NOVEL SHARES -
aɗin,"Beb ai ba za ki iya ba, ki bari sai kin gama jin sauƙi...idan muka koma gida ma wataran sai kin ƙosa da zuwa church saboda Mom". "ni dai please zan je, na fa ji sauƙi ai". ta faɗa tana riƙo hannunsa da sigar roƙo. yay ɗan jim kamin yace mata,"oak lets go". ta sakko a gadon ya tayata saka baƙin takalminta mai tudu sosai, sannan ya gyara mata zaman sarƙan cross ɗin ya riƙe hannunta suka fita, bata manta da ɗaukar bibile ɗin da ya siyo mata ba saboda karatun adu'ar dare idan zata yi bacci, dan Deborah ta faɗa masa kwana biyu bata cika bacci ba tana yawan firgita, shi ne ya siyo bible yace ta dinƙa karanta adu'oin ciki.
_________________________________
😂😂ni dai sai naga abun yay min banbarakwai namiji da suna Hajara, sak Mairo ƴar Malam Adamu me faskare ta fito a Ngozi ɗiyar Cinyare🤣.
*_Waiting For Your Warm Comments, Veiws, and Opinions...Your Support is all i need...LOVE YOU ALL._*
*Vote!Vote & Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*22)*
*Cathedral Church of Christ, Marina.*
A harabar da aka tanada domin aje motoci ya faka motar, ya dubi Mairo da cewar ta fito. ita dai tunda ta fito sai take ji ajikinta kamar wani sabon abu ke faruwa da ita, ya za'ai tsawon rayuwar da tayi a duniya kuma ace bata taɓa ganin irin wannan yanayin ba, shi kansa church ɗin kamar bata taɓa zuwansa ba, sai dai hakan kuma ba zai kasance ba ta sani.
tayi tsaye a jikin motar tana rungume da bible ɗinta tana jiran fitowarsa, kallon yanayin church ɗin take da kuma yanda mutane ke ta parking motoci su na fitowa su na shiga ciki a hanzarce, kowa dai da alama ba ya son rasa ibadar da zasu gudanar.
ko aciki da suka shiga kujerar kusa da ita Emanuel ya zauna, Mairo tana ƙarewa haɗuwar Church ɗin kallo tace,"it seems like bamu taɓa zuwa wannan church ɗin ba ko?". Emanuel ya juyo ya kalleta jin abinda tace. "kin manta ke baƙuwa ce a garin". sai ta ɗan rufe ido ta buɗe da faɗin,"ohh na manta, i feel like we are in Abuja". yayi murmushi bai ce komai ba sai ƙara damƙe hannunta da yayi, ba su jima da zama ba pastor ya ƙaraso aka fara gabatar da addu'a kafin a gama a saki kiɗa ana rawa, sosai Emanuel ya zage yana chashewa, ita kam Mairo ganin yana rawa ya bata dariya ita ma ta fara yi kamar yadda taga kowa nayi.
Bayan wani lokacin aka gama suka fito suka shiga mota su ka koma asibiti, Deborah ta shigo dan yiwa Mairo Alluranta na ƙarshe, bayan tayi mata ne ta kalle shi wanda ke tsaye yana danna waya, ta faɗa masa tana son yin magana da shi, daga bakin room ɗin su ka tsaya ta sanar masa da saƙon likita, yay ɗan jim yana wani tunani cikin ransa, he feels like violating what the doctor says, to amma ko yayi ko bai ba, ko a daɗe ko ba jima Mairo fa zata yi regaining tunaninta, to gwara ma yayi amfani da maganar likitan.
dan haka jiki a saɓule ya dawo room ɗin, Mairo na dubansa da yanayin sauyin Mood nasa cikin ƙanƙanen lokaci ta jefa masa tambayar,"Uncle what happen to you?, did someone hurt you?". ya ƙaƙalo murmushin da zai kira shi dana ƙarfin hali yace mata,"nothing, just like that". sannan ya samu kujera ya zauna, ya karɓi story book ɗin da ya siya mata musamman dan english ya zauna a kanta, yaci gaba da karanta musu labarin tare, sosai kuma shi da ita ke jin daɗin labarin kowa da salon da yake auna daɗin labarin a zuciyarsa.
ya nutsa cikin labarin sosai sai ya ajiye littafin yace da ita,"Beb lets go for a walk". ta noƙe kai alamar ita ta gaji, yace da ita,"Sorry Beb yanzu fa zamu dawo". ya faɗa yana riƙo hannunta ta sakko daga kan gadon.
fitarsu yawo suka yi sosai kuma duk a ƙafa, daga wannan store sai su shiga wannan store irin malls ɗin nan da suke a bakin titi, Mairo kuwa duk inda suka shiga jidar kayan maƙwalashe take kamar wadda zata buɗe nata kantin, saboda kuɗi abin banza ne a wurin Emanuel har da teddy ƴar 27k ta ɗauka kuma ya biya kuɗin, shi tausayinta yake matuƙa a yanda ta rasa tunaninta ta shiga cikin wata sabuwar rayuwa, wanda ya zama shi ne sila, dan haka gani yake zai iya yin komai dan ta kasance cikin farinciki da jin daɗi.
a wani restaurant da suka tsallaka da ke gefe sun dawo za su koma asibitin, mota ta bige wani tsohon mutum da ya zo tsallakawa, dan haka nan da nan jama'a su ka taru akan mai motar, ita kuma Mairo a wannan lokaci tsoratar ganin accident ɗin yasa ta ƙanƙame hannun Emanuel tana ɓoye fuskarta ajikinsa jikinta na rawa, bata so idanunta su ci gaba da ganin wannan mummunan haɗarin, shi kuwa Wannan lokacin sai ya rufe idanuwansa ya kasa buɗewa, zuciyarsa na fargabar dawowar tunaninta, dan haka sai y