sai kuma ta bar kanta ta kunna tv tana kallon labarai a BBC News.
"Yes Come in". ta faɗa a san da taji anyi knocking door, kuma ba tare da ta dubi wanda ya shigo ba ta ci gaba da kallon tv, hankalinta ya karkata ga labaran da ake akan Covid19 da ta dawo. Ahmadu ne ya shigo hannunsa riƙe da files ya aje akan table ɗin Emanuel, ganin ba ya kan kujerarsa sai ya kalli inda ya san shi ne mazauninsa bayan wannan kujerar, to amma yana kallon kujerar sai yay saurin ɗauke kai saboda yanda yayi tozali da santala-santalan cinyoyin Mairo farare ƙal da su duka a waje, zatonsa ma PA ce sai kuma ya tuna PA bata kai hasken haka ba, kuma yanzu ma ai ya barota a waje, sai daga baya ya tuna Sectery ɗin MD da Marketed sun guntsa masa gulmar Oga yazo da wata haɗaɗɗiyar Beb, amma yace musu ƙanwarsa ce, sun dai ji shi kawai amma ba su yarda ba, to ashe da gasken suke tunda ga idanuwansa sun gani.
yanayin yanda Mairo take ayanzu zaka rantse da Allah cewar bata taɓa haɗa hanya da musulunci ba, gaba ɗaya ta gama sajewa da arna ta ko'ina, a kafiranma irin waɗanda sukewa addini riƙon gamgam, saboda haka ba zaka taɓa iya shaidata ba a kallo ɗaya balle kuma ace gefen fuskarta ne kawai ka iya gani, wannan dalilin yasa ko kusa ko alama Amadu bai shaida tasu bace dan ba ta inda alama ta nuna akwai haɗi.
ɗago kai yay zai yi magana da ita sai ya saurin saukewa dan ba zai iya yin magana da ita a yanda take ɗin ba, rigarta ma bata rufe mata cibiya ba, dan haka kansa a ƙasa ya tambayeta,"ina Oga?". ba tare da ta dube shi ba tace,"He left but said he would be back soon". ta faɗa har lokacin hankalinta naga labaran, bata ko kalli inda yake ba.
yay ɗan jim kamar wanda zai ƙara cewa wani abu sai kuma ya fita, baiyi minti goma da fitar ba ya kuma shigowa, ya ƙarasa har inda take ya aje takeaway saman table, sai da ya juya zai fita sannan ta ɗago taiwa bayansa dubi ɗaya ta ɗauke kai.
Ɓangaren Emanuel kuwa bayan fitarsu da Md Fidson Healthcare Plc suka nufa, daga nan suka ƙara wucewa Federal Palace Hotel and Casino inda Dad ya turasu akan wani program da za'a gabatar. a hanyar dawowa Emanuel kewa Md complain ɗin yanda zai yi da kai Mairo gida, yana gudun ɓacin ran Mom matuƙa, duk da cewar Dad yasan da komai.
Md yay tsaki da faɗin,"kai kake neman ɗorawa kanka. tunda yarinyar nan taji sauƙi we should take her to radio station a bada a sanawa idan iyayenta sunji su nemeta a wurinka amma ka tsaya kana damun kanka...". Emanuel ya katse shi,"kaga maganar kai cigiyarta ma bai taso ba, zata zauna damu har sanda zata ji sauƙi sannan ta faɗi inda take mu kaita...so dont talk to me anymore akan wani kai cigiyarta". Md yay ɗan jim yana kallonsa sai bai ce komai ba, dan a yanda yaga ya ɗauka da zafi idan ya kuma cewa wani abu to zasu iya yin rigima.
dan haka suka bar batunta suka kama na company, bayan dawowarsu kuma Emanuel ya ke sanar masa,"idan zaka wuce you are going with her ba zan kaita hotel ba".
"ka fara sanar da Favour tukunna". ya ba shi amsar yana ɗaukan hanyar office ɗinsa, Emanuel yay ƴar dariya saboda fushin da Md yake mara dalili.
a office da ya koma ya tarar Mairo tayi bacci, bai tasheta ba ya shiga toilet ya watsa ruwa, bayan fitowarsa kuma ya isa ya zauna kan kujerar kusa da kanta, sannan ya ɗauki sauran abincin da ta ci ta rage ya cinye. yay dialling number PA ta kawo masa coffee dan ba ya rabo da shansa. Amadu ya shigo yay masa bayani akan files ɗin da ya ajiye masa, yace da shi zai duba sai zuwa gobe. da mamakin Emanuel sai yaga Amadu ya tsaya bai fita ba, abunda bai taɓa yi ba, sai dai a yanda alama ta nuna yana da abun cewa mai muhimmanci, a ransa har yana kawowa ko jikin Mamar tasu ne ya ƙara tashi, dan satin da ya wuce ya kuma zuwa gida, saboda haka ya tambaye shi,"Sectery is there any problem?". Amadu ya ɗago ya dube shi, dai-da