NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 72 of 223

a kasa taɓuka komai har tsawon daƙiƙa biyu da suka shuɗe sannan ita ta ɗago kanta ta kalle shi, har wannan lokacin bai buɗe idonsa ba, ya rasa me yasa yake fargabar samun lafiyar tunaninta, jiya zuciyarsa har faɗa masa tayi Allah sa kar ta dawo dai-dai, to amma bai san mene dalilin hakan ba. ita dai sai ta bishi da ido, zatonta ko adu'a yake yi dan haka ta ƙyale shi har sai da ya gaji ya buɗe idon dan kansa ya saukesu akanta, da mamakinsa sai yaga saɓanin tunaninsa da kuma hasashen likita, bai san lokacin da ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya ba ta farinciki, haka ya kama hannunta su ka tsallaka titin cikin sauri suka koma asibitin. washegari da safe da ya je amsar takardar sallama yay ma likita bayanin komai, shi ma kuma likitan ya ƙara tabbatar masa da cewar ai a binciken ma da ya ƙara yiwa takardar hoton da aka mata last bai zama lallai ma ta kai lokacin da su ke ƙiyasi ba, yanzu ana kan tsammanin faruwar abu biyu ne, ko ta wuce lokacin da su ke zato, ko kuma ta sami lafiya kamin lokacin. sai dai Dr Simon ya sake ba shi shawarwari na yadda za'a iya shawo kan matsalar tata da wuri, godiya yaywa likitan sannan su kai sallama ya fito, acan wani ɓari na zuciyarsa daɗi yake ji da ba zaman asibitin zasu ci gaba da yi ba balle likitan ya dinƙa kawo abubuwan da za su iya janyowa Mairo ta sami lafiya. a bakin mota ya tarar da Deborah tsaye ita da Mairo su na jiran isowarsa, Deborah tayi shaƙuwar da take jin tamkar kar su rabu da Mairo, jinta take kamar ƴar da ta haifa acikinta dan ƴarta Ciyoma sa'arta ce, a ɓangaren Mairo ma hakan take ta saba da Deborah sosai, ta shaƙu da ita da har take jin rashin daɗin rabuwar da zasu yi a yau. booth ya buɗe ya zuba kayansu, ya ɗauko kuɗi ya ƙirga dubu talatin ya bawa Deborah yace sauran zai yi mata transfer, ta amsa tana yi masa godiya sosai, sannan tayi musu sallama ta koma cikin asibitin, shi kuma yace da Mairo ta shiga mota tukunna shi ma ya shiga, zamansa yayi shiru ya kasa yiwa motar key sai aukin shafa goshi da yake. da can bai yi tunanin zai yi facing matsalar komai ba akan sallamarsu a asibiti, sai yanzu ne zuciyarsa ta fara taraddadi akan kai Mairo can gidansu, sarai yasan wace Mom, Ko da giyar wake yasha yaje da Mairo gidan sai Mom ta saito mata hanya, balle kuma ace ya kaita acikin hankalinsa, da sauƙi ma idan ace zata ce shi da itan su sauya sheƙa, to Mairon kaɗai zata sa security ɗin gidan yay waje da ita, kuma sai ta ci zarafinta kafin nan. Mahaifiyarsa mace ce mai izzah da mulki akan irin dukiyar da Allah ya wadatasu da ita, akwai jakin kishi da ƙamƙam da abun da take so, ko kaɗan bata ƙaunar wani ya raɓi iyalinta, komai tafi so daga ita sai yaranta acikin gida, Kakarsu ma dan ita ta kawo mata mijinta duniya ne da bata isa ta rayu da su acikin gida ɗaya ba. shi yasa da yawa cikin family na su ba'a fiya son zuwa gidan ba, duk da cewar ita ba mazauniya bace ko da yaushe tana kan hanyar seminer to other countries. Ƴaƴan ƴan'uwa da dama idan sun zo Abuja karatu ta ƙwammaci ta basu gidajenta na haya su zauna aciki akan dai su zauna tare da su, ita matsalarta bata da yarda, gani tke kowa macuci ne, currently rigimar ma da ake da ita akan student ne mata masu zuwa neman taimakon registration, tayi rantsuwa kan cewa ba taimako suke zuwa ba kalle mata miji suke zuwa yi, ya tsufa ɗinma amma mayu sunƙi barinsa, to balle ya kai Mairo gidan da sunan zama tare da su na tsawon wani lokaci, ita da bata son zuwan budurwa, acewarta Mace shaiɗaniya ce zata rabata da ƴaƴanta ne da mijinta. ya sauke numfashi tare da jinginar da kansa jikin kujera, ɗaya ɓari na zuciyarsa kuma ya fara tunasar da shi waye Mahaifinsa, Mom na matuƙar shakkarsa, tun aurensu ma balle kuma da ta sha bulalar soja, mutum ne shi da ba ya ɗaukan shirmen banza thats why ake samun sauƙi a wasu lamuran nata, amma duk da haka za'a sha cin magani tare da fushi da fad'a. Mairo ta katse tunaninsa da faɗin,"Uncle why the silent, ko kaima baka so mu tafi mu bar Aunt?". yay murmushin da shi kaɗai yasan ma'anarsa sannan yaywa motar key suka bar asibitin, daga nan kuma direct office ya wuce. tun kamin su shigo company ɗin Mairo ta saki baki galala tana kallon tsaruwar ma'aikatar, da su ka shigo daga ciki kuwa sai ta rufe baki dan ta lura idan ta biye ta kallonsa a haka to soon zata fara dalalar da yawu. da sauri PA ta ƙaraso ta buɗe masa ƙofa tare da amsar jakarsa, sannan ya umarceta da ta zagaya ta buɗewa Mairo ma, ai fitowar Mairo a motar sai yasa ta kusa suman tsaye, saboda gamo da kyawun halittar da bata taɓa gani ba, _aina Oga ya samo wannan Beb ɗin?_ ta faɗa a ƙasan zuciyarta, sai kuma tayi wata munafukar dariya, _ina ma Joy tana nan._ ta ayyana hakan a ranta. hannun Mairo ta riƙe suka bi bayansa tana tambayarsa,"Sir where did you find a beautifull Lady?". ta tambaye shi kai tsaye dan ita su na ɗasawa da shi. yayi gudun wannan surutun, kuma dama yasan za'a rina sai dai idan PA bata ganta ba. dan haka gudun kar surutun yay tasirin da zaija
🏠